Romawa 3 – HCB & KJV

Hausa Contemporary Bible

Romawa 3:1-31

Amincin Allah

1To, mece ce ribar zama mutumin Yahuda, ko kuwa mene ne amfanin kaciya? 2Akwai riba ƙwarai ta kowace hanya! Da farko dai, su ne aka danƙa wa kalmomin nan na Allah.

3Amma a ce waɗansu ba su da bangaskiya fa? Rashin bangaskiyarsu nan zai shafe amincin Allah? 4Ko kaɗan! Bari Allah yă zama mai gaskiya, kowane mutum kuma yă zama maƙaryaci. Kamar yadda yake a rubuce cewa,

“Gama a tabbatar kana da gaskiya, sa’ad da ka yi magana,

ka kuma yi nasara sa’ad da ka yi shari’a.”3.4 Zab 51.4

5Amma in rashin adalcinmu ya bayyana adalcin Allah a fili, me za mu ce ke nan? Za mu ce Allah ya yi rashin adalci ke nan da ya saukar da fushinsa a kanmu? (Ina magana kamar yadda mutum zai yi ne.) 6Sam, ko kusa! Da a ce haka ne, ta yaya Allah zai shari’anta duniya? 7Wani zai iya ce, “In a dalilin ƙaryata, gaskiyar Allah ta ƙara bayyana, har aka ƙara ɗaukaka shi, to, ta yaya zan zama mai zunubi, in ƙaryata tana kawo ɗaukaka ga Allah?” 8In haka ne, “Ba sai mu yi ta yin mugunta don yă zama hanyar samun nagarta ba”? Kamar yadda masu baƙar magana game da mu suna cewa wai haka muke faɗa. Tabbatacce za a hukunta irin waɗannan da hukuncin da ya dace da su.

Babu mai adalci

9To, me za mu ce ke nan? Mun fi su ke nan? Ina, ko kaɗan! Mun riga mun zartar cewa da Yahudawa da Al’ummai duk suna a ƙarƙarshin zunubi. 10Kamar yadda yake a rubuce cewa,

“Babu wani mai adalci, babu ko ɗaya;

11babu wani mai fahimta,

babu wani mai neman Allah.

12Duk sun kauce gaba ɗaya,

sun zama marasa amfani;

babu wani mai aikata nagarta,

babu ko ɗaya.”3.12 Zab 14.1-3; Zab 53.1-3; M Had 7.20

13“Maƙogwaronsu kamar buɗaɗɗun kaburbura ne,

harsunansu suna yin ƙarya.”3.13 Zab 5.9

“Dafin mugun maciji yana a leɓunansu.”3.13 Zab 140.3

14“Bakunansu sun cike da la’ana da ɗacin rai.”3.14 Zab 10.7

15“Ƙafafunsu suna saurin kai su zuwa ga zub da jini;

16hallaka da baƙin ciki suna ko’ina a hanyoyinsu,

17ba su kuma san hanyar salama ba.”3.17 Ish 59.7,8

18“Babu tsoron Allah a idanunsu.”3.18 Zab 36.1

19Yanzu mun san cewa dukan abin da doka ta ce, tana magana ne ga waɗanda suke ƙarƙarshin doka, saboda a rufe kowane baki; dukan duniya kuma ta ba da lissafin kanta a gaban Allah. 20Saboda haka babu wanda Allah zai ce da shi mai adalci ta wurin kiyaye doka kawai; a maimako, ta wurin doka ne muke sane da zunubi.

Adalci ta wurin bangaskiya

21Amma yanzu an bayyana wani adalci daga Allah, wannan adalcin bai danganta ga doka ba, Doka da Annabawa suna ba da shaida game da wannan adalci. 22Wannan adalcin Allah yana zuwa ta wurin bangaskiya a cikin Yesu Kiristi ga dukan waɗanda suka ba da gaskiya ne. Ba bambanci, 23gama duka sun yi zunubi suka kuma kāsa ga ɗaukakar Allah, 24an kuma kuɓutar da su kyauta ta wurin alherinsa bisa ga aikin fansar da ya zo ta wurin Yesu Kiristi. 25Allah ya miƙa Yesu Kiristi a matsayin hadayar kafara, ta wurin bangaskiya cikin jininsa. Ya yi haka domin yă nuna adalcinsa, domin a cikin haƙurinsa bai hukunta zunuban da aka aikata a dā ba 26ya yi haka domin yă nuna adalcinsa a wannan lokaci, saboda yă zama mai adalci da mai kuɓutar da waɗanda suke ba da gaskiya a cikin Yesu.

27To, me za mu yi taƙama a kai? Babu wani abin da zamu yi taƙama a kai. A kan wace ƙa’ida ce za mu yi taƙama? Ta hanyar bin doka ne? A’a, sai dai ta wurin bangaskiya. 28Gama mun tsaya a kan cewa ta wurin bangaskiya ne ake kuɓutar da mutum, ba ta wurin kiyaye doka ba. 29Allah ɗin, Allahn Yahudawa ne kaɗai? Shi ba Allahn Al’ummai ba ne? I, shi Allahn Al’ummai ne ma, 30da yake Allah ɗaya ne kaɗai, shi kuma zai kuɓutar da masu kaciya bisa ga bangaskiya da kuma marasa kaciya ta wurin wannan bangaskiya ɗin. 31To, za mu soke dokar saboda wannan bangaskiyar ne? Ko kaɗan! A maimako, sai ma tabbatar da ita muke yi.

King James Version

Romans 3:1-31

1What advantage then hath the Jew? or what profit is there of circumcision? 2Much every way: chiefly, because that unto them were committed the oracles of God. 3For what if some did not believe? shall their unbelief make the faith of God without effect? 4God forbid: yea, let God be true, but every man a liar; as it is written, That thou mightest be justified in thy sayings, and mightest overcome when thou art judged. 5But if our unrighteousness commend the righteousness of God, what shall we say? Is God unrighteous who taketh vengeance? (I speak as a man) 6God forbid: for then how shall God judge the world? 7For if the truth of God hath more abounded through my lie unto his glory; why yet am I also judged as a sinner? 8And not rather, (as we be slanderously reported, and as some affirm that we say,) Let us do evil, that good may come? whose damnation is just.

9What then? are we better than they? No, in no wise: for we have before proved both Jews and Gentiles, that they are all under sin; 10As it is written, There is none righteous, no, not one: 11There is none that understandeth, there is none that seeketh after God. 12They are all gone out of the way, they are together become unprofitable; there is none that doeth good, no, not one. 13Their throat is an open sepulchre; with their tongues they have used deceit; the poison of asps is under their lips: 14Whose mouth is full of cursing and bitterness: 15Their feet are swift to shed blood: 16Destruction and misery are in their ways: 17And the way of peace have they not known: 18There is no fear of God before their eyes.

19Now we know that what things soever the law saith, it saith to them who are under the law: that every mouth may be stopped, and all the world may become guilty before God. 20Therefore by the deeds of the law there shall no flesh be justified in his sight: for by the law is the knowledge of sin.

21But now the righteousness of God without the law is manifested, being witnessed by the law and the prophets; 22Even the righteousness of God which is by faith of Jesus Christ unto all and upon all them that believe: for there is no difference: 23For all have sinned, and come short of the glory of God; 24Being justified freely by his grace through the redemption that is in Christ Jesus: 25Whom God hath set forth to be a propitiation through faith in his blood, to declare his righteousness for the remission of sins that are past, through the forbearance of God; 26To declare, I say, at this time his righteousness: that he might be just, and the justifier of him which believeth in Jesus. 27Where is boasting then? It is excluded. By what law? of works? Nay: but by the law of faith. 28Therefore we conclude that a man is justified by faith without the deeds of the law. 29Is he the God of the Jews only? is he not also of the Gentiles? Yes, of the Gentiles also: 30Seeing it is one God, which shall justify the circumcision by faith, and uncircumcision through faith. 31Do we then make void the law through faith? God forbid: yea, we establish the law.