Mattiyu 5 – HCB & CCBT

Hausa Contemporary Bible

Mattiyu 5:1-48

Albarku

1Ganin taron mutane, sai ya hau kan gefen dutse ya zauna.

(Luka 6.20-23)

Almajiransa kuwa suka zo wurinsa, 2sai ya fara koya musu.

Yana cewa,

3“Masu albarka ne waɗanda suke matalauta a ruhu,

gama mulkin sama nasu ne.

4Masu albarka ne waɗanda suke makoki,

gama za a yi musu ta’aziyya.

5Masu albarka ne waɗanda suke masu tawali’u,

gama za su gāji duniya.

6Masu albarka ne waɗanda suke jin yunwa da ƙishirwa don gani an yi adalci,

gama za a ƙosar da su.

7Masu albarka ne waɗanda suke masu jinƙai,

gama za a nuna musu jinƙai.

8Masu albarka ne waɗanda suke masu tsabtar zuciya,

gama za su ga Allah.

9Masu albarka ne waɗanda suke masu ƙulla zumunci,

gama za a kira su ’ya’yan Allah.

10Masu albarka ne waɗanda ake tsananta musu don gani an yi adalci,

gama mulkin sama nasu ne.

11“Masu albarka ne ku, sa’ad da mutane suke zaginku, suna tsananta muku, suna kuma faɗin kowace irin muguwar magana a kanku saboda ni. 12Ku yi murna ku kuma yi farin ciki, domin ladarku mai yawa ne a sama, gama haka suka tsananta wa annabawan da suka riga ku.

Gishiri da kuma haske

(Markus 9.50; Luka 14.34,35)

13“Ku ne gishirin duniya, amma in gishiri ya rabu da daɗin ɗanɗanonsa, yaya za a sāke mai da daɗin ɗanɗanonsa? Ba shi da sauran amfani, sai dai a zubar da shi mutane kuma su tattaka.

14“Ku ne hasken duniya. Birnin da yake a bisan tudu ba ya ɓoyuwa. 15Mutane ba sa ƙuna fitila su rufe ta da murfi. A maimako, sukan ajiye ta a kan wurin ajiye fitila, takan kuma ba da haske ga kowa a cikin gida. 16Haka ma, bari haskenku yă haskaka a gaban mutane, domin su ga ayyukanku masu kyau, su kuwa yabi Ubanku da yake cikin sama.

Cikar doka

17“Kada ku yi tsammani na zo ne domin in kawar da Doka ko kuma Annabawa; ban zo domin in kawar da su ba ne, sai dai domin in ciccika su. 18Gaskiya nake gaya muku, kafin sama da ƙasa sun shuɗe, babu ko ɗan wasali, babu wani ɗigo ta kowace hanya da zai ɓace daga Dokar, sai an cika kome. 19Duk wanda ya karya ɗaya daga cikin mafi ƙanƙanta na umarnan nan, ya kuma koya wa waɗansu su yi haka, za a ce da shi mafi ƙanƙanta a mulkin sama. Amma duk wanda ya aikata, ya kuma koyar da waɗannan umarnai, za a kira shi mai girma a cikin mulkin sama. 20Gama ina faɗa muku cewa in dai adalcinku bai fi na Farisiyawa da na malaman dokoki ba, faufau, ba za ku shiga mulkin sama ba.

Kisankai

21“Kun dai ji an faɗa wa mutanen dā cewa, ‘Kada ka yi kisankai;5.21 Fit 20.13 kuma duk wanda ya yi kisankai za a hukunta shi.’ 22Amma ina gaya muku, duk wanda ya yi fushi da ɗan’uwansa, za a hukunta shi. Kuma duk wanda ya ce wa ɗan’uwansa ‘Raka,’5.22 Kalmar Arameyik ta reni za a kai shi gaban Majalisa. Amma duk wanda ya ce, ‘Kai wawa!’ Zai kasance a hatsarin shiga jahannama ta wuta.

23“Saboda haka, in kana cikin ba da baikonka a kan bagade, a can kuwa ka tuna cewa ɗan’uwanka yana riƙe da kai a zuci, 24sai ka bar baikonka a can gaban bagade. Ka je ka shirya tukuna da ɗan’uwanka; sa’an nan ka zo ka ba da baikonka.

25“Ka yi hanzari ka shirya al’amura da maƙiyinka wanda yake ƙararka a kotu. Ka yi haka, tun kana tare da shi a kan hanya, in ba haka ba, zai miƙa ka ga alƙali, alƙali kuma yă miƙa ka ga ɗan sanda, mai yiwuwa kuwa a jefa ka a kurkuku. 26Gaskiya nake gaya maka, ba za ka fita ba, sai ka biya kobo na ƙarshe.

Zina

27“Kun dai ji an faɗa, ‘Kada ka yi zina.’5.27 Fit 20.14 28Amma ina gaya muku, duk wanda ya dubi mace, sa’an nan ya yi sha’awarta a zuci, ya riga ya yi zina ke nan da ita a zuciyarsa. 29In idonka na dama yana sa ka yin zunubi, ƙwaƙule shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓin jikinka, da a jefa jikinka ɗungum a cikin jahannama ta wuta. 30In kuma hannunka na dama yana sa ka yin zunubi, yanke shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓin jikinka, da a jefa jikinka ɗungum a cikin jahannama ta wuta.

Kashen aure

(Mattiyu 19.9; Markus 10.11,12; Luka 16.18)

31“An kuma faɗa, ‘Duk wanda ya saki matarsa, dole yă ba ta takardar saki.’5.31 M Sh 24.1 32Amma ina gaya muku, duk wanda ya saki matarsa in ba a kan laifin zina ba, ya sa ta zama mazinaciya ke nan, kuma duk wanda ya auri macen da mijinta ya sake, shi ma yana zina ne.

Rantsuwa

33“Har wa yau dai kun ji an faɗa wa mutane a dā, ‘Kada ka karya alkawarinka, sai dai ka cika alkawaran da ka yi wa Ubangiji.’ 34Amma ina gaya muku, Kada ku yi rantsuwa sam, ko da sama, domin kursiyin Allah ne; 35ko da ƙasa, domin matashin ƙafafunsa ne; ko kuma da Urushalima, domin birnin Babban Sarki ne. 36Kada kuma ka rantse da kanka, domin ba za ka iya mai da ko gashi ɗaya yă zama fari ko baƙi ba. 37Abin da ya kamata ku ce kawai, shi ne, I, ko A’a. Abin da ya wuce haka kuwa daga wurin Mugun nan yake.

Ramuwa

(Luka 6.29,30)

38“Kun dai ji an faɗa, ‘Ido domin ido, haƙori kuma domin haƙori.’5.38 Fit 21.24; Fir 24.20; M Sh 19.21 39Amma ina gaya muku, Kada ku yi tsayayya da mugun mutum. In wani ya mare ka a kumatun dama, juya masa ɗayan ma. 40In kuma wani yana so yă yi ƙararka yă ƙwace rigarka, to, ba shi mayafinka ma. 41In wani ya tilasta ka yin tafiya mil ɗaya, to, tafi tare da shi mil biyu. 42Ka ba wa duk wanda ya roƙe ka abu, kada kuma ka hana wa wanda yake neman bashi daga gare ka.

Ƙauna don abokan gāba

(Luka 6.27,28,32-36)

43“Kun dai ji an faɗa, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka,5.43 Fir 19.18 ka kuma ƙi abokin gābanka.’ 44Amma ina gaya muku, ku ƙaunaci abokan gābanku5.44 Waɗansu rubuce-rubucen hannun da ba su jima ba suna da abokan gāba, ku sa wa waɗanda suke la’antarku albarka, ku yi wa waɗanda suke ƙinku alheri kuma ku yi wa waɗanda suke tsananta muku addu’a, 45don ku zama ’ya’yan Ubanku na sama. Shi yakan sa ranarsa ta haskaka a kan mugaye da masu kirki; yakan kuma sako ruwan sama a bisa masu adalci da marasa adalci. 46In masoyarku kawai kuke ƙauna, wace lada ce gare ku? Ko masu karɓar haraji ma ba haka suke yi ba? 47In kuwa kuna gai da ’yan’uwanku ne kaɗai, me kuke yi fiye da waɗansu? Marasa bin Allah ma ba haka suke yi ba? 48Saboda haka sai ku zama cikakku, yadda Ubanku na sama yake cikakke.

Chinese Contemporary Bible (Traditional)

馬太福音 5:1-48

八福

1耶穌看見這些人群,就上了山,剛坐下,門徒便走到祂跟前, 2祂就開口教導他們,說:

3「心靈貧窮的人有福了,

因為天國是他們的。

4哀慟的人有福了,

因為他們必得安慰。

5謙和的人有福了,

因為他們必承受土地。

6愛慕公義如饑似渴的人有福了,

因為他們必得飽足。

7心存憐憫的人有福了,

因為他們必蒙上帝的憐憫。

8心靈純潔的人有福了,

因為他們必看見上帝。

9使人和睦的人有福了,

因為他們必被稱為上帝的兒女。

10為義受迫害的人有福了,

因為天國是他們的。

11「人們因為我的緣故侮辱、迫害、肆意毀謗你們,你們就有福了。 12要歡喜快樂,因為你們在天上有很大的獎賞。他們也曾這樣迫害以前的先知。

鹽和光

13「你們是世上的鹽。如果鹽失去鹹味,怎能使它再變鹹呢?它將毫無用處,只有被丟在外面任人踐踏。 14你們是世上的光,如同建在山上的城一樣無法隱藏。 15人點亮了燈,不會把它放在斗底下,而是放在燈臺上,好照亮全家。 16同樣,你們的光也應當照在人面前,好讓他們看見你們的好行為,便讚美你們天上的父。

成全律法

17「不要以為我是來廢除律法和先知書,我不是來廢除,乃是來成全。 18我實在告訴你們,就是到天地都消失了,律法的一點一劃都不會廢除,全都要成就。 19所以,誰違背這些誡命中最小的一條,並教導別人違背,誰在天國將被稱為最小的。但誰遵守這些誡命,並教導別人遵守,誰在天國將被稱為大的。 20我告訴你們,除非你們的義勝過律法教師和法利賽人的義,否則斷不能進天國。

論仇恨

21「你們聽過吩咐古人的話,『不可殺人,殺人的要受審判。』 22但我告訴你們,凡無緣無故5·22 有古卷無「無緣無故」。向弟兄發怒的,要受審判;凡罵弟兄是白癡的,要受公會5·22 公會」是當時猶太人的最高司法機構,處理宗教、道德和倫理等事務。的審判;凡罵弟兄是笨蛋的,難逃地獄的火。

23「所以,你在祭壇前獻祭的時候,要是想起有弟兄和你有過節, 24就該把祭物留在祭壇前,先去跟他和好,然後再來獻祭。

25「趁著你和告你的人還在去法庭的路上,你要趕緊與對方和解。不然,他會把你交給審判官,審判官會把你交給差役關進監牢。 26我實在告訴你,要是有一分錢沒有還清,你絕不能從那裡出來。

論通姦

27「你們聽過這樣的話,『不可通姦。』 28但我告訴你們,凡看見婦女就動淫念的,他在心裡已經犯了通姦罪。 29如果你的右眼使你犯罪,就把它剜掉!寧可失去身體的一部分,也比整個人下地獄好。 30如果你的右手使你犯罪,就把它砍掉!寧可失去身體的一部分,也比整個人下地獄好。

論休妻

31「還有話說,『人若休妻,必須給她休書』。 32但我告訴你們,除非是妻子不貞,否則,休妻就是使妻子犯通姦罪,娶被休女子的人也犯了通姦罪。

論起誓

33「你們也聽過吩咐古人的話,『不可違背誓言,總要向主遵守所起的誓。』 34但我告訴你們,不可起誓。不可指著天起誓,因為天是上帝的寶座。 35不可指著地起誓,因為地是上帝的腳凳。不可指著聖城耶路撒冷起誓,因為那是大君王的城。 36也不可指著自己的頭起誓,因為你不能使一根頭髮變黑或變白。 37你們說話,是就說是,不是就說不是,多說的便是來自那惡者5·37 那惡者即魔鬼,又名撒旦。

論愛仇敵

38「你們聽過這樣的話,『以眼還眼,以牙還牙。』 39但我告訴你們,不要跟惡人作對。有人打你的右臉,連左臉也轉過來讓他打。 40有人想控告你,要奪取你的內衣,連外衣也給他。 41有人強迫你走一里路,你就跟他走二里路。 42有求你的,就給他;有向你借的,不可拒絕他。

43「你們聽過這樣的話,『要愛鄰居,恨仇敵。』 44但我告訴你們,要愛仇敵,為迫害你們的人禱告。 45這樣,你們才是天父的孩子。因為祂讓陽光照好人也照壞人,降雨給義人也給惡人。 46如果你們只愛那些愛你們的人,有什麼值得嘉獎的呢?就是稅吏也會這樣做。 47如果你們只問候自己的弟兄,有什麼特別呢?就是外族人也會這樣做。 48所以,你們要純全,正如你們的天父是純全的。