Mattiyu 4 – Hausa Contemporary Bible HCB

Hausa Contemporary Bible

Mattiyu 4:1-25

Gwajin Yesu

(Markus 1.12,13; Luka 4.1-13)

1Sa’an nan Ruhu ya kai Yesu cikin hamada don Iblis yă gwada shi. 2Bayan ya yi azumi yini arba’in da kuma dare arba’in, sai ya ji yunwa. 3Sai mai gwajin ya zo wurinsa ya ce, “In kai Ɗan Allah ne, ka ce wa duwatsun nan su zama burodi.”

4Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake cewa, ‘Ba da abinci kaɗai mutum yake rayuwa ba, sai dai da kowace kalmar da take fitowa daga bakin Allah.’4.4 M Sh 8.3

5Sai Iblis ya kai shi birni mai tsarki, ya kai shi can wuri mafi tsayi duka na haikali. 6Ya ce, “In kai Ɗan Allah ne, yi tsalle ka sauka ƙasa. Gama a rubuce yake,

“ ‘Zai umarci mala’ikunsa game da kai,

za su tallafe ka da hannuwansu,

don kada ka buga ƙafarka a kan dutse.’4.6 Zab 91.11,12

7Yesu ya amsa masa ya ce, “A rubuce yake kuma cewa, ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’4.7 M Sh 6.16

8Har wa yau, Iblis ya kai shi bisa wani dutse mai tsawo sosai, ya nunnuna masa dukan mulkokin duniya da darajarsu. 9Ya ce, “Zan ba ka dukan wannan, in za ka durƙusa ka yi mini sujada.”

10Sai Yesu ya ce masa, “Rabu da ni, Shaiɗan! Gama a rubuce yake, ‘Yi wa Ubangiji Allahnka sujada, shi kaɗai kuma za ka bauta wa.’4.10 M Sh 6.13

11Sa’an nan Iblis ya bar shi, mala’iku kuwa suka zo suka yi masa hidima.

Yesu ya fara wa’azi

(Markus 1.14,15; Luka 4.14,15)

12Da Yesu ya ji labari cewa an kulle Yohanna a kurkuku, sai ya koma zuwa Galili. 13Ya bar Nazaret, ya je ya zauna a Kafarnahum, wadda take a bakin tafki wajen Zebulun da Naftali 14don a cika abin da aka faɗa ta bakin annabi Ishaya cewa,

15“Ƙasar Zebulun da ƙasar Naftali,

da kuke a hanyar zuwa tekun Galili, a ƙetaren Urdun,

wannan yankin Galili ta Al’ummai,

16mutanen da suke zama cikin duhu

sun ga babban haske;

haske kuma ya haskaka

a kan waɗanda suke zama a inuwar mutuwa.”4.16 Ish 9.1,2f

17Tun daga wannan lokaci, Yesu ya fara wa’azi yana cewa, “Ku tuba, gama mulkin sama ya yi kusa.”

Kiran almajirai na farko

(Markus 1.16-20; Luka 5.1-11)

18Da Yesu yana kan tafiya a bakin Tekun Galili, sai ya ga waɗansu ’yan’uwa guda biyu, Siman wanda ake kira Bitrus da ɗan’uwansa Andarawus. Suna jefa abin kamun kifi a tafki, gama su masunta ne. 19Sai Yesu ya ce, “Zo, ku bi ni, ni kuwa zan mai da ku masu jan mutane zuwa wurina.” 20Nan da nan suka bar abin kamun kifinsu suka bi shi.

21Da ya ci gaba daga nan, sai ya ga waɗansu ’yan’uwa guda biyu, Yaƙub ɗan Zebedi da ɗan’uwansa Yohanna. Suna cikin jirgin ruwa tare da mahaifinsu Zebedi, suna shirya abin kamun kifinsu. Yesu ya kira su, 22nan take suka bar jirgin ruwan da mahaifinsu suka kuwa bi Yesu.

Yesu ya warkar da marasa lafiya

(Luka 6.17-19)

23Yesu ya zazzaga dukan Galili, yana koyarwa a cikin majami’unsu, yana wa’azin labari mai daɗi na mulkin sama, yana kuma warkar da kowace cuta da rashin lafiyar mutane. 24Labarinsa ya bazu ko’ina a Suriya, mutane kuwa suka kawo masa dukan waɗanda suke fama da cututtuka iri-iri, da waɗanda suke da zafin ciwo, da masu aljanu, da waɗanda suke masu farfaɗiya, da shanyayyu, ya kuwa warkar da su. 25Taron mutane mai yawa daga Galili, Dekafolis,4.25 Wato, Birane Goma Urushalima, Yahudiya da kuma yankin hayin Urdun suka bi shi.