Luke 18 – NIRV & HCB

New International Reader’s Version

Luke 18:1-43

The Story of the Widow Who Would Not Give Up

1Jesus told his disciples a story. He wanted to show them that they should always pray and not give up. 2He said, “In a certain town there was a judge. He didn’t have any respect for God or care about what people thought. 3A widow lived in that town. She came to the judge again and again. She kept begging him, ‘Make things right for me. Someone is treating me badly.’

4“For some time the judge refused. But finally he said to himself, ‘I don’t have any respect for God. I don’t care about what people think. 5But this widow keeps bothering me. So I will see that things are made right for her. If I don’t, she will someday come and attack me!’ ”

6The Lord said, “Listen to what the unfair judge says. 7God’s chosen people cry out to him day and night. Won’t he make things right for them? Will he keep putting them off? 8I tell you, God will see that things are made right for them. He will make sure it happens quickly. But when the Son of Man comes, will he find people on earth who have faith?”

The Story of the Pharisee and the Tax Collector

9Jesus told a story to some people who were sure they were right with God. They looked down on everyone else. 10He said to them, “Two men went up to the temple to pray. One was a Pharisee. The other was a tax collector. 11The Pharisee stood by himself and prayed. ‘God, I thank you that I am not like other people,’ he said. ‘I am not like robbers or those who do other evil things. I am not like those who commit adultery. I am not even like this tax collector. 12I fast twice a week. And I give a tenth of all I get.’

13“But the tax collector stood farther away than the Pharisee. He would not even look up to heaven. He brought his hand to his heart and prayed. He said, ‘God, have mercy on me. I am a sinner.’

14“I tell you, the tax collector went home accepted by God. But not the Pharisee. All those who lift themselves up will be made humble. And those who make themselves humble will be lifted up.”

Little Children Are Brought to Jesus

15People were also bringing babies to Jesus. They wanted him to place his hands on the babies. When the disciples saw this, they told the people to stop. 16But Jesus asked the children to come to him. “Let the little children come to me,” he said. “Don’t keep them away. God’s kingdom belongs to people like them. 17What I’m about to tell you is true. Anyone who will not receive God’s kingdom like a little child will never enter it.”

Rich People and the Kingdom of God

18A certain ruler asked Jesus a question. “Good teacher,” he said, “what must I do to receive eternal life?”

19“Why do you call me good?” Jesus answered. “No one is good except God. 20You know what the commandments say. ‘Do not commit adultery. Do not commit murder. Do not steal. Do not be a false witness. Honor your father and mother.’ ” (Exodus 20:12–16; Deuteronomy 5:16–20)

21“I have obeyed all those commandments since I was a boy,” the ruler said.

22When Jesus heard this, he said to him, “You are still missing one thing. Sell everything you have. Give the money to those who are poor. You will have treasure in heaven. Then come and follow me.”

23When the ruler heard this, he became very sad. He was very rich. 24Jesus looked at him. Then he said, “How hard it is for rich people to enter God’s kingdom! 25Is it hard for a camel to go through the eye of a needle? It is even harder for someone who is rich to enter God’s kingdom!”

26Those who heard this asked, “Then who can be saved?”

27Jesus replied, “Things that are impossible with people are possible with God.”

28Peter said to him, “We have left everything we had in order to follow you!”

29“What I’m about to tell you is true,” Jesus said to them. “Has anyone left home or wife or husband or brothers or sisters or parents or children for God’s kingdom? 30They will receive many times as much in this world. In the world to come they will receive eternal life.”

Jesus Speaks a Third Time About His Coming Death

31Jesus took the 12 disciples to one side. He told them, “We are going up to Jerusalem. Everything that the prophets wrote about the Son of Man will come true. 32He will be handed over to the Gentiles. They will make fun of him. They will laugh at him and spit on him. 33They will whip him and kill him. On the third day, he will rise from the dead!”

34The disciples did not understand any of this. Its meaning was hidden from them. So they didn’t know what Jesus was talking about.

A Blind Beggar Receives His Sight

35Jesus was approaching Jericho. A blind man was sitting by the side of the road begging. 36The blind man heard the crowd going by. He asked what was happening. 37They told him, “Jesus of Nazareth is passing by.”

38So the blind man called out, “Jesus! Son of David! Have mercy on me!”

39Those who led the way commanded him to stop. They told him to be quiet. But he shouted even louder, “Son of David! Have mercy on me!”

40Jesus stopped and ordered the man to be brought to him. When the man came near, Jesus spoke to him. 41“What do you want me to do for you?” Jesus asked.

“Lord, I want to be able to see,” the blind man replied.

42Jesus said to him, “Receive your sight. Your faith has healed you.” 43Right away he could see. He followed Jesus, praising God. When all the people saw it, they also praised God.

Hausa Contemporary Bible

Luka 18:1-43

Misalin gwauruwa mai naciya

1Yesu ya ba wa almajiransa wani misali, don yă koya musu yadda ya kamata su dinga yin addu’a kullum, ban da fasawa. 2Ya ce, “A wani gari, an yi wani alƙali wanda ba ya tsoron Allah, bai kuma kula da mutane ba. 3A garin nan kuma, akwai wata gwauruwa, wadda ta dinga zuwa wurin alƙalin nan, da roƙo cewa, ‘Ka yi mini adalci tsakanina da maƙiyina.’

4“An daɗe yana ƙi, amma a ƙarshe ya ce cikin tunaninsa, ‘Ko da yake ba na tsoron Allah, ba na kuma kula da mutane ba, 5amma don gwauruwan nan ta dame ni, zan tabbatar cewa ta sami adalci, domin kada tă gajiyar da ni, da yawan zuwanta.’ ”

6Sai Ubangiji ya ce, “Ku ji fa abin da alƙalin nan, marar gaskiya, ya ce. 7Ashe, Allah ba zai biya wa zaɓaɓɓunsa da suke masa kuka, dare da rana adalci ba? Zai ci gaba da ƙin sauraronsu ne? 8Ina gaya muku, zai tabbatar sun sami adalci, ban da ɓatan lokaci. Amma sa’ad da Ɗan Mutum ya dawo, zai sami bangaskiya a duniya ke nan?”

Misalin Bafarisiye da mai karɓar haraji

9Yesu ya kuma faɗi wannan misali ga waɗansu masu taƙama da adalcinsu, kuma suna rena sauran mutane ya ce, 10“Waɗansu mutane biyu sun tafi haikali don yin addu’a. Ɗaya Bafarisiye ne, ɗayan kuma mai karɓar haraji. 11Sai Bafarisiyen ya tashi tsaye, ya yi addu’a game da kansa yana cewa, ‘Allah, na gode maka, saboda ni ba kamar sauran mutane ba ne, wato, mafasa, masu aikata mugunta, masu zina, ko kuma kamar mai karɓar harajin nan. 12Ina azumi sau biyu a mako, ina ba da zakka daga kowane abin da na samu.’

13“Amma mai karɓar harajin ya tsaya daga nesa. Bai ma iya ɗaga kansa sama ba, sai ya buga ƙirjinsa, yana cewa, ‘Allah, ka yi mini jinƙai, ni mai zunubi ne.’

14“Ina gaya muku, wannan mutum ne, ba ɗayan ba, ya koma gida baratacce, babu laifi a gaban Allah. Gama duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Wanda kuma ya ƙasƙantar da kansa, za a ɗaukaka shi.”

Yesu da ƙananan yara

(Mattiyu 19.13-15; Markus 10.13-16)

15Mutane suna kawo jarirai wurin Yesu don yă taɓa su. Da almajiransa suka ga haka, sai suka kwaɓe su. 16Amma Yesu ya kira yaran a wurinsa ya ce, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina. Kada ku hana su, gama mulkin Allah na irin waɗannan ne. 17Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ba zai karɓi mulkin Allah kamar ƙaramin yaro ba, ba zai taɓa shiga mulkin ba.”

Mai mulki mai arziki

(Mattiyu 19.16-30; Markus 10.17-31)

18Wani mai mulki ya tambayi Yesu ya ce, “Malam managarci, me zan yi don in gāji rai madawwami?”

19Yesu ya amsa ya ce, “Don me kake kira na managarci? Ai, ba wani nagari, sai Allah kaɗai. 20Ka san dokokin da suka ce, ‘Kada ka yi zina, kada ka yi kisankai, kada ka yi sata, kada ka ba da shaida ta ƙarya, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.’ ”

21Mutumin ya ce, “Ai, tun ina ƙarami, na kiyaye duka waɗannan.”

22Da Yesu ya ji haka, sai ya ce masa, “Akwai abu ɗaya har yanzu da ya rage maka. Ka sayar da duk abin da kake da shi, ka ba wa matalauta, sa’an nan za ka sami dukiya a sama. Bayan haka, ka zo ka bi ni.”

23Da jin haka, sai ya ɓata rai, domin shi mai arziki ne sosai. 24Yesu ya kalle shi ya ce, “Yana da wuya fa, masu arziki su shiga mulkin Allah! 25Tabbatacce, zai fi sauƙi raƙumi ya shiga ta kafar allura, da mai arziki ya shiga mulkin Allah.”

26Waɗanda suka ji wannan suka yi tambaya suka ce, “To, wa zai iya samun ceto?”

27Yesu ya amsa ya ce, “Abin da ba ya yiwuwa ga mutane, mai yiwuwa ne ga Allah.”

28Sai Bitrus ya ce, masa, “To, ga shi mun bar kome da muke da shi, don mu bi ka!”

29Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, ba wanda ya bar gida, ko mata, ko ’yan’uwa maza, ko iyaye, ko yara, saboda mulkin Allah, 30da zai kāsa samun riɓi mai yawa, a wannan zamani, ya kuma sami rai madawwami a zamani mai zuwa.”

Yesu ya sāke magana a kan mutuwarsa

(Mattiyu 20.17-19; Markus 10.32-34)

31Sai ya kai Sha Biyun gefe ɗaya, ya ce musu, “Za mu Urushalima, kuma dukan abin da annabawa suka rubuta a kan Ɗan Mutum zai cika. 32Za a ba da shi ga Al’ummai, za su yi masa ba’a, su zage shi, su tofa masa miyau, 33za su yi masa bulala, su kuma kashe shi. A rana ta uku kuma zai tashi.”

34Almajiran ba su gane da ko ɗaya daga cikin wannan ba. An ɓoye musu ma’anarsa, kuma ba su gane da abin da yake magana a kai ba.

Makaho mai bara ya sami ganin gari

(Mattiyu 20.17-19; Markus 10.32-34)

35Da Yesu ya yi kusa da Yeriko, akwai wani makaho da yake zaune a gefen hanya, yana bara. 36Da ya ji taron suna wucewa, sai ya yi tambaya ko mene ne ke faruwa. 37Suka ce masa, “Ai, Yesu Banazare ne ke wucewa.”

38Sai ya yi kira ya ce, “Yesu, Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai!”

39Mutane da suke gaba suka kwaɓe shi, suka ce masa ya yi shiru. Amma sai ya ƙara ɗaga murya, yana cewa, “Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai!”

40Sai Yesu ya tsaya, ya ba da umarni a kawo mutumin wurinsa. Da ya zo kusa, Yesu ya tambaye shi ya ce, 41“Me kake so in yi maka?”

Sai ya amsa ya ce, “Ubangiji, ina so in sami ganin gari.”

42Yesu ya ce masa, “Ka sami ganin garinka; bangaskiyarka ta warkar da kai.” 43Nan da nan, ya sami ganin garinsa, kuma ya bi Yesu, yana yabon Allah. Da dukan mutane suka ga wannan, sai su ma suka yabi Allah.