Luka 12 – HCB & GKY

Hausa Contemporary Bible

Luka 12:1-59

Faɗakarwa da ƙarfafawa

1Ana nan sa’ad da taron dubban mutane suka taru har suna tattaka juna, Yesu fara yin magana, da farko da almajiransa ya ce, “Ku yi hankali da yistin Farisiyawa, wato, munafunci. 2Ba abin da yake rufe da ba za a fallasa ba, ko kuma abin da yake ɓoye da ba za a bayyana ba. 3Abin da kuka faɗa a cikin duhu, za a ji shi a hasken rana. Kuma abin da kuka faɗa a kunne, a cikin ɗakunan ciki-ciki, za a yi shelarsa daga kan rufin ɗakuna.

(Mattiyu 10.28-31)

4“Ina dai gaya muku abokaina, kada ku ji tsoron masu kashe jiki, amma bayan haka, ba sauran abin da za su iya yi. 5Amma zan nuna muku wanda za ku ji tsoronsa. Ku ji tsoron wanda, bayan da ya kashe jikin, yana da iko ya jefa ku cikin jahannama ta wuta. I, ina gaya muku, ku ji tsoronsa. 6Ba ana sayar da kanari biyar a kan kobo biyu ba? Duk da haka, Allah bai manta da ko ɗayansu ba. 7Tabbatacce, gashin kanku ɗin nan ma, an ƙidaya su duka. Kada ku ji tsoro. Darajarku ta fi na kanari masu yawa girma.

(Mattiyu 10.32,33; 12.32; 10.19,20)

8“Ina gaya muku, duk wanda ya shaida ni a gaban mutane, Ɗan Mutum ma zai shaida shi a gaban mala’ikun Allah. 9Amma wanda ya yi mūsun sanina a gaban mutane, shi ma za a yi mūsunsa a gaban mala’ikun Allah. 10Kuma duk wanda ya faɗi kalmar zagi a kan Ɗan Mutum, za a gafarta masa, amma duk wanda ya saɓa wa Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba.

11“Sa’ad da an kai ku a gaban majami’u, da gaban masu mulki, da kuma gaban masu iko, kada ku damu da yadda za ku kāre kanku, ko kuma abin da za ku faɗa, 12gama Ruhu Mai Tsarki zai koya muku abin da ya dace ku faɗa a lokacin.”

Misalin wawa mai arziki

13Sai wani mutum daga cikin taron ya ce masa, “Malam, ka ce wa ɗan’uwana ya raba gādon da ni.”

14Yesu ya amsa masa ya ce, “Kai, wa ya naɗa ni alƙali, ko mai sulhu a tsakaninku?” 15Sai ya ce musu, “Ku lura fa! Ku tsare kanku daga dukan kowane irin kwaɗayi. Ran mutum ba ya danganta a kan yawan dukiyarsa ba.”

16Sai ya gaya musu wannan misali ya ce, “Gonar wani mai arziki ta ba da amfani sosai. 17Ya yi tunani a ransa ya ce, ‘Ba ni da inda zan ajiye amfanin gonana. Me zan yi ke nan?’

18“Sai ya ce, ‘Ga abin da zan yi. Zan rushe rumbunana, in gina manya, in zuba dukan hatsina da kayana a ciki. 19Ni kuma zan ce wa raina, “Kana da kaya da yawa masu kyau, da aka yi ajiyarsu domin shekaru da dama masu zuwa. Yi hutunka, ka ci, ka sha, ka yi annashuwa.” ’

20“Amma Allah ya ce masa, ‘Kai wawa! A wannan dare za a nemi ranka. Bayan haka, wa zai gāji abin da ka tara wa kanka?’

21“Haka zai zama ga duk wanda ya tara wa kansa dukiya, amma ba shi da arziki a gaban Allah.”

Kada ku damu

(Mattiyu 6.25-34)

22Sai Yesu ya ce wa almajiransa, “Saboda haka, ina faɗa muku, kada ku damu game da rayuwarku, abin da za ku ci, ko kuma game da jikinku, abin da za ku yafa. 23Rai ya fi abinci, jiki kuma ya fi tufafi. 24Ku dubi hankaki. Ba sa shuki ko girbi, kuma ba su da ɗakin ajiya ko rumbu ba, duk da haka, duk da haka, Allah na ciyar da su. Darajarku ta fi na tsuntsaye sau da yawa! 25Wane ne a cikinku ta wurin damuwarsa, zai iya ƙara ko sa’a ɗaya ga rayuwarsa? 26Tun da ba za ku iya yin wannan ƙanƙanin abu ba, me ya sa kuke damuwa a kan sauran?

27“Ku dubi yadda furanni suke girma. Ba sukan yi aiki, ko saƙa ba, duk da haka, ina faɗa muku cewa, ko Solomon cikin kyakkyawan darajarsa duka, bai yafa kayan ado da ya kai kamar na ko ɗaya a cikinsu ba. 28In haka ne Allah yake yi wa ciyayin jeji sutura, wadda yau suna nan, sa’an nan gobe kuma a jefa cikin wuta, Allah ba zai yi muku sutura fiye da ciyayin jeji ba, ya ku masu ƙarancin bangaskiya! 29Kada ku sa zuciyarku a kan abin da za ku ci, ko abin da za ku sha, kada ku damu a kan su. 30Gama duniya da ba tă san Allah ba, tana faman neman dukan waɗannan abubuwa, Ubanku na sama kuwa, ya san kuna bukatarsu. 31Amma ku nemi mulkinsa, za a kuwa ƙara muku waɗannan abubuwa.

32“Ya ƙaramin garke, kada ku ji tsoro, gama ya gamshi Ubanku ya ba ku mulkin. 33Ku sayar da dukiyarku, ku ba wa matalauta. Ku yi wa kanku jakar kuɗin da ba za su lalace ba. Ku yi wa kanku ajiyar dukiyar da ba za tă kare ba a sama, inda ɓarawo ba zai yi kusa ba, asu kuma ba za su iya su lalatar ba. 34Gama inda dukiyarku take, nan ne zuciyarku ma take.

Zama a faɗake

(Mattiyu 24.45-51)

35“Ku shirya ɗamara don hidima. Ku bar fitilunku suna ci, 36kamar maza da suke jiran maigidansu ya dawo daga bikin aure. Saboda duk lokacin da ya dawo ya ƙwanƙwasa ƙofa, a shirye suke su buɗe masa nan da nan. 37Zai zama da albarka in maigida ya dawo, ya tarar da bayinsa suna zaman tsaro. Gaskiya ni faɗa muku, zai sa kayan hidima da kansa, ya sa bayinsa su zauna kan tebur, sa’an nan ya yi musu hidimar abinci. 38Zai zama da albarka ga bayin da maigidansu ya iske su, suna zaman tsaro, a duk lokacin da ya dawo, ko da ya dawo a sa’a ta biyu, ko ta uku na tsakar dare ne. 39Amma ku fahimci wannan. Da maigida ya san sa’ar da ɓarawo zai zo, ai, da ba zai bari a shiga, a fasa masa gida ba. 40Ku ma, sai ku zauna da shiri, domin Ɗan Mutum zai zo a sa’ar da ba ku yi tsammani ba.”

41Bitrus ya yi tambaya ya ce, “Ya Ubangiji, mu ne kake faɗa wa wannan misali, ko kuwa ga kowa da kowa ne?”

42Ubangiji ya amsa ya ce, “To, wane ne manaja mai aminci da hikima, wanda maigida ya ba shi riƙon bayinsa, domin ya ba su abincinsu a daidai lokaci? 43Zai zama da albarka ga bawan nan wanda maigidan ya dawo, ya same shi yana yin haka. 44Gaskiya nake gaya muku, maigidan zai ba shi riƙon dukan dukiyarsa. 45Amma da a ce bawan ya yi tunani a zuciyarsa ya ce, ‘Ai, maigidana ya yi jinkirin dawowa,’ sa’an nan ya fara dūkan bayin, maza da mata, ya kuma shiga ci, da sha, har da buguwa. 46Maigidan bawan nan zai dawo a ranar da wannan bawan bai yi tsammaninsa ba, kuma a sa’ar da bai sani ba. Maigidan zai yayyanka shi, ya kuma ba shi rabonsa tare da marasa bangaskiya.

47“Bawan da ya san nufin maigidansa, kuma bai yi shiri ba, ko kuma bai yi abin da maigidansa yake so ba, zai sha mummunan duka. 48Amma wanda bai sani ba, ya kuwa yi abin da ya isa horo, za a dūke shi kaɗan. Duk wanda aka ba shi mai yawa, mai yawan ne za a bida daga gare shi. Duk wanda kuma aka ba shi riƙon amana mai yawa, fiye da haka kuma za a bida daga gare shi.

Ba salama ba sai dai rabuwa

(Mattiyu 24.45-51)

49“Na zo ne domin in kawo wuta a duniya. Ina so da ta riga ta ƙunu! 50Amma ina da baftismar da za a yi mini, na kuwa damu sosai, sai na kammala ta! 51Kuna tsammani na zo domin in kawo salama a duniya ne? A’a! Ina gaya muku, rabuwa ne. 52Daga yanzu, za a iske mutum biyar a gida ɗaya sun rabu, suna gāba da juna, uku suna gāba da biyu, biyun suna gāba da ukun. 53Za su rarrabu. Mahaifi yana gāba da ɗan, ɗan kuma yana gāba da mahaifin. Mahaifiya tana gāba da diyar, diyar kuma tana gāba da mahaifiyar. Suruka tana gāba da matar ɗa, matar ɗa kuma tana gāba da suruka.”

Fahimtar lokuta

(Mattiyu 16.2,3; 5.25,26)

54Ya ce wa taron, “Sa’ad da kuka ga hadari ya fito daga yamma, nan da nan kukan ce, ‘Za a yi ruwan sama,’ sai a kuwa yi. 55Sa’ad da kuma iska ta taso daga kudu, kukan ce, ‘Za a yi zafi,’ sai kuwa a yi. 56Munafukai! Kuna san yadda za ku fassara yanayin ƙasa da na sararin sama. Ta yaya ba ku san yadda za ku yi fassarar wannan zamani ba?

57“Don me ba ku iya auna wa kanku, abin da yake daidai ba? 58Yayinda kake kan hanyar zuwa kotu da maƙiyinka, ka yi matuƙar ƙoƙari ku shirya tun kuna kan hanya. In ba haka ba, zai kai ka gaban alƙali, alƙali kuma ya miƙa ka ga ɗan sanda, ɗan sanda kuma ya jefa ka a kurkuku. 59Ina gaya maka, ba za ka fita ba, sai ka biya kobo na ƙarshe.”

Holy Bible in Gĩkũyũ

Luka 12:1-59

Gũkaanio na Kũũmĩrĩrio

112:1 Math 16:6, 11, 12O hĩndĩ ĩyo, rĩrĩa kĩrĩndĩ kĩa andũ ngiri nyingĩ kĩonganĩte hamwe, nginya makarangana-rĩ, Jesũ akĩamba kwarĩria arutwo ake, akĩmeera atĩrĩ, “Mwĩmenyererei ndawa ya kũimbia mĩgate ya Afarisai, na nĩyo ũhinga. 212:2 Mar 4:22Gũtirĩ ũndũ mũhithanie ũtakaguũrio, o na kana ũndũ mũhithe ũtakamenyeka. 3Maũndũ marĩa mwarĩirie nduma-inĩ, makaiguuo mũthenya barigici, na ũrĩa wothe mwanahehanĩrĩra matũ-inĩ mũrĩ tũnyũmba twa thĩinĩ, nĩũkanĩrĩrwo kuuma nyũmba igũrũ.

412:4 Joh 15:14-15“Ngũmwĩra atĩrĩ arata akwa, tigagai gwĩtigĩra arĩa mooragaga mwĩrĩ na thuutha ũcio gũtirĩ ũndũ mangĩhota gwĩka. 512:5 Ahib 10:31No nĩ ngũmuonia ũrĩa inyuĩ mwagĩrĩirwo nĩ gwĩtigĩra: Mwĩtigagĩrei ũrĩa ũngĩũraga mwĩrĩ na thuutha wa ũguo arĩ na ũhoti wa gũikia mũndũ Jehanamu. Ngũmwĩra atĩrĩ na ma, mwĩtigagĩrei ũcio. 6Githĩ tũnyoni tũtano tũtiendagio tũthendi twĩrĩ? No rĩrĩ, gũtirĩ o na kamwe gatuo Ngai ariganagĩrwo nĩko. 712:7 Math 10:30; Math 12:12No ti-itherũ, o na njuĩrĩ cianyu cia mũtwe nĩ ndare. Tigagai gwĩtigĩra, inyuĩ mũrĩ a bata gũkĩra tũnyoni tũingĩ.

8“Ngũmwĩra atĩrĩ, ũrĩa wothe ũkanyumbũra mbere ya andũ, o nake Mũrũ wa Mũndũ nĩakamumbũra mbere ya araika a Ngai. 9No ũrĩa ũkangaana mbere ya andũ ũcio nĩagakaanwo mbere ya araika a Ngai. 1012:10 Math 12:31, 32; 1Joh 5:16Nake mũndũ o wothe ũrĩa ũgaacambia Mũrũ wa Mũndũ nĩakarekerwo, no ũrĩa wothe ũkaruma Roho Mũtheru ndakarekerwo.

11“Rĩrĩa mũgaatwarwo mbere ya thunagogi, na mbere ya aathani na anene mũciirithio-rĩ, mũtikanetange na ũrĩa mũgacookia kana ũrĩa mũkoiga, 1212:12 Math 10:20nĩgũkorwo hĩndĩ ĩyo Roho Mũtheru nĩakamũruta ũrĩa mwagĩrĩirwo nĩ kuuga.”

Ngerekano ya Gĩtonga Kĩrimũ

13Mũndũ ũmwe warĩ gatagatĩ-inĩ ka andũ acio akĩmwĩra atĩrĩ, “Mũrutani, ĩra mũrũ wa maitũ tũgayane nake igai riitũ.”

14Nake Jesũ akĩmũcookeria atĩrĩ, “Mũndũ ũyũ, nũũ ũnduĩte wa kũmũtuithania ciira kana wa kũmũgayania indo cianyu?” 1512:15 Ayub 20:20; 31:24; Thab 62:10Agĩcooka akĩmeera atĩrĩ, “Mwĩmenyererei! Mũtigakorokere maũndũ; nĩgũkorwo muoyo wa mũndũ ndũthimagwo na mũigana wa indo iria arĩ nacio.”

16Agĩcooka akĩmahe ũhoro na ngerekano, akĩmeera atĩrĩ, “Mũgũnda wa mũndũ ũmwe gĩtonga nĩwaciarire mũno. 17Nake akĩĩyũria na ngoro yake atĩrĩ, ‘Ngwĩka atĩa? Ndirĩ na handũ ha kũiga magetha makwa.’

18“Agĩcooka akiuga atĩrĩ, ‘Nĩndamenya ũrĩa ngwĩka. Ngũtharia makũmbĩ makwa, njake mangĩ manene kũrĩ mo, njige magetha makwa mothe na indo ciakwa ciothe kuo. 19Njooke njĩĩre ngoro yakwa atĩrĩ, “Ũrĩ na indo nyingĩ njega wĩigĩire cia gũkũigana mĩaka mĩingĩ. Wĩhuurũkĩre, ũrĩe na ũnyue, na ũcanjamũke.” ’

2012:20 Jer 17:11; Ayub 27:8; Thab 39:6“No Ngai akĩmwĩra atĩrĩ, ‘Wee kĩrimũ gĩkĩ! Ũtukũ ũyũ wa ũmũthĩ nĩũgwĩtio muoyo waku. Indo icio wĩigĩire-rĩ, igaatuĩka cia ũ?’

21“Ũguo nĩguo gũgaatuĩka harĩ mũndũ o wothe ũrĩa wĩigagĩra mĩthithũ, no akaaga gwĩtongia na ũhoro wa Ngai.”

Mũtigatangĩke

22Jesũ agĩcooka akĩĩra arutwo ake atĩrĩ, “Nĩ ũndũ ũcio ngũmwĩra atĩrĩ, mũtigetangage nĩ ũndũ wa mĩoyo yanyu nĩ ũndũ wa kĩrĩa mũrĩrĩĩaga, kana kĩrĩa mũrĩhumbaga mĩĩrĩ yanyu. 23Muoyo-rĩ, ũrĩ bata gũkĩra irio, naguo mwĩrĩ ũrĩ bata gũkĩra nguo. 2412:24 Ayub 38:41Ta mwĩciiriei ũhoro wa mahuru: Matihaandaga kana makagetha, o na matirĩ kũndũ gwa kũiga irio kana makũmbĩ, no Ngai nĩamaheaga irio. Inyuĩ githĩ mũtirĩ a bata mũno gũkĩra nyoni! 25Nũũ wanyu ũngĩhota kuongerera muoyo wake ithaa o na rĩmwe nĩ ũndũ wa gwĩtanga? 26Rĩu-rĩ, angĩkorwo mũtingĩhota gwĩka ũndũ mũnini ũguo-rĩ, mũgĩtangĩkaga na maũndũ macio mangĩ nĩkĩ?”

2712:27 1Ath 10:4-7Ta mwĩcũraniei ũrĩa itoka ikũraga. Itirutaga wĩra kana ikogotha ndigi. No ngũmwĩra atĩrĩ, o na Solomoni arĩ na riiri wake wothe, ndaagemete ta kĩmwe gĩacio. 2812:28 Math 6:30Angĩkorwo ũguo nĩguo Ngai ahumbaga nyeki ya gĩthaka, ĩrĩa ĩrĩ ho ũmũthĩ na rũciũ igaikio mwaki-inĩ-rĩ, githĩ inyuĩ ndarĩkĩmũhumbaga makĩria, inyuĩ mwĩtĩkĩtie o hanini! 29Tigagai gũthĩĩnĩka ngoro-inĩ cianyu nĩ ũndũ wa kĩrĩa mũrĩrĩĩaga kana mũrĩnyuuaga; mũtigatangĩkage nĩ ũndũ wa ũguo. 3012:30 Math 6:8Nĩgũkorwo maũndũ maya mothe nĩmo andũ a gũkũ thĩ arĩa matetĩkĩtie Ngai macaranagia namo, no Ithe wanyu nĩoĩ atĩ nĩmũbatarĩtio nĩmo. 31No rĩrĩ, caragiai ũthamaki wake, na maũndũ maya mangĩ mothe nĩmũrĩheagwo o namo.

3212:32 Math 14:27“Tigagai gwĩtigĩra, inyuĩ rũũru rũrũ rũnini, nĩgũkorwo Ithe wanyu nĩonete arĩ wega kũmũhe ũthamaki ũcio. 3312:33 Math 6:20; Atũm 2:45; Jak 5:2Endiai indo iria mũrĩ nacio mũcooke mũteithie athĩĩni. Mwĩthondekerei ibeeti cia mbeeca iria itangĩtarũka, na mwĩgĩĩre na kĩgĩĩna igũrũ kĩrĩa gĩtangĩthira, kũrĩa gũtarĩ mũici ũngĩkuhĩrĩria na gũtirĩ memenyi cia gũkĩananga 3412:34 Math 6:21Nĩgũkorwo o kũrĩa mĩthiithũ wanyu ĩrĩ, nokuo ngoro cianyu o nacio irĩkoragwo irĩ.

Gũikara Mwĩiguĩte

35“Ikaragai mwĩhotorete, mwĩhaarĩirie gũtungata, na mũige matawa manyu magĩakanaga, 36o ta andũ metereire mwathi wao acooke kuuma iruga-inĩ rĩa kĩhikanio, nĩguo rĩrĩa agaacooka, aaringaringa mũrango mamũhingũrĩre o narua. 3712:37 Math 24:42, 46; 25:13Nĩũgakorwo ũrĩ ũndũ mwega harĩ ndungata iria mwathi wacio agaakora ciĩiguĩte rĩrĩa agacooka. Ngũmwĩra atĩrĩ na ma, nĩakehotora acitungatĩre, aciikarie metha-inĩ, na acooke acirehere irio irĩe. 38Nĩũgakorwo ũrĩ ũndũ mwega harĩ ndungata iria mwathi wacio agaakora ciĩhaarĩirie, o na angĩgooka ũtukũ gatagatĩ kana thaa kenda gũgĩkĩa. 3912:39 Math 6:19; 1Athe 5:2; Kũg 3:3No rĩrĩ, menyai ũũ: Korwo mwene nyũmba nĩamenyete ithaa rĩrĩa mũici egũũka-rĩ, ndangĩarekire nyũmba yake ĩtuuo. 40O na inyuĩ no nginya mũikarage mwĩhaarĩirie, tondũ Mũrũ wa Mũndũ agooka ithaa rĩrĩa mũtamwĩrĩgĩrĩire.”

41Petero akĩmũũria atĩrĩ, “Mwathani, nĩ ithuĩ ũrahe ũhoro na ngerekano ĩno kana ũreera mũndũ o wothe?”

4212:42 Luk 7:13Nake Mwathani agĩcookia akĩmũũria atĩrĩ, “Ndungata ya kwĩhokwo na njũgĩ, o ĩrĩa mwathi wayo angĩĩhokera kũroraga ndungata ciake, na ĩciheage irio hĩndĩ ĩrĩa yagĩrĩire, nĩĩrĩkũ? 43Nĩũgakorwo ũrĩ ũndũ mwega harĩ ndungata ĩyo, ĩrĩa mwathi wayo agooka akore ĩgĩĩka ũguo. 44Ngũmwĩra atĩrĩ na ma, nĩakamĩĩhokera indo ciake ciothe. 45No rĩrĩ, ĩ ndungata ĩyo ĩngĩĩra na ngoro yayo atĩrĩ, ‘Mwathi wakwa ndaracooka narua,’ nayo yambĩrĩrie kũhũũra ndungata cia arũme na cia andũ-a-nja, na kũrĩa na kũnyua na kũrĩĩo-rĩ, 46Mwathi wa ndungata ĩyo agooka mũthenya ũrĩa ĩtamwĩrĩgĩrĩire o na ithaa rĩrĩa ĩtooĩ, nake nĩakamĩherithia mũno, na amĩtuĩre ciira ta wa andũ arĩa matarĩ ehokeku.

4712:47 Gũcook 25:2“Ndungata ĩrĩa ĩmenyaga ũrĩa mwathi wayo endaga na ndĩĩhaaragĩria kana ĩgeeka ũrĩa Mwathi wayo endaga, ĩkaahũũrwo mahũũra maingĩ. 4812:48 Alaw 5:17; Ndar 15:27-30No ĩrĩa ĩtooĩ na nĩĩkaga maũndũ marĩa magĩrĩire kũherithanĩrio, ĩkaahũũrwo mahũũra matarĩ maingĩ. Ũrĩa wothe ũheetwo indo nyingĩ, ageetio indo nyingĩ; nake ũrĩa wĩhokeirwo nyingĩ makĩria nĩageetio nyingĩ makĩria.

Gũtirĩ Thayũ o tiga Nyamũkano

49“Njũkĩte kũrehe mwaki gũkũ thĩ, naarĩ korwo mwaki ũcio nĩwambĩrĩirie gwakana! 5012:50 Mar 10:38No ndĩ na ũbatithio ndĩrĩbatithio naguo, no kaĩ nĩngũthĩĩnĩka mũno ũngĩgaakinya-ĩ! 51Mũgwĩciiria ndokire kũrehe thayũ gũkũ thĩ? Ngũmwĩra atĩrĩ, ũguo tiguo, ndookire kũrehe nyamũkano. 52Kuuma rĩu gũthiĩ na mbere, andũ atano a mũciĩ ũmwe marĩkoragwo magayũkanĩte, atatũ magookĩrĩra eerĩ, nao eerĩ magookĩrĩra atatũ. 5312:53 Mik 7:6; Math 10:21Nao marĩkoragwo magayũkanĩte ũũ, ithe agookĩrĩra mũriũ nake mũriũ agookĩrĩra ithe, nyina agookĩrĩra mwarĩ nake mwarĩ agookĩrĩra nyina, nyaciarawe agookĩrĩra mũtumia wa mũriũ nake mũtumia wa mũriũ agookĩrĩra nyaciarawe.”

Gũkũũrana Mahinda

5412:54 Math 16:2Jesũ akĩĩra kĩrĩndĩ kĩu atĩrĩ, “Hĩndĩ ĩrĩa muona itu rĩkĩambata riumĩte ithũĩro, o rĩmwe muugaga atĩrĩ, ‘Nĩgũkuura mbura,’ na gũkoira. 55Hĩndĩ ĩrĩa rũhuho rwahurutana ruumĩte gũthini muugaga atĩrĩ, ‘Nĩgũkũgĩa na ũrugarĩ,’ na gũkagĩa. 5612:56 Math 16:3Inyuĩ hinga ici! Nĩmũũĩ wega gũkũũrana ũrĩa igũrũ na thĩ gũtariĩ. Mũkĩremagwo nĩgũkũũrana ũhoro wa mahinda maya tũrĩ nĩkĩ?

57“Mwagaga gwĩtuĩra inyuĩ ene ũrĩa kwagĩrĩire nĩkĩ? 5812:58 Math 5:25Na rĩrĩ, rĩrĩa mũrathiĩ na thũ yaku kũrĩ mũciirithania-rĩ, geria mũno wĩiguithanie nayo mũrĩ o njĩra-inĩ, ndĩgagũkururie ĩgũtware kũrĩ mũciirithania, nake mũciirithania akũneane kũrĩ mũnene, nake mũnene ũcio agũikie njeera. 5912:59 Math 12:42Ngũkwĩra atĩrĩ, ndũkoima kuo ũtarĩhĩte thiirĩ wothe, hatarĩ gathendi ũgũtigia.”