New International Version

1 Peter 4:1-19

Living for God

1Therefore, since Christ suffered in his body, arm yourselves also with the same attitude, because whoever suffers in the body is done with sin. 2As a result, they do not live the rest of their earthly lives for evil human desires, but rather for the will of God. 3For you have spent enough time in the past doing what pagans choose to do—living in debauchery, lust, drunkenness, orgies, carousing and detestable idolatry. 4They are surprised that you do not join them in their reckless, wild living, and they heap abuse on you. 5But they will have to give account to him who is ready to judge the living and the dead. 6For this is the reason the gospel was preached even to those who are now dead, so that they might be judged according to human standards in regard to the body, but live according to God in regard to the spirit.

7The end of all things is near. Therefore be alert and of sober mind so that you may pray. 8Above all, love each other deeply, because love covers over a multitude of sins. 9Offer hospitality to one another without grumbling. 10Each of you should use whatever gift you have received to serve others, as faithful stewards of God’s grace in its various forms. 11If anyone speaks, they should do so as one who speaks the very words of God. If anyone serves, they should do so with the strength God provides, so that in all things God may be praised through Jesus Christ. To him be the glory and the power for ever and ever. Amen.

Suffering for Being a Christian

12Dear friends, do not be surprised at the fiery ordeal that has come on you to test you, as though something strange were happening to you. 13But rejoice inasmuch as you participate in the sufferings of Christ, so that you may be overjoyed when his glory is revealed. 14If you are insulted because of the name of Christ, you are blessed, for the Spirit of glory and of God rests on you. 15If you suffer, it should not be as a murderer or thief or any other kind of criminal, or even as a meddler. 16However, if you suffer as a Christian, do not be ashamed, but praise God that you bear that name. 17For it is time for judgment to begin with God’s household; and if it begins with us, what will the outcome be for those who do not obey the gospel of God? 18And,

“If it is hard for the righteous to be saved,

what will become of the ungodly and the sinner?”4:18 Prov. 11:31 (see Septuagint)

19So then, those who suffer according to God’s will should commit themselves to their faithful Creator and continue to do good.

Hausa Contemporary Bible

1 Bitrus 4:1-19

Rayuwa saboda Allah

1Saboda haka, da yake Kiristi ya sha wahala a jikinsa, sai ku ma ku yi wa kanku ɗamara da irin wannan hali, gama wanda ya sha wahala a jikinsa ya gama da zunubi ke nan. 2Ta haka, ba ya sauran rayuwarsa a kan mugayen sha’awace-sha’awacen jiki, sai dai nufin Allah. 3Gama kun ɓata lokaci sosai a dā kuna yin abubuwan da masu bauta gumaka suka zaɓa su yi, kuna rayuwa cikin lalata, sha’awace-sha’awace, buguwa, shashanci, shaye-shaye da kuma bautar gumaka masu banƙyama. 4Sun yi mamaki da ba kwa haɗa kai da su a yanzu, da ba kwa kutsa kai tare da su cikin irin rayuwar banzan nan, har suna zaginku. 5Amma dole su ba da lissafi gare shi wanda yake a shirye yă shari’anta masu rai da matattu. 6Dalilin ke nan da ya sa aka yi wa’azin bishara har ga waɗanda yanzu suke mutattu, don ko da yake an hukunta su a matsayin mutane a batun jiki, amma su rayu ga Allah a batun ruhu.

7Ƙarshen abubuwa duka ya yi kusa. Saboda haka ku kasance masu tunani mai kyau da masu kamunkai don ku iya yin addu’a. 8Fiye da kome, ku ƙaunaci juna sosai, domin ƙauna tana rufe zunubai masu ɗumbun yawa. 9Ku riƙa karɓar juna ba da gunaguni ba. 10Kowa yă yi amfani da kowace baiwar da ya samu don kyautata wa waɗansu, cikin aminci yana aikata alherin Allah a hanyoyi dabam-dabam. 11In wani ya yi magana, ya kamata yă yi ta a matsayin wanda yake magana ainihin kalmomin Allah. In wani yana yin hidima, ya kamata yă yi ta da ƙarfin da Allah ya tanadar, domin a cikin kome a yabi Allah ta wurin Yesu Kiristi. A gare shi ɗaukaka da iko sun tabbata har abada abadin. Amin.

Shan wahala don zaman Kirista

12Abokaina ƙaunatattu, kada ku yi mamakin gwaji mai tsananin da kuke sha, sai ka ce wani baƙon abu ne yake faruwa da ku. 13Sai dai ku yi murna cewa kuna tarayya cikin shan wahalolin Kiristi, domin ku kai ga farin ciki mai yawa sa’ad da aka bayyana ɗaukakarsa. 14In an zage ku saboda sunan Kiristi, ku masu albarka ne, gama Ruhun ɗaukaka da kuma na Allah yana bisanku. 15In kuna shan wahala, kada yă zama don ku masu kisankai ne ko ɓarayi ko masu wani irin laifi ko kuma masu shisshigi. 16Amma fa, in kuka sha wahala a matsayin ku Kirista ne, kada ku ji kunya, sai dai ku yabi Allah cewa kuna amsa wannan suna. 17Gama lokaci ya yi da za a fara yi wa iyalin Allah shari’a; in kuwa ya fara da mu, to, me zai faru da waɗanda ba sa biyayya da bisharar Allah? 18Kuma,

“In da ƙyar masu adalci su kuɓuta,

me zai faru da marasa tsoron Allah da kuma masu zunubi?”4.18 K Mag 11.31

19Saboda haka, waɗanda suke shan wahala bisa ga nufin Allah ya kamata su danƙa kansu ga Mahaliccinsu mai aminci, su kuma ci gaba da aikata abin da yake daidai.