1 Tessalonikawa 2 – HCB & CRO

Hausa Contemporary Bible

1 Tessalonikawa 2:1-20

Aikin Bulus a Tessalonika

1Kun sani, ’yan’uwa, cewa ziyararmu a gare ku ba tă zama a banza ba. 2Mun riga mun sha wahala, aka kuma zage mu a Filibbi, kamar yadda kuka sani, amma da taimakon Allahnmu muka yi ƙarfin hali muka sanar muku bishararsa duk da matsananciyar gāba. 3Gama roƙon da muke yi bai fito daga kuskure ko munafunci ba, ba kuwa ƙoƙari muke yi mu yaudare ku ba. 4A maimako haka, muna magana ne kamar mutanen da Allah ya amince yă danƙa musu amanar wannan bishara. Ba ma ƙoƙari mu gamshi mutane sai dai Allah, mai auna zukatanmu. 5Kun san ba ma taɓa yin daɗin baki ko mu yi ƙoƙarin kasance da halin kwaɗayin da muke ɓoyewa, Allah shi ne shaidarmu. 6Ba ma neman yabo daga wurin mutane, ko a gare ku, ko ga waɗansu.

A matsayinmu na manzannin Kiristi da mun so, da mun nawaita muku, 7amma muka kasance masu sauƙinkai a cikinku, kamar yadda mahaifiya take lura da ƙananan ’ya’yanta. 8Muka ƙaunace ku ƙwarai har muka ji daɗin bayyana muku, ba bisharar Allah kaɗai ba amma har rayukanmu ma, domin kun zama ƙaunatattu a gare mu. 9Ba shakka kuna iya tunawa, ’yan’uwa, famarmu da kuma wahalarmu; mun yi aiki dare da rana don kada mu zama nauyi wa wani yayinda muke muku wa’azin bisharar Allah.

10Ku shaidu ne, haka ma Allah, na yadda muka yi zaman tsarki, adalci da kuma marar aibi a cikinku, ku da kuka ba da gaskiya. 11Gama kun san cewa mun bi da kowannenku yadda mahaifi yakan yi da ’ya’yansa, 12muna ƙarfafa ku, muna ta’azantar da ku, muna kuma gargaɗe ku ku yi rayuwar da za tă cancanci Allah, wanda ya kira ku zuwa mulkinsa da kuma ɗaukakarsa.

13Muna kuma gode wa Allah ba fasawa domin, sa’ad da kuka karɓi maganar Allah, wadda kuka ji daga gare mu, kun karɓe ta ba kamar maganar mutane ba, sai dai kamar yadda take, maganar Allah wadda take aiki a cikinku ku da kuka ba da gaskiya. 14Gama ku, ’yan’uwa, kun zama masu koyi da ikkilisiyoyin Allah a Yahudiya waɗanda suke cikin Kiristi Yesu. Kun sha wahala a hannun mutanen ƙasarku kamar yadda ikkilisiyoyin nan ma suka sha a hannun Yahudawa, 15waɗanda suka kashe Ubangiji Yesu da annabawa suka kuma kore mu. Ba sa yin aikin da Allah yake so, masu gāba ne kuwa da dukan mutane 16suna ƙoƙarin hana mu yin magana ga Al’ummai don kada su sami ceto. Ta haka kullum suke ƙara tara tsibin zunubansu. Fushin Allah ya aukar musu a ƙarshe.

Marmarin Bulus na ganin Tessalonikawa

17Amma, ’yan’uwa, sa’ad da aka raba mu da ku na ɗan lokaci (a jiki, ba a tunani ba), daga cikin marmarinmu mai tsanani mun yi duk abin da muke iya yi mu gan ku. 18Gama mun so mu zo wurinku, tabbatacce ni, Bulus, na yi ƙoƙari sau da sau, amma Shaiɗan ya hana mu. 19Gama mene ne begenmu, farin cikinmu, ko kuma rawanin da zai zama mana abin ɗaukaka a gaban Ubangijinmu Yesu sa’ad da ya dawo? Ba ku ba ne? 20Tabbatacce, ku ne ɗaukakarmu da kuma farin cikinmu.

Knijga O Kristu

1 Solunjanima 2:1-20

Pavao se sjeća posjeta Solunjanima

1Znate i sami, draga braćo i sestre, da naš dolazak k vama nije bio uzaludan. 2Znate da su nas prije toga u Filipima zlostavljali i izvrgnuli ruglu. Ipak smo se odvažili, pouzdajući se u Boga, propovijedati vam evanđelje, iako uz tešku borbu. 3Vidite dakle da u našemu propovijedanju nema govora o zabludi, nečistim pobudama ili prijevari.

4Navješćujemo Radosnu vijest upravo onako kako nam je Bog povjerio da činimo. Ne trudimo se ugoditi ljudima, nego Bogu koji proniče srca. 5Nikada vas nismo pokušali pridobiti laskanjem. Bog nam je svjedok i da nikada ništa nismo činili iz pohlepe. 6Niti smo od ljudi tražili slavu—ni od vas ni od bilo koga drugoga. 7Mogli smo od vas kao Kristovi apostoli što i zahtijevati, ali nismo. Bili smo prema vama blagi poput majke koja s ljubavlju njeguje svoju djecu. 8Toliko smo vas voljeli da smo vam htjeli predati ne samo Božju Radosnu vijest nego i vlastiti život.

9Pa sjećate se, draga braćo i sestre, našega teškog truda i umora! Dok smo vam propovijedali evanđelje, radili smo noću i danju da nikomu od vas ne budemo na teret. 10I vi i Bog ste nam svjedoci da smo se sveto, pravedno i besprijekorno vladali prema vama vjernicima. 11Postupali smo prema svakomu od vas kao otac prema vlastitoj djeci. 12Poticali smo vas, hrabrili i zaklinjali da živite životom dostojnim Boga koji vas je pozvao u svoje kraljevstvo da s njime dijelite njegovu slavu.

13Zato bez prestanka zahvaljujemo Bogu što Božju poruku koju smo vam navijestili niste primili kao ljudsku, nego kao Božju riječ, što ona uistinu i jest. A ona djeluje u vama koji vjerujete.

14Vi ste, draga braćo, pretrpjeli od svojih sunarodnjaka progonstvo te ste tako prošli jednako kao i članovi Božjih kršćanskih crkava u Judeji, koje su zbog vjere u Krista Isusa progonili njihovi vlastiti sunarodnjaci, Židovi. 15Oni su poubijali vlastite proroke, pa čak i Gospodina Isusa. Nas su žestoko progonili. Ne ugađaju Bogu i neprijatelji su svim ljudima 16jer nam priječe propovijedati poganima da se oni ne bi spasili. Navršili su tako mjeru svojih zlodjela. Navukli su na sebe najveći Božji gnjev.

Timotejeva pohvala Crkvi

17Draga braćo, pošto smo zakratko bili odvojeni od vas (ali ne i srcem), vruće smo čeznuli za vama te smo pokušali doći da vas vidimo. 18Zaista smo nastojali doći k vama, ja Pavao i više puta, ali Sotona nas je spriječio. 19Tko će, na koncu, biti naša nada i radost, naš ponos i naša nagrada pred našim Gospodinom Isusom kada opet dođe? 20Vi ste naša slava i naša radost!