Luke 16 – NIRV & HCB

New International Reader’s Version

Luke 16:1-31

The Story of the Clever Manager

1Jesus told his disciples another story. He said, “There was a rich man who had a manager. Some said that the manager was wasting what the rich man owned. 2So the rich man told him to come in. He asked him, ‘What is this I hear about you? Tell me exactly how you have handled what I own. You can’t be my manager any longer.’

3“The manager said to himself, ‘What will I do now? My master is taking away my job. I’m not strong enough to dig. And I’m too ashamed to beg. 4I know what I’m going to do. I’ll do something so that when I lose my job here, people will welcome me into their houses.’

5“So he called in each person who owed his master something. He asked the first one, ‘How much do you owe my master?’

6“ ‘I owe 900 gallons of olive oil,’ he replied.

“The manager told him, ‘Take your bill. Sit down quickly and change it to 450 gallons.’

7“Then he asked the second one, ‘And how much do you owe?’

“ ‘I owe 1,000 bushels of wheat,’ he replied.

“The manager told him, ‘Take your bill and change it to 800 bushels.’

8“The manager had not been honest. But the master praised him for being clever. The people of this world are clever in dealing with those who are like themselves. They are more clever than God’s people. 9I tell you, use the riches of this world to help others. In that way, you will make friends for yourselves. Then when your riches are gone, you will be welcomed into your eternal home in heaven.

10“Suppose you can be trusted with something very little. Then you can also be trusted with something very large. But suppose you are not honest with something very little. Then you will also not be honest with something very large. 11Suppose you have not been worthy of trust in handling worldly wealth. Then who will trust you with true riches? 12Suppose you have not been worthy of trust in handling someone else’s property. Then who will give you property of your own?

13“No one can serve two masters at the same time. Either you will hate one of them and love the other. Or you will be faithful to one and dislike the other. You can’t serve God and money at the same time.”

14The Pharisees loved money. They heard all that Jesus said and made fun of him. 15Jesus said to them, “You try to make yourselves look good in the eyes of other people. But God knows your hearts. What people think is worth a lot is hated by God.

More Teachings

16“The teachings of the Law and the Prophets were preached until John the Baptist came. Since then, the good news of God’s kingdom is being preached. And everyone is trying very hard to enter it. 17It is easier for heaven and earth to disappear than for the smallest part of a letter to drop out of the Law.

18“Anyone who divorces his wife and marries another woman commits adultery. Also, the man who marries a divorced woman commits adultery.

The Rich Man and Lazarus

19“Once there was a rich man. He was dressed in purple cloth and fine linen. He lived an easy life every day. 20A man named Lazarus was placed at his gate. Lazarus was a beggar. His body was covered with sores. 21Even dogs came and licked his sores. All he wanted was to eat what fell from the rich man’s table.

22“The time came when the beggar died. The angels carried him to Abraham’s side. The rich man also died and was buried. 23In the place of the dead, the rich man was suffering terribly. He looked up and saw Abraham far away. Lazarus was by his side. 24So the rich man called out, ‘Father Abraham! Have pity on me! Send Lazarus to dip the tip of his finger in water. Then he can cool my tongue with it. I am in terrible pain in this fire.’

25“But Abraham replied, ‘Son, remember what happened in your lifetime. You received your good things. Lazarus received bad things. Now he is comforted here, and you are in terrible pain. 26Besides, a wide space has been placed between us and you. So those who want to go from here to you can’t go. And no one can cross over from there to us.’

27“The rich man answered, ‘Then I beg you, father Abraham. Send Lazarus to my family. 28I have five brothers. Let Lazarus warn them. Then they will not come to this place of terrible suffering.’

29“Abraham replied, ‘They have the teachings of Moses and the Prophets. Let your brothers listen to them.’

30“ ‘No, father Abraham,’ he said. ‘But if someone from the dead goes to them, they will turn away from their sins.’

31“Abraham said to him, ‘They do not listen to Moses and the Prophets. So they will not be convinced even if someone rises from the dead.’ ”

Hausa Contemporary Bible

Luka 16:1-31

Misalin manaja mai wayo

1Yesu ya ce wa almajiransa, “An yi wani mai arziki wanda aka yi wa manajansa zargin yin banza da dukiyarsa. 2Sai ya kira manajan, ya tambaye shi, ‘Me nake ji haka a kanka? Ka kawo lissafin aikinka, domin ba za ka iya cin gaba da aikinka ba.’

3“Sai manajan ya ce cikin tunaninsa, ‘Maigidana zai kore ni daga aiki, me zan yi? Ba ni da ƙarfin noma, kuma ina jin kunyan yin bara. 4Na san abin da zan yi, don mutane su karɓe ni a gidajensu, bayan an kore ni daga aiki a nan.’

5“Sai ya kira kowane ɗaya da maigidansa yake bin bashi. Ya tambayi na farkon ya ce, ‘Nawa ne maigidana yake bin ka?’

6“Ya amsa ya ce, ‘Garwar mai na zaitun guda ɗari tara.’

“Manajan ya ce, ‘Ga takardarka, ka zauna maza ka mai da shi ɗari huɗu.’

7“Ya kuma tambayi na biyun, ‘Kai fa, nawa ne ake bin ka?’

“Sai ya amsa ya ce, ‘Buhunan alkama dubu.’

“Ya ce, ‘Ga takardarka, ka mai da shi ɗari takwas.’

8“Maigidan kuwa ya yabi manajan nan marar gaskiya saboda wayonsa. Gama ’yan duniyan nan suna da wayon yin hulɗa da junansu fiye da ’yan haske. 9Ina gaya muku, ku yi amfani da dukiya na wannan duniya, domin ku sami wa kanku abokai. Saboda bayan dukiyar ta ƙare, za a karɓe ku a wuraren zama da sun dawwama.

10“Duk wanda ana amincewa da shi cikin ƙaramin abu, ana kuma amincewa da shi cikin babba. Kuma duk marar gaskiya cikin ƙaramin abu, zai zama marar gaskiya cikin babba. 11In fa ku ba amintattu ne cikin tafiyar da dukiya ta wannan duniya ba, wa zai amince muku da dukiya ta gaskiya? 12In fa ku ba amintattu ne cikin tafiyar da dukiyar wani ba, wa zai ba ku dukiya naku, na kanku?

13“Babu wani bawa mai iya bauta wa iyayengiji biyu ba. Ko dai ya ƙi ɗaya, ya so ɗayan, ko kuwa ya dāge ga yi wa ɗaya bauta, sa’an nan ya rena ɗayan. Ba za ku iya ku bauta wa Allah tare da bauta wa Mammon (wato, Kuɗi) a lokaci ɗaya ba.”

(Mattiyu 11.12,13; 5.31,32; Markus 10.11,12)

14Da Farisiyawa masu son kuɗi suka ji wannan duka, sai suka yi wa Yesu tsaki. 15Ya ce musu, “Ku ne masu mai da kanku marasa laifi a gaban mutane, amma Allah ya san zuciyarku. Abu mai daraja a gaban mutane, abin ƙyama ne a gaban Allah.

Ƙarin koyarwa

16“An yi shelar Doka da Annabawa har zuwa lokacin Yohanna. Tun daga lokacin nan, bisharar mulkin Allah ne ake wa’azinta, kowa kuma yana ƙoƙarin kutsa kai ya shiga. 17Gama ta fi sauƙi sama da ƙasa su shuɗe, da a ce ɗigo guda ɗaya na rubutun, ya fita ya fāɗi daga cikin Doka.

18“Duk wanda ya saki matarsa ya auri wata mace, zina ne yake yi. Kuma mutumin da ya auri macen da aka sake, zina ne yake yi.

Mai arziki da Lazarus

19“An yi wani mutum mai arziki wanda yakan sa tufafi masu ruwan shunayya, da kuma na lallausan lilin, yana kuma cikin rayuwar jin daɗi kullum. 20A ƙofar gidansa kuma akan ajiye wani mai bara, mai suna Lazarus, wanda jikinsa duk gyambuna ne. 21Shi kuwa yakan yi marmarin cin abin da yakan fāɗi daga tebur na mai arzikin nan. Har karnuka ma sukan zo su lashe gyambunansa.

22“Ana nan, sai mai baran ya mutu, kuma mala’iku suka ɗauke shi zuwa gefen Ibrahim. Mai arzikin ma ya mutu, aka kuma binne shi. 23A cikin jahannama ta wuta, inda yana shan azaba, ya ɗaga kai ya hangi Ibrahim can nesa, da kuma Lazarus a gefensa. 24Sai ya yi masa kira ya ce, ‘Baba, Ibrahim, ka ji tausayina, ka aiki Lazarus ya sa ɗan yatsarsa a ruwa, ya ɗiga mini a harshe saboda in ji sanyi, domin ina shan azaba cikin wannan wuta.’

25“Amma Ibrahim ya ce, ‘Ka tuna fa ɗana, a lokacin da kake duniya, ka sami abubuwa masu kyau naka, Lazarus kuwa ya sami munanan abubuwa. Amma yanzu ya sami ta’aziyya a nan, kai kuwa kana shan azaba. 26Ban da wannan duka ma, tsakaninmu da kai, akwai wani babban rami da aka yi, yadda waɗanda suke son ƙetarewa daga nan zuwa wurinku, ba za su iya ba, kuma ba mai iya ƙetarewa daga wurinku zuwa wurinmu.’

27“Ya amsa ya ce, ‘To, ina roƙonka, ya uba, ka aiki Lazarus zuwa gidan mahaifina, 28gama ina da ’yan’uwana biyar maza. Bari yă ba su gargaɗi, don kada su ma su zo wurin nan mai azaba.’

29“Ibrahim ya amsa ya ce, ‘Suna da Musa da Annabawa, ai, sai su saurare su.’

30“Sai ya ce, ‘A’a, ya uba, Ibrahim, in dai wani ya tashi daga matattu ya je wurinsu, za su tuba.’

31“Amma ya ce masa, ‘In ba su saurari Musa da Annabawa ba, kai, ko da wani ya tashi daga matattu ma, ba za su saurare shi ba.’ ”