Yohanna 3 – HCB & KJV

Hausa Contemporary Bible

Yohanna 3:1-36

Yesu ya koyar da Nikodimus

1Akwai wani Bafarisiye mai suna Nikodimus, wani ɗan majalisar Yahudawa. 2Ya zo wurin Yesu da dad dare ya ce, “Rabbi, mun sani kai malami ne daga Allah. Gama ba wanda zai iya yin waɗannan abubuwan banmamaki da kake yi in Allah ba ya tare da shi.”

3Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake faɗa maka, ba wanda zai iya ganin mulkin Allah sai an sāke haihuwarsa.”

4Nikodimus ya yi tambaya ya ce, “Yaya za a haifi mutum sa’ad da ya tsufa? Tabbatacce ba zai sāke koma sau na biyu a cikin mahaifiyarsa don a haife shi kuma ba!”

5Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake faɗa maka, ba wanda zai iya ganin mulkin Allah sai an haife shi ta wurin ruwa da kuma Ruhu. 6Jiki yakan haifi jiki, amma Ruhu yana haifi ruhu. 7Kada ka yi mamaki da na ce, ‘Dole ne a sāke haifarku.’ 8Iska takan hura zuwa inda take so. Kai kakan ji motsinta, sai dai ba ka iya sanin inda take fitowa ko kuwa inda za ta. Haka yake ga duk wanda aka haifa ta wurin Ruhu.”

9Nikodimus ya yi tambaya ya ce, “Yaya wannan zai yiwu?”

10Yesu ya ce, “Kai ma da kake malami na Isra’ila, ba ka fahimci waɗannan abubuwa ba? 11Gaskiya nake faɗa maka, muna magana a kan abin da muka sani, muka kuma shaida abin da muka gani ne, amma har yanzu kun ƙi ku karɓi shaidarmu. 12Na yi muku magana a kan abubuwan duniya amma ba ku gaskata ba; to, yaya za ku gaskata in na yi magana a kan abubuwan sama? 13Ba wanda ya taɓa hawa zuwa sama sai wanda ya sauka daga sama, wato, Ɗan Mutum.3.13 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā suna da Mutum, wanda yake cikin sama 14Kamar dai yadda Musa ya ɗaga maciji a hamada, haka dole ne a ɗaga Ɗan Mutum, 15don duk mai gaskata da shi ya sami rai madawwami.”

16Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami. 17Gama Allah bai aiki Ɗansa duniya don yă yi wa duniya hukunci ba, sai dai domin yă ceci duniya ta wurinsa. 18Duk wanda ya gaskata da shi ba za a yi masa hukunci ba, amma duk wanda bai gaskata ba an riga an yi masa hukunci domin bai gaskata da sunan wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗan Allah ba. 19Hukuncin shi ne, Haske ya zo cikin duniya, amma mutane suka so duhu a maimakon haske domin ayyukansu mugaye ne. 20Duk mai aikata mugunta yana ƙin haske, ba zai kuwa zo cikin haske ba don yana tsoro kada ayyukansa su tonu. 21Amma duk mai rayuwa bisa ga gaskiya yakan zo cikin haske, domin a gani a sarari cewa ayyukan da ya yi an yi su ne ta wurin Allah.

Shaidar Yohanna Mai Baftisma a kan Yesu

22Bayan wannan, Yesu da almajiransa suka tafi ƙauyukan Yahudiya, inda ya ɗan jima da su, ya kuma yi baftisma. 23To, Yohanna ma yana yin baftisma a Ainon kusa da Salim, saboda akwai ruwa da yawa a can, mutane kuwa suka yi ta zuwa don a yi musu baftisma. 24(Wannan kuwa kafin a sa Yohanna a kurkuku.) 25Sai gardama ta tashi tsakanin waɗansu almajiran Yohanna da wani mutumin Yahuda3.25 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā suna da da waɗansu Yahudawa a kan zancen al’adar tsarkakewa. 26Sai suka zo wurin Yohanna suka ce masa, “Rabbi, wancan mutumin da yake tare da kai a ƙetaren Urdun, wannan da ka ba da shaida a kansa sosai nan, yana baftisma, kuma kowa yana zuwa wurinsa.”

27Ga wannan zancen Yohanna ya amsa ya ce, “Mutum yakan karɓi kawai abin da aka ba shi ne daga sama. 28Ku kanku za ku shaida cewa na ce, ‘Ba ni ne Kiristi ba, sai dai an aiko ni ne in sha gabansa.’ 29Ango ne mai amarya. Abokin da yake masa hidima yakan jira ya kuma saurara masa, yakan kuma cika da farin ciki sa’ad da ya ji muryar ango. Wannan farin cikin kuwa nawa ne, ya kuma cika a yanzu. 30Dole ne yă yi ta ƙaruwa, ni kuma in yi ta raguwa.

31“Wannan da ya zo daga sama ya fi kowa; wannan da ya zo daga ƙasa na ƙasa ne, yana kuma magana kamar wanda ya zo daga ƙasa ne. Wannan da ya zo daga sama ya fi kowa. 32Yana ba da shaidar abin da ya gani da kuma ya ji, duk da haka ba wanda ya yarda da shaidarsa. 33Mutumin da ya yarda da ita ya tabbatar da cewa Allah mai gaskiya ne. 34Gama wannan da Allah ya aiko yakan faɗi kalmomin Allah ne, gama Allah yana ba da Ruhu babu iyaka. 35Uban yana ƙaunar Ɗan ya kuma danƙa kome a hannuwansa. 36Duk wanda ya gaskata da Ɗan yana da rai madawwami, amma duk wanda ya ƙi Ɗan ba zai sami rai ba, gama fushin Allah yana nan a bisansa.”

King James Version

John 3:1-36

1There was a man of the Pharisees, named Nicodemus, a ruler of the Jews: 2The same came to Jesus by night, and said unto him, Rabbi, we know that thou art a teacher come from God: for no man can do these miracles that thou doest, except God be with him. 3Jesus answered and said unto him, Verily, verily, I say unto thee, Except a man be born again, he cannot see the kingdom of God. 4Nicodemus saith unto him, How can a man be born when he is old? can he enter the second time into his mother’s womb, and be born? 5Jesus answered, Verily, verily, I say unto thee, Except a man be born of water and of the Spirit, he cannot enter into the kingdom of God. 6That which is born of the flesh is flesh; and that which is born of the Spirit is spirit. 7Marvel not that I said unto thee, Ye must be born again. 8The wind bloweth where it listeth, and thou hearest the sound thereof, but canst not tell whence it cometh, and whither it goeth: so is every one that is born of the Spirit. 9Nicodemus answered and said unto him, How can these things be? 10Jesus answered and said unto him, Art thou a master of Israel, and knowest not these things? 11Verily, verily, I say unto thee, We speak that we do know, and testify that we have seen; and ye receive not our witness. 12If I have told you earthly things, and ye believe not, how shall ye believe, if I tell you of heavenly things? 13And no man hath ascended up to heaven, but he that came down from heaven, even the Son of man which is in heaven.

14¶ And as Moses lifted up the serpent in the wilderness, even so must the Son of man be lifted up: 15That whosoever believeth in him should not perish, but have eternal life.

16¶ For God so loved the world, that he gave his only begotten Son, that whosoever believeth in him should not perish, but have everlasting life. 17For God sent not his Son into the world to condemn the world; but that the world through him might be saved.

18¶ He that believeth on him is not condemned: but he that believeth not is condemned already, because he hath not believed in the name of the only begotten Son of God. 19And this is the condemnation, that light is come into the world, and men loved darkness rather than light, because their deeds were evil. 20For every one that doeth evil hateth the light, neither cometh to the light, lest his deeds should be reproved. 21But he that doeth truth cometh to the light, that his deeds may be made manifest, that they are wrought in God.

22¶ After these things came Jesus and his disciples into the land of Judæa; and there he tarried with them, and baptized.

23¶ And John also was baptizing in Ænon near to Salim, because there was much water there: and they came, and were baptized. 24For John was not yet cast into prison.

25¶ Then there arose a question between some of John’s disciples and the Jews about purifying. 26And they came unto John, and said unto him, Rabbi, he that was with thee beyond Jordan, to whom thou barest witness, behold, the same baptizeth, and all men come to him. 27John answered and said, A man can receive nothing, except it be given him from heaven. 28Ye yourselves bear me witness, that I said, I am not the Christ, but that I am sent before him. 29He that hath the bride is the bridegroom: but the friend of the bridegroom, which standeth and heareth him, rejoiceth greatly because of the bridegroom’s voice: this my joy therefore is fulfilled. 30He must increase, but I must decrease. 31He that cometh from above is above all: he that is of the earth is earthly, and speaketh of the earth: he that cometh from heaven is above all. 32And what he hath seen and heard, that he testifieth; and no man receiveth his testimony. 33He that hath received his testimony hath set to his seal that God is true. 34For he whom God hath sent speaketh the words of God: for God giveth not the Spirit by measure unto him. 35The Father loveth the Son, and hath given all things into his hand. 36He that believeth on the Son hath everlasting life: and he that believeth not the Son shall not see life; but the wrath of God abideth on him.