Mattiyu 14 – HCB & HHH

Hausa Contemporary Bible

Mattiyu 14:1-36

An yanke kan Yohanna Mai Baftisma

(Markus 6.14-29; Luka 9.7-9)

1A lokacin nan sarki Hiridus ya ji labarin Yesu, 2sai ya ce wa fadawansa, “Wannan Yohanna Mai Baftisma ne; ya tashi daga matattu! Shi ya sa abubuwan banmamakin nan suke faruwa ta wurinsa.”

3To, dā Hiridus ya kama Yohanna ya daure, ya kuma sa shi cikin kurkuku saboda Hiridiyas, matar ɗan’uwansa Filibus, 4gama Yohanna ya dinga ce masa, “Ba daidai ba ne ka aure ta.” 5Hiridus ya so yă kashe Yohanna, amma yana jin tsoron mutane, don sun ɗauka shi annabi ne.

6A bikin tuna da ranar haihuwar Hiridus, diyar Hiridiyas ta yi musu rawa ta kuma gamsar da Hiridus ƙwarai, 7har ya yi alkawari da rantsuwa cewa zai ba ta duk abin da ta roƙa. 8Da mahaifiyarta ta zuga ta, sai ta ce, “Ba ni a cikin kwanon nan, kan Yohanna Mai Baftisma.” 9Sarki ya yi baƙin ciki, amma saboda rantsuwarsa da kuma baƙinsa, sai ya ba da umarni a ba ta abin da ta roƙa 10ya kuma sa aka yanke kan Yohanna a kurkuku. 11Aka kawo kansa cikin kwano aka ba yarinyar, ita kuma ta kai wa mahaifiyarta. 12Almajiran Yohanna suka zo suka ɗauki gawarsa suka binne. Sa’an nan suka je suka gaya wa Yesu.

Yesu ya ciyar da dubu biyar

(Markus 6.30-44; Luka 9.10-17; Yohanna 6.1-14)

13Sa’ad da Yesu ya ji abin da ya faru, sai ya shiga jirgin ruwa ya janye shi kaɗai zuwa wani wuri inda ba kowa. Da jin haka, taron mutane suka bi shi da ƙafa daga garuruwa. 14Da Yesu ya sauka ya kuma ga taro mai yawa, sai ya ji tausayinsu ya kuma warkar da marasa lafiyarsu.

15Da yamma ta yi, sai almajiransa suka zo wurinsa suka ce, “Wurin nan fa ba kowa, ga shi kuma rana ta kusa fāɗuwa. Ka sallami taron don su shiga ƙauyuka su nemi wa kansu abinci.”

16Yesu ya amsa, “Ba su bukata su tafi. Ku ku ba su wani abu su ci.”

17Suka ce, “Burodi biyar da kifi biyu ne kawai muke da su a nan.”

18Ya ce, “Ku kawo mini su a nan.” 19Sai ya umarci mutanen su zazzauna a kan ciyawa. Da ya ɗauki burodi biyar da kifin biyun nan ya dubi sama, ya yi godiya ya kuma kakkarya burodin. Sa’an nan ya ba wa almajiransa, almajiran kuwa suka ba wa mutane. 20Duk suka ci suka ƙoshi, almajiran kuwa suka kwashe ragowar gutsattsarin cike da kwanduna goma sha biyu. 21Yawan waɗanda suka ci, sun yi wajen maza dubu biyar, ban da mata da yara.

Yesu ya yi tafiya a kan ruwa

(Markus 6.45-52; Yohanna 6.15-21)

22Nan da nan Yesu ya sa almajiran su shiga jirgin ruwa su sha gabansa, su haye zuwa ɗayan hayin, yayinda shi kuma yă sallami taron. 23Bayan ya sallame su, sai ya haura bisan gefen dutse shi kaɗai don yă yi addu’a. Da yamma ta yi, yana can shi kaɗai, 24jirgin ruwan kuwa ya riga ya yi nesa da gaci, yana fama da raƙuman ruwa domin iska tana gāba da shi.

25Wajen tsaro na huɗu na dare, sai Yesu ya nufe su, yana takawa a kan tafkin. 26Sa’ad da almajiran suka gan shi yana takawa a kan tafkin, sai tsoro ya kama su. Suka yi ihu don tsoro suka ce, “Fatalwa ce.”

27Amma nan da nan Yesu ya ce musu, “Ku yi ƙarfin hali! Ni ne. Kada ku ji tsoro.”

28Sai Bitrus ya amsa ya ce, “Ubangiji in kai ne ka ce mini in zo wurinka a kan ruwan.”

29Ya ce, “Zo.”

Sai Bitrus ya fita daga jirgin ruwan, ya taka a kan ruwan ya nufe wajen Yesu. 30Amma da ya ga haukar iskar, sai ya ji tsoro, ya kuma fara nutsewa, sai ya yi ihu ya ce, “Ubangiji, ka cece ni!”

31Nan da nan Yesu ya miƙa hannu ya kamo shi ya ce, “Kai mai ƙarancin bangaskiya, don me ka yi shakka?”

32Da suka hau jirgin ruwan, sai iskar ta kwanta. 33Waɗanda suke cikin jirgin ruwan kuwa suka yi masa sujada, suna cewa, “Gaskiya kai Ɗan Allah ne.”

(Markus 6.45-52; Yohanna 6.15-21)

34Sa’ad da suka haye, sai suka sauka a Gennesaret. 35Da mutanen wurin suka gane da Yesu, sai suka kai labari a ko’ina a ƙauyukan da suke kewaye. Mutane suka kawo masa dukan marasa lafiyarsu 36suka kuwa roƙe shi yă bar marasa lafiya su taɓa ko da gefen rigarsa kawai, duk waɗanda suka taɓa shi kuwa suka warke.

Habrit Hakhadasha/Haderekh

הבשורה על-פי מתי 14:1-36

1כאשר שמע הורדוס (שר הרובע של המדינה) על ישוע, 2אמר לאנשיו: ”אין ספק שהאיש הזה הוא יוחנן המטביל! יוחנן קם לתחייה, ולכן הוא מסוגל לחולל את כל הנסים האלה.“ 3הורדוס אמר דברים אלה משום שזמן מה קודם לכן אסר את יוחנן וכבל אותו בכלא, על־פי דרישת אשתו הורודיה שהייתה בעבר אשת אחיו פיליפוס, 4משום שיוחנן אמר להורדוס שאסור לו להתחתן אתה. 5הורדוס רצה להרוג את יוחנן, אולם פחד ממהומות ומרידות, כי העם חשב את יוחנן לנביא.

6אולם במסיבת יום הולדתו של הורדוס רקדה לפניו בת הורודיה ריקוד שמצא־חן בעיניו מאוד, 7והוא הבטיח בשבועה לתת לה כל מה שתרצה. 8לפי דרישת אמה ביקשה הנערה שיביאו לפניה על מגש את ראשו של יוחנן המטביל.

9המלך הצטער, אולם לא רצה להפר את שבועתו, ולא רצה לאבד את יוקרתו בעיני אורחיו. משום כך נתן הורדוס את ההוראות הדרושות, 10וראשו של יוחנן נכרת בבית הסוהר 11והובא על מגש לבתה של הורודיה, אשר נתנה אותו לאמה.

12תלמידי יוחנן באו וביקשו את גופתו, ולאחר שקברו אותו הלכו לישוע וסיפרו לו מה שקרה.

13כששמע ישוע מה שקרה, הפליג לבדו בסירה למקום מבודד, אולם ההמונים גילו אותו, ולכן עזבו את כפריהם והלכו אחריו לאורך חוף הים. 14ישוע ירד מהסירה, וכשראה את האנשים הרבים שחיכו לו, ריחם עליהם וריפא את החולים שביניהם.

15לפנות ערב ניגשו אליו תלמידיו ואמרו: ”אמור לכל האנשים האלה שילכו לקנות אוכל בכפרים שבאזור, כי השעה מאוחרת ובמקום השומם הזה אין מה לאכול.“

16אולם ישוע השיב להם: ”אין צורך. אתם תאכילו אותם.“

17”מה?“ קראו התלמידים בתמיהה. ”יש לנו רק חמש ככרות לחם ושני דגים.“

18”הביאו אותם לכאן“, הורה ישוע. 19הוא ציווה על האנשים לשבת על הדשא, לאחר מכן לקח את חמש ככרות הלחם ואת שני הדגים, הביט לשמים, ביקש מאלוהים שיברך את האוכל, פרס את הלחם ונתן לתלמידיו שיחלקו לעם. 20כולם אכלו עד ששבעו, וכשאספו לבסוף את הפירורים שנשארו, מילאו שנים־עשר סלים. 21באותו ערב היו שם כחמשת־אלפים גברים מלבד הנשים והילדים!

22לאחר מכן אמר ישוע לתלמידיו להיכנס לסירה ולחצות את הים, בעוד שהוא עצמו נשאר להיפרד מהקהל ולפזר אותם הביתה. 23‏-24לאחר ששלח ישוע את האנשים עלה על גבעה להתפלל. עם רדת הלילה, כשהתלמידים היו בסירה וישוע היה לבדו על החוף, פרצה סערה עזה והתלמידים נאבקו נגד הרוח החזקה והגלים הגבוהים.

25בערך בשעה ארבע לפנות בוקר בא ישוע לקראתם, כשהוא פוסע על־פני המים. 26התלמידים המבוהלים צעקו מפחד, כי חשבו שהוא רוח רפאים.

27ישוע דיבר אליהם מיד והרגיע אותם: ”אל תפחדו, זה אני!“

28”אדון, אם זה באמת אתה,“ קרא אליו שמעון פטרוס, ”צווה עלי ללכת לקראתך על־פני המים!“

29”בסדר“, ענה ישוע. ”בוא!“ ופטרוס ירד מן הסירה והחל ללכת על־פני המים לקראת ישוע. 30אולם כשהביט פטרוס בגלים הגבוהים שסבבוהו נבהל והחל לטבוע. ”הצל אותי, אדון!“ צעק פטרוס.

31מיד הושיט ישוע את ידו וחילץ את פטרוס. ”חסר־אמונה אתה!“ הוכיח אותו ישוע. ”מדוע פקפקת?“ 32כשעלו ישוע ופטרוס לסירה פסקה הרוח.

33התלמידים האחרים ישבו שם המומים ונדהמים. ”אתה באמת בן האלוהים!“ קראו.

34הם המשיכו בדרכם ועגנו בחוף גניסרת. 35אנשי המקום הכירו אותו מיד, והפיצו את דבר בואו בכל האזור. תוך זמן קצר הובאו אליו חולים רבים כדי שירפא אותם. 36החולים ביקשו מישוע שירשה להם רק לגעת בכנף בגדו, וכל מי שנגע בו נרפא.