Ruʼuya ta Yohanna 20 – HCB & PCB

Hausa Contemporary Bible

Ruʼuya ta Yohanna 20:1-15

Shekaru dubu

1Na kuma ga wani mala’ika yana saukowa daga sama, yana da mabuɗin Abis yana kuma riƙe da ƙaton sarƙa a hannunsa. 2Ya kama macijin, wannan tsohon maciji, wanda yake shi ne Iblis, ko kuwa Shaiɗan, aka kuma ɗaura shi har shekara dubu. 3Ya jefa shi cikin Abis, ya kuma kulle ya sa hatimi a kansa, don a hana kada yă ƙara ruɗin al’ummai, sai shekarun nan dubu sun cika. Bayan wannan, dole a sake shi na ɗan lokaci.

4Na ga kursiyoyi inda waɗanda aka ba su ikon shari’a suke zama a kai. Sai na ga rayukan waɗanda aka yanke kawunansu saboda shaidarsu don Yesu saboda kuma maganar Allah. Ba su yi wa dabban nan ko siffarta sujada ba, ba su kuma sami alamarta a goshinsu ko a hannuwansu ba. Suka sāke rayuwa daga matattu, suka yi mulki tare da Kiristi shekaru dubu. 5(Sauran matattu ba su sāke rayuwa ba, sai da shekaru dubun nan suka cika.) Wannan fa shi ne tashin matattu na farko. 6Masu albarka da kuma tsarki ne waɗanda suke da rabo a tashin matattu na farko. Mutuwa ta biyu ba ta da iko a kansu, sai dai za su zama firistocin Allah da kuma na Kiristi za su kuma yi mulki tare da shi na shekaru dubu.

Hallakar Shaiɗan

7Sa’ad da shekaru dubun nan suka cika, za a saki Shaiɗan daga kurkukun da yake, 8zai kuma fito don yă ruɗi al’ummai da suke a kursuyoyi huɗu na duniya, Gog da Magog, yă tattara su don yaƙi. Yawansu kuwa ya yi kamar yashi a bakin teku. 9Suka mamaye duk fāɗin duniya suka kuma kewaye sansanin mutanen Allah, birnin da yake ƙauna. Amma wuta ta fito daga sama ta cinye su. 10Aka jefa Iblis da ya ruɗe su cikin tafkin farar wuta, inda aka jefa dabban nan da annabin ƙaryan nan. Za a ba su azaba dare da rana har abada abadin.

An shari’anta matattu

11Sa’an nan na ga babban farin kursiyi da kuma wannan da yake zama a kansa. Duniya da sararin sama kuwa suka ɓace daga gabansa, babu wuri kuwa dominsu. 12Sai na ga matattu, babba da yaro tsaye a gaban kursiyin, aka kuma buɗe littattafai. Aka buɗe wani littafi, wanda yake shi ne littafin rai. Aka yi wa matattu shari’a bisa ga abin da suka aikata yadda yake a rubuce a cikin littattafai. 13Teku ya ba da matattu da suke cikinsa, mutuwa da Hades kuma suka ba da matattu da suke cikinsu, aka kuma yi wa kowane mutum shari’a bisa ga abin da ya aikata. 14Sa’an nan aka jefar da mutuwa da kuma Hades cikin tafkin wuta. Tafkin wutar nan kuwa shi ne mutuwa ta biyu. 15Duk wanda ba a sami sunansa a rubuce a cikin littafin rai ba, an jefar da shi cikin tafkin wutar nan.

Persian Contemporary Bible

مکاشفه 20:1-15

دوران هزار سالهٔ

1سپس، فرشته‌ای را ديدم كه از آسمان پايين آمد. او كليد چاه بی‌انتها را همراه می‌آورد و زنجيری محكم نيز در دست داشت. 2‏-3او اژدها را گرفت و به زنجير كشيد و برای مدت هزار سال به چاه بی‌انتها افكند. سپس در چاه را بست و قفل كرد، تا در آن هزار سال نتواند هيچ قومی را فريب دهد. پس از گذشت اين مدت، اژدها برای چند لحظه آزاد گذاشته خواهد شد. اژدها، همان مار قديم است كه اهريمن و شيطان نيز ناميده می‌شود.

4آنگاه تختهايی ديدم و كسانی بر آنها نشستند و به ايشان اختيار و قدرت دادرسی داده شد. سپس جانهای كسانی را ديدم كه به سبب اعلام پيغام عيسی و كلام خدا سر بريده شدند. همچنين جانهای آنانی را ديدم كه جاندار خبيث و مجسمه‌اش را نپرستيده بودند و علامتش را بر پيشانی و دستهای خود نداشتند. اينان همگی، زندگی را از سر نو آغاز كردند و با مسيح هزار سال سلطنت نمودند.

5اين «قيامت اول» است. قيامت بعدی در پايان آن هزار سال رخ خواهد داد؛ در آن زمان، بقيهٔ مردگان زنده خواهند شد.

6خوشبخت و مقدسند آنانی كه در اين قيامت اول سهمی دارند. اينان از مرگ دوم هيچ هراسی ندارند، بلكه كاهنان خدا و مسيح بوده، با او هزار سال سلطنت خواهند كرد.

نابودی نهايی شيطان

7پس از پايان آن هزار سال، شيطان از زندان آزاد خواهد شد. 8او بيرون خواهد رفت تا قومهای جهان يعنی جوج و ماجوج را فريب داده، برای جنگ متحد سازد. آنان سپاه عظيمی را تشكيل خواهند داد كه تعدادشان همچون ماسه‌های ساحل دريا بی‌شمار خواهد بود. 9ايشان در دشت وسيعی، خلق خدا و شهر محبوب اورشليم را از هر سو محاصره خواهند كرد. اما آتش از آسمان، از سوی خدا خواهد باريد و همه را خواهد سوزاند.

10سپس شيطان كه ايشان را فريب داده بود، به درياچهٔ آتش افكنده خواهد شد. درياچهٔ آتش همان جايی است كه با گوگرد می‌سوزد و آن جاندار خبيث و پيامبر دروغين او شبانه روز، تا به ابد، در آنجا عذاب می‌كشند.

روز داوری آخر

11آنگاه تخت بزرگ سفيدی را ديدم. بر آن تخت كسی نشسته بود كه زمين و آسمان از روی او گريختند و ناپديد شدند. 12سپس مرده‌ها را ديدم كه از بزرگ و كوچک در برابر خدا ايستاده‌اند. دفترها يكی پس از ديگری گشوده شد تا به دفتر حيات رسيد. مردگان همگی بر طبق نوشته‌های اين دفترها محاكمه شدند. 13بنابراين، دريا و زمين و قبرها، مرده‌هايی را كه در خود داشتند، تحويل دادند تا مطابق اعمالشان محاكمه شوند. 14آنگاه مرگ و دنيای مردگان به درياچهٔ آتش افكنده شد. اينست مرگ دوم، يعنی همان درياچهٔ آتش. 15هر كه نامش در دفتر حيات نبود، به درياچهٔ آتش افكنده شد.