Afisawa 2 – HCB & NIRV

Hausa Contemporary Bible

Afisawa 2:1-22

An raya ku a cikin Kiristi

1Ku kam, a dā ku matattu ne saboda laifofinku da kuma zunubanku. 2Kun yi rayuwa kamar yadda sauran mutanen duniya suke yi, cike da zunubi, kuna biyayya ga sarki masu ikon sarari sama, wato, ruhun nan da yanzu yake aiki a cikin masu ƙin biyayya ga Allah. 3Dukanmu a dā mun yi irin rayuwan nan a cikinsu, muna bin kwaɗayi da sha’awace-sha’awacen jikunanmu da tunaninmu. Kamar sauran mutane, mun cancanci fushin Allah. 4Amma saboda yawan ƙaunar da yake mana, Allah, wanda yake mai yawan jinƙai, 5ya ba mu rai sa’ad da ya tashe Kiristi daga matattu. Ta wurin alherin Allah ne aka cece ku. 6Allah ya tashe mu tare da Kiristi, ya kuma ba mu wurin zama tare da shi a cikin mulkin samaniya. 7Allah ya yi haka domin a tsararraki masu zuwa yă nuna yalwar alherinsa da ya wuce misali, an bayyana alheransa da ya yi mana ta wurin Kiristi Yesu. 8Allah ya cece ku ta wurin alheri sa’ad da kuka ba da gaskiya. Wannan kuwa ba yinku ba ne, kyauta ce daga Allah. 9Ba kuwa saboda aikin lada ba, don kada wani yă ɗaga kai. 10Ai, mu aikinsa ne, an sāke halittarmu a cikin Kiristi Yesu musamman domin mu yi kyawawan ayyuka, waɗanda Allah ya tanadar mana tun da fari, mu yi.

An sulhunta Yahudawa da al’ummai su zama ɗaya ta wurin Kiristi

11Saboda haka, ku tuna dā ku Al’ummai ne bisa ga haihuwa, waɗanda kuma ake kira masu “kaciya” sukan kira ku “marasa kaciya” (ga shi kuwa, kaciyar nan ta jiki ce, wadda ake yi da hannu). 12Ku kuma tuna a lokacin ba ku san Kiristi ba. A ware kuke daga mutanen Isra’ila, ba ku kuma da dangantaka da alkawaran da Allah ya yi da su. Kun yi zama a duniyan nan babu bege kuma babu Allah. 13Amma yanzu a cikin Kiristi Yesu, ku da dā kuke can da nesa an kawo ku kusa ta wurin jinin Kiristi.

14Gama shi kansa shi ne salamarmu, shi ne ya kawo ƙungiyoyi biyu suka zama ɗaya, ya kuma rushe katangan nan ta ƙiyayya wadda ta raba mu. 15Kiristi ya ba da jikinsa don yă kawar da doka da dukan umarnanta da kuma ƙa’idodinta. Ya yi haka domin yă halicci sabuwar zuriya daga zuriyoyin nan biyu. Ta haka kuma ya kawo salama tsakaninsu. 16A kan gicciye, Kiristi ya kawar da ƙiyayyar da take tsakaninmu da juna. Ya kuma kawo sulhu tsakaninmu da Allah. 17Ya zo ya yi muku wa’azin salama; ku da kuke nesa da shi, ya kuma yi wa waɗanda suke kusa. 18Gama ta wurinsa dukanmu za mu iya zuwa gun Uba ta wurin Ruhu guda.

19Don haka, yanzu ku ba baƙi ba ne, ku kuma ba bare ba ne. Ku ’yan ƙasa ne tare da mutanen Allah, iyalin gidan Allah kuma. 20Ku gini ne wanda manzanni da annabawa suke tushensa, Kiristi kuma shi ne dutse mafi muhimmanci na ginin. 21Ta wurinsa ne dukan ginin yake a haɗe, shi ne kuma yake sa ginin yă yi girma, yă zama haikali mai tsarki domin Ubangiji. 22Ku ma sashe ne na wannan ginin da Kiristi ya yi inda Allah yake zaune ta wurin Ruhunsa.

New International Reader’s Version

Ephesians 2:1-22

God Has Given Us New Life Through Christ

1You were living in your sins and lawless ways. But in fact you were dead. 2You used to live as sinners when you followed the ways of this world. You served the one who rules over the spiritual forces of evil. He is the spirit who is now at work in those who don’t obey God. 3At one time we all lived among them. Our desires were controlled by sin. We tried to satisfy what they wanted us to do. We followed our desires and thoughts. God was angry with us like he was with everyone else. That’s because of the kind of people we all were. 4But God loves us deeply. He is full of mercy. 5So he gave us new life because of what Christ has done. He gave us life even when we were dead in sin. God’s grace has saved you. 6God raised us up with Christ. He has seated us with him in his heavenly kingdom. That’s because we belong to Christ Jesus. 7He has done it to show the riches of his grace for all time to come. His grace can’t be compared with anything else. He has shown it by being kind to us. He was kind to us because of what Christ Jesus has done. 8God’s grace has saved you because of your faith in Christ. Your salvation doesn’t come from anything you do. It is God’s gift. 9It is not based on anything you have done. No one can brag about earning it. 10We are God’s creation. He created us to belong to Christ Jesus. Now we can do good works. Long ago God prepared these works for us to do.

God’s New Family of Jews and Gentiles

11You who are not Jews by birth, here is what I want you to remember. You are called “uncircumcised” by those who call themselves “circumcised.” But they have only been circumcised in their bodies by human hands. 12Before you believed in Christ, you were separated from him. You were not considered to be citizens of Israel. You were not included in what the covenants promised. You were without hope and without God in the world. 13At one time you were far away from God. But now you belong to Christ Jesus. He spilled his blood for you. This has brought you near to God.

14Christ himself is our peace. He has made Jews and Gentiles into one group of people. He has destroyed the hatred that was like a wall between us. 15Through his body on the cross, Christ set aside the law with all its commands and rules. He planned to create one new people out of Jews and Gentiles. He wanted to make peace between them. 16He planned to bring both Jews and Gentiles back to God as one body. He planned to do this through the cross. On that cross, Christ put to death their hatred toward one another. 17He came and preached peace to you who were far away. He also preached peace to those who were near. 18Through Christ we both come to the Father by the power of one Holy Spirit.

19So you are no longer outsiders and strangers. You are citizens together with God’s people. You are also members of God’s family. 20You are a building that is built on the apostles and prophets. They are the foundation. Christ Jesus himself is the most important stone in the building. 21The whole building is held together by him. It rises to become a holy temple because it belongs to the Lord. 22And because you belong to him, you too are being built together. You are being made into a house where God lives through his Spirit.