Mattiyu 20 – HCB & NRT

Hausa Contemporary Bible

Mattiyu 20:1-34

Misalin ma’aikata a gonar inabi

1“Mulkin sama yana kama da wani mai gona, wanda ya fita da sassafe don yă yi hayar mutane su yi aiki a gonar inabinsa. 2Ya yarda yă biya su dinari guda a yini, sai ya tura su gonar inabinsa.

3“Wajen sa’a ta uku, ya fita sai ya ga waɗansu suna tsattsaye a bakin kasuwa ba sa kome. 4Ya ce musu, ‘Ku ma ku tafi gonar inabina ku yi aiki, zan kuwa biya ku abin da ya dace.’ 5Saboda haka suka tafi.

“Ya sāke fita a sa’a ta shida da kuma sa’a ta tara, ya sāke yin haka. 6Wajen sa’a ta goma sha ɗaya, ya sāke fita, ya tarar da waɗansu har yanzu suna tsattsaye. Ya tambaye su, ‘Don me kuke yini tsattsaye a nan ba kwa kome?’

7“Suka amsa, ‘Don ba wanda ya ɗauke mu aiki.’

“Ya ce musu, ‘Ku ma ku je ku yi aiki a gonar inabina.’

8“Sa’ad da yamma ta yi, sai mai gonar inabin ya ce wa wakilinsa, ‘Kira ma’aikatan, ka biya su hakkin aikinsu, fara daga waɗanda aka ɗauke su a ƙarshe har zuwa na farko.’

9“Ma’aikatan da ka ɗauka wajen sa’a ta goma sha ɗaya suka zo, kowannensu kuwa ya karɓi dinari guda. 10Saboda haka da waɗanda aka ɗauka da fari suka zo, sun zaci za su sami fiye da haka. Amma kowannensu ma ya karɓi dinari guda. 11Sa’ad da suka karɓa, sai suka fara yin gunaguni a kan mai gonar. 12Suna cewa, ‘Waɗannan mutanen da aka ɗauka a ƙarshe sun yi aikin sa’a ɗaya ne kawai, ka kuma mai da su daidai da mu da muka yini muna faman aiki, muka kuma sha zafin rana.’

13“Amma ya amsa wa ɗayansu ya ce, ‘Aboki, ban cuce ka ba. Ba ka yarda ka yi aiki a kan dinari guda ba? 14Ka karɓi hakkinka ka tafi. Ni na ga damar ba waɗannan na ƙarshe daidai da yadda na ba ka. 15Ba ni da ikon yin abin da na ga dama da kuɗina ne? Ko kana kishi saboda ni mai kyauta ne?’

16“Saboda haka fa, na ƙarshe za su zama na farko, na farko kuma su zama na ƙarshe.”

Yesu ya sāke yin zancen mutuwarsa

(Markus 10.32-34; Luka 18.31-34)

17To, da Yesu yana haurawa zuwa Urushalima, sai ya ja almajiran nan goma sha biyu gefe, ya ce musu, 18“Za mu haura zuwa Urushalima, za a kuma bashe Ɗan Mutum ga manyan firistoci da malaman dokoki. Za su yi masa hukuncin kisa 19za su kuma bashe shi ga Al’ummai su yi masa ba’a, su yi masa bulala, su kuma gicciye shi. A rana ta uku kuma a tashe shi!”

Roƙon mahaifiya

(Markus 10.35-45)

20Sai mahaifiyar ’ya’yan Zebedin nan ta zo wurin Yesu tare da ’ya’yanta, da ta durƙusa a ƙasa, sai ta roƙe shi yă yi mata wani abu.

21Ya yi tambaya ya ce, “Mene ne kike so?”

Ta ce, “Ka sa daga cikin ’ya’yan nan nawa biyu, ɗaya yă zauna a damarka, ɗaya kuma a hagunka, a mulkinka.”

22Yesu ya ce musu, “Ba ku san abin da kuke roƙo ba. Za ku iya sha daga kwaf da zan sha?”

Suka amsa, “Za mu iya.”

23Yesu ya ce musu, “Tabbatacce za ku sha daga kwaf na, sai dai zama a damana, ko haguna, ba ni nake da izinin bayarwa ba. Waɗannan wurare na waɗanda Ubana ya shirya wa ne.”

24Da goman suka ji haka, sai suka yi fushi da ’yan’uwan nan biyu. 25Yesu ya kira su wuri ɗaya ya ce, “Kun san cewa masu mulkin Al’ummai sukan nuna musu iko, hakimansu kuma sukan gasa musu iko. 26Ba haka zai kasance da ku ba. Maimakon haka, duk mai son zama babba a cikinku, dole yă zama bawanku, 27kuma duk mai son zama shugaba, dole yă zama bawanku, 28kamar yadda Ɗan Mutum bai zo don a bauta masa ba, sai dai don yă yi bauta, yă kuma ba da ransa fansa saboda mutane da yawa.”

Makafi biyu sun sami ganin gari

(Markus 10.46-52; Luka 18.35-43)

29Sa’ad da Yesu da almajiransa suke barin Yeriko, sai wani babban taro ya bi shi. 30Makafi biyu kuwa suna zaune a bakin hanya, da suka ji cewa Yesu yana wucewa, sai suka ɗaga murya suka ce, “Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka ji tausayinmu!”

31Mutane suka tsawata musu, suka ce musu su yi shiru. Sai suka ƙara ɗaga murya suna cewa, “Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka ji tausayinmu!”

32Yesu ya tsaya ya kira su. Ya tambaye su, “Me kuke so in yi muku?”

33Suka amsa suka ce, “Ubangiji, muna so mu sami ganin gari.”

34Sai Yesu ya ji tausayinsu, ya taɓa idanunsu. Nan da nan kuwa suka sami ganin gari, suka kuma bi shi.

New Russian Translation

Матфея 20:1-34

Притча о равной плате нанятым работникам

1– Небесное Царство подобно хозяину, который рано утром вышел нанять людей на работу в своем винограднике. 2Он договорился с ними, что заплатит им по динарию за день работы, и послал их в свой виноградник. 3В третьем часу20:3 То есть в девять часов. он опять вышел и увидел, что на площади еще стоят люди без работы. 4Он говорит им: «Идите и вы работать в мой виноградник, и я заплачу вам по справедливости». 5Те пошли. В шестом и в девятом часу он опять выходил и делал то же самое. 6Потом он вышел в одиннадцатом часу и вновь нашел стоящих людей. «Что вы тут стоите весь день без дела?» – спросил он их. 7«Никто нас не нанял», – ответили те. «Идите и вы работать в мой виноградник», – говорит им хозяин. 8Когда наступил вечер, хозяин сказал своему управляющему: «Позови всех работников и выдай им плату. Начни с тех, которые были наняты последними, и в конце рассчитайся с теми, кто нанят утром». 9Работники, которых наняли в одиннадцатом часу, пришли, и каждый из них получил по динарию. 10Когда подошла очередь работников, нанятых первыми, они ожидали, что получат больше, но каждый из них тоже получил по одному динарию. 11Когда с ними расплатились, они стали роптать на хозяина: 12«Те, кого ты нанял последними, работали всего один час, и ты заплатил им столько же, сколько и нам, а мы трудились в такую жару весь день!» 13Хозяин ответил одному из них: «Друг, я же не обманываю тебя. Разве ты не согласился работать за один динарий? 14Так возьми свою плату и иди. А я хочу заплатить тем, кого я нанял последними, столько же, сколько и тебе. 15Не вправе ли я распоряжаться своими деньгами так, как хочу? Или, может, моя щедрость вызывает в тебе зависть?» 16Так вот, последние будут первыми, и первые – последними.

Иисус в третий раз говорит о Своей смерти и воскресении

(Мк. 10:32-34; Лк. 18:31-33)

17По дороге в Иерусалим Иисус отвел двенадцать учеников в сторону и сказал им:

18– Вот, мы восходим в Иерусалим, там Сына Человеческого выдадут первосвященникам и учителям Закона. Они приговорят Его к смерти 19и отдадут язычникам на глумление, бичевание и распятие. Но на третий день Он воскреснет.

Не господствуйте, но служите

(Мк. 10:35-45; Лк. 22:24-27)

20Потом к Иисусу подошла мать сыновей Зеведея вместе с сыновьями. Кланяясь, она обратилась к Нему с просьбой.

21– Что ты хочешь? – спросил Он ее.

Она сказала:

– Вели, чтобы оба мои сына сели один по правую, а другой по левую руку от Тебя в Твоем Царстве.

22– Вы не знаете, о чем просите, – ответил Иисус. – Можете ли пить чашу, которую Я буду пить, или креститься крещением, которым Я крещусь?20:22 В древнейших рукописях отсутствуют слова: «или креститься крещением, которым Я крещусь».

– Можем, – ответили они.

23Иисус сказал им:

– Пить из Моей чаши вы будете, и крещением, которым Я крещусь, будете креститься, но кому сидеть по правую, а кому по левую руку от Меня, решаю не Я, эти места принадлежат тем, кому они назначены Моим Отцом.

24Когда остальные десять учеников услышали это, они рассердились на братьев. 25Иисус же подозвал их и сказал:

– Вы знаете, что языческие правители господствуют над своими народами, и владеет людьми их знать. 26У вас пусть будет не так. Наоборот, кто хочет стать среди вас самым великим, должен быть вам слугой, 27и кто хочет быть среди вас первым, пусть будет вам слугой. 28Ведь и Сын Человеческий пришел не для того, чтобы Ему служили, но чтобы служить другим и отдать Свою жизнь как выкуп за многих.

Исцеление двух слепых

(Мк. 10:46-52; Лк. 18:35-43)

29Когда Иисус и ученики покидали Иерихон, за ними следовало множество людей. 30У дороги сидели двое слепых, которые, услышав, что мимо идет Иисус, стали кричать:

– Господи, Сын Давидов, сжалься над нами!

31Люди стали говорить им, чтобы они замолчали, но те кричали еще громче:

– Господи, Сын Давидов, сжалься над нами!

32Иисус остановился и позвал их.

– Что вы хотите, чтобы Я сделал для вас? – спросил Он.

33– Господи, хотим прозреть, – ответили те.

34Иисусу стало их жаль, и Он прикоснулся к их глазам. Слепые сразу же обрели зрение и пошли за Ним.