Luka 11 – HCB & GKY

Hausa Contemporary Bible

Luka 11:1-54

Koyarwar Yesu a kan addu’a

(Mattiyu 6.9-13; 7.7-11)

1Wata rana Yesu yana addu’a a wani wuri. Da ya gama, sai ɗaya daga cikin almajiransa ya ce masa, “Ubangiji, ka koya mana yin addu’a, kamar yadda Yohanna ya koya wa almajiransa.”

2Sai ya ce musu, “Sa’ad da kuke yin addu’a ku ce,

“ ‘Ya Uba,

sunanka mai tsarki ne

mulkinka ya zo.

3Ka ba mu kowace rana abincin yini.

4Ka gafarta mana zunubanmu,

kamar yadda mu ma ke gafarta wa duk wanda ya yi mana laifi.

Kada ka bari a kai mu cikin jarraba.’ ”

5Sa’an nan ya ce musu, “Da a ce ɗayanku yana da aboki, sa’an nan ya je wurinsa da tsakar dare ya ce, ‘Aboki, ranta mini burodi guda uku, 6domin wani abokina da yake tafiya ya sauka a wurina. Ga shi, ba ni da abinci da zan ba shi.’ 7Sai wanda yake cikin ɗaki ya amsa ya ce, ‘Kada ka dame ni. An riga an kulle ƙofa, da ni da yarana kuwa mun kwanta, ba zan iya tashi in ba ka kome ba.’ 8Ina gaya muku, ko da yake ba zai so ya tashi ya ba shi burodin don shi abokinsa ne ba, duk da haka, zai tashi ya ba shi yawan abin da yake bukata, saboda nacewarsa.

9“Don haka ina faɗa muku, ku roƙa, za a ba ku, ku nema za ku samu, ku ƙwanƙwasa za a kuwa buɗe muku ƙofa. 10Gama duk wanda ya roƙa, yana karɓa, mai nema yana samu, wanda ya ƙwanƙwasa kuma, za a buɗe masa ƙofa.

11“Wane mahaifi ne a cikinku, in ɗansa ya roƙe shi kifi, zai ba shi maciji a maimakon, 12ko kuma in ya roƙi ƙwai, ya ba shi kunama? 13In fa haka ne, ko da yake ku mugaye ne, kun san ba ’ya’yanku kyautai masu kyau, balle fa Ubanku na sama, zai yi fiye da haka, ta wurin ba da Ruhu Mai Tsarki, ga masu roƙonsa!”

Yesu da Be’elzebub

(Mattiyu 12.22-30; Markus 3.20-27)

14Sa’ad da Yesu yake fitar da wani beben aljani daga wani mutum, da aljanin ya fita, sai mutumin wanda da bebe ne, ya yi magana, taron kuwa suka yi mamaki. 15Amma waɗansunsu suka ce, “Ai, da ikon Be’elzebub, sarkin aljanu ne, yake fitar da aljanu.” 16Waɗansu kuma suka gwada shi, ta wurin neman yă nuna musu wata alama daga sama.

17Yesu kuwa ya san tunaninsu, sai ya ce musu, “Duk mulkin da yake gāba da kansa, zai lalace, kuma gidan da yake gaba da kansa zai rushe. 18In Shaiɗan yana gāba da kansa, yaya mulkinsa zai tsaya? Ina faɗin haka domin kun ce, da ikon Be’elzebub nake fitar da aljanu. 19In da ikon Be’elzebub nake fitar da su, to, da ikon wa masu binku suke fitar da su? Saboda haka, za su zama alƙalanku ke nan. 20Amma in da ikon Allah ne ni nake fitar da aljanu, ashe, mulkin Allah ya zo muku ke nan.

21“Sa’ad da mutum mai ƙarfi, wanda yake da makamai yana gadin gidan kansa, an tsare lafiyar dukiyarsa ke nan. 22Amma in wani wanda ya fi shi ƙarfi, ya faɗa masa ya kuma sha ƙarfinsa, yakan ƙwace makaman da mutumin ke dogara da su, ya kuma rarraba ganima.

23“Wanda ba ya tare da ni, yana gāba da ni, wanda kuma ba ya tarawa da ni, watsarwa yake yi.

(Mattiyu 12.43-45)

24“Lokacin da mugun ruhu ya fita daga mutum, sai ya bi ta wuraren da ba mutane, yana neman hutu, amma ya kāsa samu, sai ya ce, ‘Zan koma gidan da na bari.’ 25Sa’ad da ya koma, ya tarar da gidan a share da tsabta, kuma a shirye. 26Sai ya je ya ɗebo waɗansu ruhohi bakwai da suka fi shi mugunta, sai su shiga su zauna a wurin. Ƙarshen wannan mutum kuwa zai fi farkonsa muni.”

27Da Yesu yake cikin faɗin waɗannan abubuwa, sai wata mace daga cikin taron ta ɗaga murya ta ce masa, “Mai albarka ce uwar da ta haife ka, wadda ka sha mamanta.”

28Yesu ya amsa ya ce, “A maimakon, masu albarka ne waɗanda suke jin maganar Allah, suna kuma biyayya da ita.”

Alamar Yunana

(Mattiyu 12.38-42; Markus 8.12)

29Da taron mutane suka ƙaru, sai Yesu ya ce, “Wannan mugun zamani ne. Tana neman wani abin banmamaki, amma ba ko ɗaya da za a ba ta, sai dai ta Yunana. 30Kamar yadda Yunana ya zama alama ga mutanen Ninebe, haka ma Ɗan Mutum zai zama ga zamanin nan. 31A ranar shari’a, Sarauniyar Kudu za tă tashi tsaye tare da wannan zamani, ta yanke wa wannan zamani hukunci, domin ta zo daga ƙarshen duniya ta saurari hikimar Solomon, ga shi kuwa, shi wanda ya fi Solomon girma, na nan. 32A ranar shari’a, mutanen Ninebe za su tashi tsaye tare da wannan zamani, su yanke wa wannan zamani hukunci. Gama sun tuba sa’ad da Yunana ya yi musu wa’azi. Ga shi yanzu, shi wanda ya fi Yunana girma, na nan.

Fitilar jiki

(Mattiyu 5.15; 6.22,23)

33“Babu wanda yakan ƙuna fitila sa’an nan ya ɓoye ta, ko ya rufe ta da murfi ba. A maimako, yakan ajiye ta a kan wurin ajiye fitila, don masu shiga su ga haske. 34Idonka shi ne fitilar jikinka. Sa’ad da idanunka suna da lafiya, dukan jikinka ma na cike da haske, amma sa’ad da idanunka suna da lahani, dukan jikinka ma na cike da duhu. 35Ka lura fa, kada hasken da yake cikinka ya zamana duhu ne. 36Saboda haka, in dukan jikinka yana cike da haske, ba inda ke da duhu, jikinka kuwa zai kasance da haske gaba ɗaya, kamar yadda hasken fitila yake haskaka ka.”

La’anu a kan Farisiyawa da kuma masanan doka

(Mattiyu 5.15; 6.22,23)

37Da Yesu ya gama magana, sai wani Bafarisiye ya gayyace shi cin abinci tare da shi. Sai kuwa ya shiga ya zauna a tebur. 38Amma Bafarisiyen ya lura cewa, Yesu bai wanke hannu kafin ya ci abinci ba, sai mamaki ya kama shi.

39Sai Ubangiji ya ce masa, “Ku Farisiyawa, kukan wanke bayan kwano da kwaf, amma a ciki kuna cike da kwaɗayi da mugunta. 40Ku wawayen mutane! Ashe, wanda ya yi bayan, ba shi ne kuma ya yi cikin ba? 41Ku ba matalauta abin da yake cikin kwano, kuma kome zai zama muku da tsabta.

42“Kaitonku, Farisiyawa, domin kuna ba wa Allah zakka na na’ana’arku, da ƙarƙashinku, da kuma sauran ganyen lambunku iri-iri, amma kun ƙyale adalci da ƙaunar Allah. Ya kamata da kun kiyaye na ƙarshen, ban ba barin na farkon.

43“Kaitonku, Farisiyawa, domin kun cika son wuraren zama masu daraja a majami’u, da kuma yawan gaisuwa a wuraren kasuwanci.

44“Kaitonku, domin ku kamar kaburbura ne da ba a sa musu alama ba, waɗanda mutane suke takawa don rashin sani.”

45Sai ɗaya daga cikin masanan dokoki ya ce wa Yesu, “Malam, in ka faɗi waɗannan abubuwa haka, kai kuma ka zage mu ke nan.”

46Yesu ya amsa ya ce, “Ku masanan dokoki ma, kaitonku, domin kun ɗora wa mutane kaya masu nauyi waɗanda da ƙyar suke ɗaukawa, amma ku da kanku ba za ku sa ko yatsa ɗaya, don ku taimake su ba.

47“Kaitonku, domin kun gina kaburbura saboda annabawa, nan kuwa kakannin-kakanninku ne suka kashe su. 48Wannan ya shaida cewa kun amince da abin da kakannin-kakanninku suka yi. Sun karkashe annabawa, ku kuma kun gina kaburburansu. 49Saboda haka, Allah a cikin hikimarsa ya ce, ‘Zan aika musu da annabawa da manzanni. Za su kashe waɗansu, su kuma tsananta wa waɗansu.’ 50Saboda haka, alhakin jinin dukan annabawa da aka kashe, tun farkon duniya, yana kan wannan zamani, 51wato, tun daga jinin Habila, har zuwa jinin Zakariya, wanda aka kashe tsakanin bagade da mazauni. I, ina gaya muku, alhakinsu duka yana kan wannan zamani.

52“Kaitonku, masanan dokoki, domin kun ɗauke mabuɗin ilimi. Ku kanku ba ku shiga ba, kuma kun hana wa waɗanda suke shiga, su shiga.”

53Da Yesu ya bar wurin, sai Farisiyawa da malaman dokoki suka fara gaba mai tsanani da shi, kuma suna tsokanansa da tambayoyi. 54Suna fakonsa, don su kama shi a kan wata magana da zai faɗa.

Holy Bible in Gĩkũyũ

Luka 11:1-54

Ũrutani wa Jesũ ũkoniĩ Mahooya

111:1 Luk 3:21Na rĩrĩ, mũthenya ũmwe Jesũ aarĩ handũ akĩhooya. Rĩrĩa aarĩkirie kũhooya, mũrutwo ũmwe wake akĩmwĩra atĩrĩ, “Mwathani, tũrute kũhooya o ta ũrĩa Johana aarutire arutwo ake.”

2Nake Jesũ akĩmeera atĩrĩ, “Rĩrĩa mũkũhooya, ugagai atĩrĩ:

“ ‘Ithe witũ (ũrĩ Igũrũ),

rĩĩtwa rĩaku nĩrĩamũrwo,

ũthamaki waku nĩũũke.

(Ũrĩa wendete nĩwĩkagwo gũkũ thĩ,

o ta ũrĩa gwĩkagwo kũu igũrũ.)

3Tũheage o mũthenya irio ciitũ cia gũtũigana.

411:4 Math 18:35; Math 11:25Na ũtũrekere mehia maitũ,

o ta ũrĩa o na ithuĩ tũrekagĩra arĩa othe matwĩhagĩria.

Na ndũgatũtware magerio-inĩ

(no kũhonokia ũtũhonokagie ũũru-inĩ).’ ”

5Agĩcooka akĩmeera atĩrĩ, “Mũndũ ũmwe wanyu angĩkorwo arĩ na mũrata nake athiĩ gwake ũtukũ gatagatĩ amwĩre atĩrĩ, ‘Mũrata wakwa, he mĩgate ĩtatũ, 6nĩgũkorwo ndĩ na mũrata wakwa wanjeerera, na ndirĩ na kĩndũ gĩa kũmũhe arĩe.’

7“Nake mũndũ ũcio ũrĩ nyũmba thĩinĩ amũcookerie atĩrĩ, ‘Tiga gũũthĩĩnia. Nĩndĩkĩtie kũhinga mũrango na tũrĩ toro hamwe na ciana ciakwa. Ndingĩhota gũũkĩra ngũhe mĩgate.’ 811:8 Luk 18:1-6Ngũmwĩra atĩrĩ, o na angĩkorwo ndangĩũkĩra amũhe mĩgate ĩyo nĩ ũndũ wa ũrata-rĩ, no nĩ ũndũ wa ũrĩa amũringĩrĩirie-rĩ, mũndũ ũcio nĩegũũkĩra amũhe kĩrĩa gĩothe abatairio nĩkĩo.”

911:9 Math 7:7“Nĩ ũndũ ũcio ngũmwĩra atĩrĩ: Hooyai na nĩmũkũheo; mathaai na nĩmũkuona; ringaringai mũrango na nĩmũkũhingũrĩrwo. 10Nĩgũkorwo ũrĩa wothe ũhooyaga nĩaheagwo; na ũrĩa ũmaathaga nĩonaga; na ũrĩa ũringaringaga mũrango nĩahingũragĩrwo.

11“Nĩ mũciari ũrĩkũ thĩinĩ wanyu ũngĩĩtio thamaki nĩ mwana wake, nake amũhe nyoka? 12Kana eetio itumbĩ amũhe kangʼaurũ? 13Angĩkorwo inyuĩ, o na mũrĩ ooru, nĩmũũĩ kũhe ciana cianyu iheo njega-rĩ, Ithe wanyu ũrĩa ũrĩ Igũrũ githĩ ndarĩkĩragĩrĩria kũhe Roho Mũtheru kũrĩ arĩa mamũhooyaga!”

Jesũ na Beelizebuli

1411:14 Math 9:32, 33Na rĩrĩ, Jesũ nĩaingataga ndaimono yume thĩinĩ wa mũndũ ũtaaragia. Rĩrĩa ndaimono ĩyo yoimire, mũndũ ũcio ũtaaragia akĩaria, nakĩo kĩrĩndĩ kĩa andũ gĩkĩgega. 15No amwe ao makiuga atĩrĩ, “Aingataga ndaimono na hinya wa Beelizebuli ũrĩa mũnene wa ndaimono.” 1611:16 Math 12:38Nao andũ angĩ makĩmũgeria, makĩmũũria amaringĩre kĩama kiumĩte igũrũ.

17Jesũ nĩamenyire ũrĩa meciiragia, nake akĩmeera atĩrĩ: “Ũthamaki o wothe ũngĩgayũkana ũũkanĩrĩre guo mwene no ũharagane, nayo nyũmba ĩngĩgayũkana yũkanĩrĩre yo nyene no ĩgwe. 1811:18 Math 4:10Angĩkorwo Shaitani nĩagayũkanĩte akeyũkĩrĩra we mwene-rĩ, ũthamaki wake ũngĩkĩĩhaanda atĩa? Ndoiga ũguo tondũ mũroiga atĩ niĩ nyingataga ndaimono na hinya wa Beelizebuli. 19Ningĩ angĩkorwo niĩ nyingataga ndaimono na hinya wa Beelizebuli-rĩ, arũmĩrĩri anyu maingataga ndaimono na hinya wa ũ? Nĩ ũndũ ũcio-rĩ, acio nĩo makaamũtuĩra ciira. 2011:20 Thaam 8:19; Math 3:2Na rĩrĩ, ingĩkorwo nyingataga ndaimono na hinya wa kĩara kĩa Ngai-rĩ, ũthamaki wa Ngai nĩũũkĩte kũrĩ inyuĩ.

21“Rĩrĩa mũndũ njamba oya indo ciake ciothe cia mbaara, arangĩre nyũmba yake mwene, indo ciake ciikaraga irĩ ngitĩre. 22No rĩrĩ, mũndũ ũngĩ ũrĩ na hinya kũmũkĩra angĩmũtharĩkĩra amũtoorie, nĩamũtunyaga indo ciake cia mbaara iria ehokete, na akagaĩra andũ indo iria akoragwo atahĩte.

2311:23 Math 12:30; Luk 9:50“Mũndũ ũrĩa ũtarĩ hamwe na niĩ, ũcio nĩ thũ yakwa, na ũrĩa ũtacookanagĩrĩria hamwe na niĩ, ũcio nĩ kũhurunja ahurunjaga.

24“Na rĩrĩ, hĩndĩ ĩrĩa ngoma thũku yoima thĩinĩ wa mũndũ, ĩtuĩkanagĩria werũ-inĩ ĩgĩcaria ũhurũko na ĩkawaga. Hĩndĩ ĩyo ĩkoiga atĩrĩ, ‘Nĩngũcooka nyũmba ĩrĩa ndoimire.’ 25Na yacooka ĩgakora nyũmba ĩyo ĩrĩ haate, ĩgathondekwo wega. 2611:26 2Pet 2:20Hĩndĩ ĩyo ngoma ĩyo thũku ĩkagĩĩra ngoma ingĩ mũgwanja thũku makĩria mayo, igatoonya, igaikara kuo. Naguo mũikarĩre wa mũndũ ũcio ũgathũka gũkĩra wa mbere.”

27Rĩrĩa Jesũ aaragia maũndũ maya-rĩ, mũndũ-wa-nja warĩ gatagatĩ-inĩ ga kĩrĩndĩ akĩanĩrĩra na mũgambo mũnene, akiuga atĩrĩ, “Kũrathimwo nĩ maitũguo ũrĩa wagũciarire na agĩkuongithia.”

2811:28 Ahib 4:12; Luk 8:21; Joh 14:21Nake Jesũ agĩcookia atĩrĩ, “Kũrathimwo nĩ arĩa maiguaga kiugo kĩa Ngai na magagĩathĩkĩra.”

Kĩmenyithia kĩa Jona

29Na rĩrĩa kĩrĩndĩ kĩa andũ kĩongererekire-rĩ, Jesũ akiuga atĩrĩ, “Rũrũ nĩ rũciaro rwaganu. Rũũragia rũringĩrwo kĩama, no gũtirĩ kĩama rũkaringĩrwo tiga o kĩrĩa kĩaringĩirwo Jona. 30Nĩgũkorwo o ta ũrĩa Jona aarĩ kĩmenyithia kũrĩ andũ a Nineve, ũguo noguo Mũrũ wa Mũndũ egũkorwo arĩ kĩmenyithia kũrĩ rũciaro rũrũ. 3111:31 1Ath 10:1Mũtumia-mũthamaki ũrĩa wa mwena wa Gũthini nĩakarũgama hĩndĩ ya ciira hamwe na andũ a rũciaro rũrũ arũtuĩre ciira, nĩgũkorwo oimire ituri cia thĩ oke athikĩrĩrie ũũgĩ wa Solomoni, na rĩu ũmwe mũnene gũkĩra Solomoni arĩ haha. 3211:32 Jon 3:5Andũ a Nineve nĩmakarũgama hĩndĩ ya ciira hamwe na rũciaro rũrũ marũtuĩre ciira; nĩgũkorwo nĩmeririre maahunjĩirio nĩ Jona, na rĩu ũmwe mũnene gũkĩra Jona arĩ haha.

Tawa wa Mwĩrĩ

33“Gũtirĩ mũndũ ũgwatagia tawa agacooka akaũiga handũ ũtangĩoneka kana akaũiga rungu rwa irebe, no aũigaga handũ igũrũ nĩguo arĩa megũtoonya nyũmba mathererwo nĩ ũtheri. 34Riitho rĩaku nĩrĩo tawa wa mwĩrĩ waku. Rĩrĩa maitho maku marĩ mega, mwĩrĩ waku wothe o naguo ũkoragwo ũiyũrĩte ũtheri. No rĩrĩa matarĩ mega-rĩ, mwĩrĩ waku o naguo ũkoragwo ũiyũrĩte nduma. 35Hakĩrĩ ũguo-rĩ, menyerera ũtheri ũrĩa ũrĩ thĩinĩ waku ndũgatuĩke nduma. 36Nĩ ũndũ ũcio-rĩ, mwĩrĩ waku wothe ũngĩiyũrwo nĩ ũtheri, na ndũrĩ handũ harĩ nduma, nĩũrĩtheragĩrwo nĩ ũtheri biũ, o ta ũrĩa ũtheri wa tawa ũkũmũrĩkagĩra.”

Haaro Ithathatũ

37Hĩndĩ ĩrĩa Jesũ aarĩkirie kwaria, Mũfarisai ũmwe akĩmũnyiita ũgeni gwake makarĩanĩre; nĩ ũndũ ũcio agĩthiĩ, agĩikara metha-inĩ. 3811:38 Mar 7:3, 4No Mũfarisai ũcio ona ũguo akĩgega nĩ ũndũ Jesũ ndaambire gwĩthamba moko atanarĩa irio.

3911:39 Math 23:25, 26Nake Mwathani akĩmwĩra atĩrĩ, “Inyuĩ Afarisai mũthambagia gĩkombe na thaani mwena wa na igũrũ, no thĩinĩ wanyu mũiyũrĩtwo nĩ ũkoroku na waganu. 40Inyuĩ irimũ ici! Githĩ ũrĩa wombire mwena wa na nja to we wombire mwena wa na thĩinĩ? 41No rĩrĩ, heagai athĩĩni kĩrĩa kĩrĩ thĩinĩ wa thaani, na hĩndĩ ĩyo indo ciothe nĩigũtuĩka theru harĩ inyuĩ.”

4211:42 Luk 18:12; Math 23:23“Kaĩ mũrĩ na haaro inyuĩ Afarisai-ĩ! Tondũ mũrutagĩra Ngai gĩcunjĩ gĩa ikũmi gĩa terere, na togotia na nyeni cia mĩthemba yothe no mũkaaga kũrũmbũiya kĩhooto na wendani wa Ngai. Mwaagĩrĩirwo nĩ gwĩkaga maũndũ macio mũtegũtiganĩria macio mangĩ ma mbere.

43“Kaĩ mũrĩ na haaro inyuĩ Afarisai-ĩ! Tondũ mwendaga gũikarĩra itĩ iria cia mbere thunagogi-inĩ na mũgeithagio mũrĩ ndũnyũ-inĩ.

4411:44 Math 23:27“Kaĩ mũrĩ na haaro-ĩ, tondũ mũtariĩ ta mbĩrĩra itarĩ rũũri iria andũ mageragĩra igũrũ rĩacio matekũmenya.”11:44 Ayahudi nĩmahakaga mbĩrĩra ciao coka nĩgeetha gũtikagĩe na mũndũ ũngĩcihutia tondũ ũguo nĩkũngĩatũmire mũndũ anyiitwo nĩ thaahu.

45Mũrutani ũmwe wa Watho akĩmũcookeria, akĩmwĩra atĩrĩ, “Mũrutani, rĩrĩa ũkwaria maũndũ macio-rĩ, nĩũratũruma o na ithuĩ.”

4611:46 Math 23:4Nake Jesũ akĩmũcookeria atĩrĩ, “O na inyuĩ arutani a Watho kaĩ mũrĩ na haaro-ĩ! Tondũ mũkuuithagia andũ mĩrigo mĩritũ ĩrĩa matangĩhota gũkuua, na inyuĩ ene mũtingĩmĩhutia o na kaara kamwe mũmateithie.

47“Kaĩ mũrĩ na haaro-ĩ! Tondũ mwakagĩra anabii mbĩrĩra, o arĩa mooragirwo nĩ maithe manyu ma tene. 48Nĩ ũndũ ũcio mũgakĩruta ũira atĩ nĩmwĩtĩkanĩtie na ũrĩa maithe manyu meekire; atĩ nĩo mooragire anabii, na inyuĩ mũkamaakĩra mbĩrĩra. 4911:49 1Akor 1:24, 30; Math 23:34Tondũ wa ũguo ũũgĩ wa Ngai uugĩte atĩrĩ, ‘Nĩngamatũmĩra anabii na atũmwo, moorage amwe ao na manyariire arĩa angĩ.’ 50Nĩ ũndũ ũcio rũciaro rũrũ nĩrũgaciirithĩrio thakame ya anabii othe ĩrĩa yanaitwo kuuma o kĩambĩrĩria gĩa thĩ, 5111:51 Kĩam 4:8; 2Maũ 24:20, 21kuuma thakame ya Habili nginya thakame ya Zekaria ũrĩa woragĩirwo gatagatĩ-inĩ ga kĩgongona na handũ harĩa hatheru. Ĩĩ nĩguo, ngũmwĩra atĩrĩ, rũciaro rũrũ nĩrũkaherithĩrio thakame ĩyo.

5211:52 Math 23:13“Kaĩ mũrĩ na haaro inyuĩ arutani a watho-ĩ! Tondũ nĩmweheretie kĩhingũro kĩa ũmenyo. Inyuĩ ene mũtiigana gũtoonya, na arĩa marenda gũtoonya mũkamagiria.”

53Jesũ aarĩkia kuuma kũu, Afarisai na arutani a watho makĩambĩrĩria kũmũkararia marĩ na ũũru mũno na kũmũũgita na kũmũũria ciũria nĩguo aarie maũndũ maingĩ, 54makĩgeria kũmũtega maigue kana nĩ harĩ ũndũ mũũrũ angĩaria.