King James Version

2 Corinthians 11:1-33

1Would to God ye could bear with me a little in my folly: and indeed bear with me. 2For I am jealous over you with godly jealousy: for I have espoused you to one husband, that I may present you as a chaste virgin to Christ. 3But I fear, lest by any means, as the serpent beguiled Eve through his subtilty, so your minds should be corrupted from the simplicity that is in Christ. 4For if he that cometh preacheth another Jesus, whom we have not preached, or if ye receive another spirit, which ye have not received, or another gospel, which ye have not accepted, ye might well bear with him. 5For I suppose I was not a whit behind the very chiefest apostles. 6But though I be rude in speech, yet not in knowledge; but we have been throughly made manifest among you in all things. 7Have I committed an offence in abasing myself that ye might be exalted, because I have preached to you the gospel of God freely? 8I robbed other churches, taking wages of them, to do you service. 9And when I was present with you, and wanted, I was chargeable to no man: for that which was lacking to me the brethren which came from Macedonia supplied: and in all things I have kept myself from being burdensome unto you, and so will I keep myself. 10As the truth of Christ is in me, no man shall stop me of this boasting in the regions of Achaia. 11Wherefore? because I love you not? God knoweth. 12But what I do, that I will do, that I may cut off occasion from them which desire occasion; that wherein they glory, they may be found even as we. 13For such are false apostles, deceitful workers, transforming themselves into the apostles of Christ. 14And no marvel; for Satan himself is transformed into an angel of light. 15Therefore it is no great thing if his ministers also be transformed as the ministers of righteousness; whose end shall be according to their works.

16I say again, Let no man think me a fool; if otherwise, yet as a fool receive me, that I may boast myself a little. 17That which I speak, I speak it not after the Lord, but as it were foolishly, in this confidence of boasting. 18Seeing that many glory after the flesh, I will glory also. 19For ye suffer fools gladly, seeing ye yourselves are wise. 20For ye suffer, if a man bring you into bondage, if a man devour you, if a man take of you, if a man exalt himself, if a man smite you on the face. 21I speak as concerning reproach, as though we had been weak. Howbeit whereinsoever any is bold, (I speak foolishly,) I am bold also. 22Are they Hebrews? so am I. Are they Israelites? so am I. Are they the seed of Abraham? so am I. 23Are they ministers of Christ? (I speak as a fool) I am more; in labours more abundant, in stripes above measure, in prisons more frequent, in deaths oft. 24Of the Jews five times received I forty stripes save one. 25Thrice was I beaten with rods, once was I stoned, thrice I suffered shipwreck, a night and a day I have been in the deep; 26In journeyings often, in perils of waters, in perils of robbers, in perils by mine own countrymen, in perils by the heathen, in perils in the city, in perils in the wilderness, in perils in the sea, in perils among false brethren; 27In weariness and painfulness, in watchings often, in hunger and thirst, in fastings often, in cold and nakedness. 28Beside those things that are without, that which cometh upon me daily, the care of all the churches. 29Who is weak, and I am not weak? who is offended, and I burn not? 30If I must needs glory, I will glory of the things which concern mine infirmities. 31The God and Father of our Lord Jesus Christ, which is blessed for evermore, knoweth that I lie not. 32In Damascus the governor under Aretas the king kept the city of the Damascenes with a garrison, desirous to apprehend me: 33And through a window in a basket was I let down by the wall, and escaped his hands.

Hausa Contemporary Bible

2 Korintiyawa 11:1-33

Bulus da manzannin ƙarya

1Ina fata za ku yi haƙuri da ’yar wautata. Amma, ai, kun riga kun yi haƙuri. 2Ina kishinku da kishi irin na Allah. Na yi muku alkawarin aure ga miji ɗaya, Kiristi, domin in miƙa ku a gare shi kamar budurwa zalla. 3Sai dai ina tsoro kada yă zama, kamar yadda maciji ya yaudari Hawwa’u da makircinsa, ku ma a bauɗar da hankalinku daga sahihiyar biyayya amintacciya ga Kiristi. 4Gama in wani ya zo wurinku yana wa’azin wani Yesu dabam da wanda muka yi wa’azinsa, ko kuma in kun karɓi wani ruhu dabam da wanda kuka karɓa, ko wata bishara dabam da wadda kuka karɓa, ya nuna kun yarda da su ke nan cikin sauƙinkai. 5Amma a ganina waɗancan da kuke ce da su “manyan manzanni” ba su fi ni da wani abu ba. 6Mai yiwuwa ni ba horarre ba ne a magana, amma ina da sani. Mun kuwa bayyana muku wannan a sarari, ta kowace hanya.

7Laifi ke nan ne na yi da na ƙasƙantar da kaina, don a ɗaga ku zuwa babban matsayi ta wurin yin muku wa’azin bisharar Allah kyauta? 8Na yi wa waɗansu ikkilisiyoyi ƙwace ta wurin karɓar taimako daga wurinsu, domin in yi muku hidima. 9Sa’ad da nake tare da ku kuma nake zaman rashi, ban nawaita wa kowa ba, gama ’yan’uwan da suka zo daga Makidoniya sun biya bukata. Na kiyaye kaina daga nawaita muku ta kowace hanya, zan kuma ci gaba da yin haka. 10Ba shakka, kamar yadda gaskiyar Kiristi take a cikina, babu wani a yankunan Akayya da zai iya hana yin taƙaman nan tawa. 11Don me? Don ba na ƙaunar ku ne? Allah dai ya sani ina ƙaunarku!

12Zan kuma ci gaba da yin abin da nake yi, domin in toshe kafar mutanen nan da suke fariya, suna nema mu daidaita da su. 13Gama irin waɗannan mutane manzannin ƙarya ne, ma’aikata ne masu ruɗi, sun ɓad da kamanni kamar su manzannin Kiristi ne. 14Ba abin mamaki ba ne, gama Shaiɗan kansa ma yana ɓad da kamanni kamar shi mala’ikan haske ne. 15Don haka, ba abin mamaki ba ne, in bayin Shaiɗan sun ɓad da kamanni kamar su bayin adalci ne. A ƙarshe, za a sāka musu gwargwadon ayyukansu.

Bulus ya yi taƙama game da wahalarsa

16Ina sāke faɗa, kada wani yă ɗauka ni wawa ne. Amma in kun ɗauke ni haka, to, sai ku karɓe ni kamar yadda kuke karɓan wawa, domin in ɗan in yi taƙama. 17A wannan taƙamata ba na magana yadda Ubangiji zai yi ba ne, sai dai magana ce irin ta wawa. 18Da yake mutane da yawa suna taƙama irin ta duniya, ni ma haka zan yi. 19Ku kam kuna da wayo sosai, har kuna jimre wa wawaye da murna! 20Gaskiyar ita ce, kuna haƙuri da duk wanda ya sa ku bauta ko ya cuce ku ko ya more ku ko ya nuna muku isa ko kuma ya mare ku a fuska. 21Ina jin kunya in ce mun nuna kāsawa da ba mu yi waɗannan abubuwan ba!

Abin da wani yake da ƙarfin hali yin taƙama a kai, shi ne ni ma nake ƙarfin hali yin taƙama a kai. Ina magana kamar wawa ne. 22In su Ibraniyawa ne, ni ma haka. In su Isra’ilawa ne, ni ma haka. In su zuriyar Ibrahim ne, ni ma haka. 23In su bayin Kiristi ne, ni na fi su ma, ina magana kamar ruɗaɗɗe ne fa! Ai, na fi su shan fama ƙwarai da gaske, da shan dauri, na sha dūka marar iyaka, na sha hatsarin mutuwa iri-iri. 24Sau biyar Yahudawa suka yi mini bulala arba’in ɗaya babu. 25Sau uku aka bulale ni da bulalar ƙarfe, sau ɗaya aka jajjefe ni da duwatsu, sau uku jirgin ruwa ya ragargaje ina ciki, na kwana na kuma yini ruwan teku yana tafiya da ni. 26Na yi tafiye-tafiye da yawa, na sha hatsari a koguna, na sha hatsarin ’yan fashi, na sha hatsari a hannun kabilarmu, na sha hatsari a hannun al’ummai, na sha hatsari a birane, na sha hatsari a jeji, na sha hatsari a teku, na kuma sha hatsarin ’yan’uwa na ƙarya. 27Na yi fama, na shan wuya, ga kuma rashin barci sau da yawa. Na san abin da ake nufin da jin yunwa da ƙishirwa, sau da yawa kuwa na kasance da rashin abinci, na sha sanyi da zaman tsirara. 28Ban da waɗannan abubuwa, kowace rana ina ɗauke da nauyin kula da dukan ikkilisiyoyi. 29Wane ne ya rasa ƙarfi, da ban ji shi a jikina ba? Wane ne ya fāɗi cikin zunubi, da ban ji zafin wannan ba?

30In ma lalle ne in yi taƙama, to, sai in yi taƙama da abubuwan da suka nuna rashin ƙarfina. 31Allah Uban Ubangiji Yesu Kiristi, wanda yabo ta tabbata a gare shi har abada, ya san cewa ba ƙarya nake yi ba. 32A Damaskus, gwamnan da yake ƙarƙashin Sarki Aretas, ya sa tsare ƙofofin birnin Damaskus, don yă kama ni. 33Amma aka saukar da ni cikin kwando ta tagar katanga, na kuɓuce masa.