Luke 17 – NIRV & HCB

New International Reader’s Version

Luke 17:1-37

Sin, Faith and Duty

1Jesus spoke to his disciples. “Things that make people sin are sure to come,” he said. “But how terrible it will be for anyone who causes those things to come! 2Suppose people lead one of these little ones to sin. It would be better for those people to be thrown into the sea with a millstone tied around their neck. 3So watch what you do.

“If your brother or sister sins against you, tell them they are wrong. Then if they turn away from their sins, forgive them. 4Suppose they sin against you seven times in one day. And suppose they come back to you each time and say, ‘I’m sorry.’ You must forgive them.”

5The apostles said to the Lord, “Give us more faith!”

6He replied, “Suppose you have faith as small as a mustard seed. Then you can say to this mulberry tree, ‘Be pulled up. Be planted in the sea.’ And it will obey you.

7“Suppose one of you has a servant plowing or looking after the sheep. And suppose the servant came in from the field. Will you say to him, ‘Come along now and sit down to eat’? 8No. Instead, you will say, ‘Prepare my supper. Get yourself ready. Wait on me while I eat and drink. Then after that you can eat and drink.’ 9Will you thank the servant because he did what he was told to do? 10It’s the same with you. Suppose you have done everything you were told to do. Then you should say, ‘We are not worthy to serve you. We have only done our duty.’ ”

Jesus Heals Ten Men Who Have a Skin Disease

11Jesus was on his way to Jerusalem. He traveled along the border between Samaria and Galilee. 12As he was going into a village, ten men met him. They had a skin disease. They were standing close by. 13And they called out in a loud voice, “Jesus! Master! Have pity on us!”

14Jesus saw them and said, “Go. Show yourselves to the priests.” While they were on the way, they were healed.

15When one of them saw that he was healed, he came back. He praised God in a loud voice. 16He threw himself at Jesus’ feet and thanked him. The man was a Samaritan.

17Jesus asked, “Weren’t all ten healed? Where are the other nine? 18Didn’t anyone else return and give praise to God except this outsider?” 19Then Jesus said to him, “Get up and go. Your faith has healed you.”

The Coming of God’s Kingdom

20Once the Pharisees asked Jesus when God’s kingdom would come. He replied, “The coming of God’s kingdom is not something you can see. 21People will not say, ‘Here it is.’ Or, ‘There it is.’ That’s because God’s kingdom is among you.”

22Then Jesus spoke to his disciples. “The time is coming,” he said, “when you will long to see one of the days of the Son of Man. But you won’t see it. 23People will tell you, ‘There he is!’ Or, ‘Here he is!’ Don’t go running off after them. 24When the Son of Man comes, he will be like the lightning. It flashes and lights up the sky from one end to the other. 25But first the Son of Man must suffer many things. He will not be accepted by the people of today.

26“Remember how it was in the days of Noah. It will be the same when the Son of Man comes. 27People were eating and drinking. They were getting married. They were giving their daughters to be married. They did all those things right up to the day Noah entered the ark. Then the flood came and destroyed them all.

28“It was the same in the days of Lot. People were eating and drinking. They were buying and selling. They were planting and building. 29But on the day Lot left Sodom, fire and sulfur rained down from heaven. And all the people were destroyed.

30“It will be just like that on the day the Son of Man is shown to the world. 31Suppose someone is on the housetop on that day. And suppose what they own is inside the house. They should not go down to get what they own. No one in the field should go back for anything either. 32Remember Lot’s wife! 33Whoever tries to keep their life will lose it. Whoever loses their life will keep it. 34I tell you, on that night two people will be in one bed. One person will be taken and the other left. 35-36Two women will be grinding grain together. One will be taken and the other left.”

37“Where, Lord?” his disciples asked.

He replied, “The vultures will gather where there is a dead body.”

Hausa Contemporary Bible

Luka 17:1-37

Zunubi, bangaskiya da aiki

(Mattiyu 18.6,7,21,22; Markus 9.42)

1Yesu ya ce wa almajiransa, “Dole ne a sami abubuwan da suke sa mutane su yi zunubi, amma kaiton mutumin nan wanda suke zuwa ta wurinsa. 2Gwamma a ɗaura dutsen niƙa a wuyansa, a jefa shi cikin teku, da ya sa ɗaya daga cikin ƙananan yaran nan ya yi zunubi. 3Saboda haka, ku lura da kanku.

“In ɗan’uwanka ya yi zunubi, ka kwaɓe shi. In ya tuba, ka gafarta masa. 4In ya yi maka laifi sau bakwai a rana ɗaya, ya kuma dawo sau bakwai ɗin a wurinka, yana cewa, ‘Na tuba,’ sai ka gafarta masa.”

5Sai manzannin suka ce wa Ubangiji, “Ka ƙara mana bangaskiya!”

6Ya amsa musu ya ce, “In kuna da bangaskiya da take ƙanƙani kamar ƙwayar mustad, kuna iya ce wa wannan itacen durumi, ‘Ka tumɓuke daga nan, ka dasu a cikin teku.’ Zai kuwa yi muku biyayya.

7“In ɗaya a cikinku yana da bawa, wanda yake masa noma, ko kiwon tumaki, da dawowar bawan daga gonar, ai, ba zai ce masa, ‘Ka zo nan, ka zauna, ka ci abinci ba’? 8Ashe, ba zai ce masa, ‘Ka shirya mini abincin yamma, ka shirya ka yi mini hidima domin in ci in sha, bayan haka kana iya ci, ka kuma sha ba’? 9Shin, zai gode wa bawan don yă yi aikin da aka ce ya yi ne? 10Haka ku ma, bayan kun yi duk abin da aka ce muku ku yi, ya kamata ku ce, ‘Mu bayi ne marasa cancanta, mun dai yi aikinmu ne kaɗai.’ ”

An warkar da kutare goma

11Yesu yana kan hanyarsa zuwa Urushalima, sai ya bi takan iyakar Samariya da Galili. 12Da zai shiga wani ƙauye, sai maza goma da suke da kuturta suka sadu da shi. Suka tsaya da nesa, 13suka yi kira da babbar murya, suka ce, “Yesu, Ubangiji, ka ji tausayinmu!”

14Da ya gan su sai ya ce, “Ku je ku nuna kanku ga firistoci.” Suna kan hanyar tafiya sai suka tsabtacce.

15Da ɗayansu ya ga ya warke, sai ya koma, yana yabon Allah da babbar murya. 16Ya zo ya fāɗi a gaban Yesu, ya gode masa. Shi kuwa mutumin Samariya ne.

17Yesu ya yi tambaya ya ce, “Ba duka goma ne aka tsabtacce ba? Ina sauran taran? 18Ba wanda ya dawo don yă yabi Allah, sai dai wannan baƙon?” 19Sai ya ce masa, “Tashi, ka yi tafiyarka, bangaskiyarka ta warkar da kai.”

Zuwan mulkin Allah

(Mattiyu 24.23-28,37-41)

20Wata rana, Farisiyawa suka tambaye shi lokacin da mulkin Allah zai zo, Yesu ya amsa ya ce, “Ai, mulkin Allah ba takan zo ta wurin yin kallon ku ba. 21Mutane kuma ba za su ce, ‘Ga shi nan,’ ko kuma, ‘Ga shi can’ ba, domin mulkin Allah yana cikinku ne.”

22Sai ya ce wa almajiransa, “Lokaci yana zuwa da za ku yi marmarin ganin rana ɗaya cikin ranakun Ɗan Mutum, amma ba za ku gani ba. 23Mutane za su ce muku, ‘Ga shi can!’ Ko kuma, ‘Ga shi nan!’ Kada ku yi hanzarin binsu. 24Gama Ɗan Mutum, a cikin ranarsa, zai zama kamar walƙiya da take walƙawa, da take kuma haskaka sararin sama, daga wannan kusurwa zuwa wancan kusurwa. 25Amma da fari, dole yă sha wahaloli masu yawa, kuma mutanen zamanin nan su ƙi shi.

26“Daidai kamar yadda ya faru a zamanin Nuhu, haka zai zama a zamanin Ɗan Mutum. 27Mutane suna ci, suna sha, suna aurayya, ana kuma ba da su ga aure, har ranar da Nuhu ya shiga jirgin. Sa’an nan ambaliyar ruwan ya sauka, ya hallaka su duka.

28“Haka ma aka yi a zamanin Lot. Mutane suna ci, suna sha, suna saya, suna sayarwa, suna shuki, suna kuma gine-gine. 29Amma a ranar da Lot ya bar Sodom, sai aka yi ruwan wuta da farar wuta daga sama, aka hallaka su duka.

30“Daidai haka zai zama, a ranar da Ɗan Mutum zai bayyana. 31A ranan nan, kada wanda yake kan rufin gidansa ya sauka don yă kwashe dukiyarsa da take cikin gidan. Haka ma duk wanda yake gona, kada yă koma don wani abu. 32Ku tuna fa da matar Lot! 33Duk wanda yake so ya ceci ransa, zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa, zai cece shi. 34Ina gaya muku, a daren nan, mutane biyu za su kasance a gado ɗaya, za a ɗauki ɗaya, a bar ɗayan. 35Mata biyu za su kasance suna niƙan hatsi tare, za a ɗauki ɗaya, a bar ɗayan.”17.35 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā suna da bar. 36 Mutum biyu za su kasance a gona, a ɗau ɗaya, a bar ɗaya.

37Suka tambaya, suka ce, “A ina ne, ya Ubangiji?”

Ya ce musu, “Ai, inda gawa take, nan ne ungulai za su taru.”