1 Korintiyawa 1 – HCB & NIRV

Hausa Contemporary Bible

1 Korintiyawa 1:1-31

1Bulus, wanda aka kira domin yă zama manzon Kiristi Yesu, bisa ga nufin Allah, da kuma ɗan’uwanmu Sostenes,

2Zuwa ga ikkilisiyar Allah da take a Korint, da waɗanda aka tsarkake cikin Kiristi Yesu, aka kuma kira domin su zama masu tsarki, tare da dukan waɗanda suke ko’ina da suke kiran sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi, Ubangijinsu da kuma namu.

3Alheri da salama daga Allah Ubanmu, da Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku.

Godiya

4Ina gode wa Allah kullum dominku, saboda alherinsa da aka ba ku a cikin Kiristi Yesu. 5Gama a cikinsa kuka sami wadata ta kowace hanya, a cikin dukan maganarku, da kuma cikin dukan saninku 6gama shaidarmu game da Kiristi ta tabbata a cikinku. 7Saboda haka, ba ku rasa kowace baiwa ta ruhaniya ba, yayinda kuke jira da marmari, saboda bayyanuwar Ubangijinmu Yesu Kiristi. 8Zai ƙarfafa ku har zuwa ƙarshe, domin ku zama marasa aibi a ranar Ubangijinmu Yesu Kiristi. 9Allah, wanda ya kira ku zuwa ga zumunci tare da Ɗansa Yesu Kiristi Ubangijinmu, shi mai aminci ne.

Tsattsaguwa cikin ikkilisiya

10Ina roƙonku ’yan’uwa, a cikin sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi, dukanku ku yarda da juna, domin kada a sami tsattsaguwa a cikinku, domin kuma ku zama ɗaya, cikakku a cikin halinku da tunaninku. 11’Yan’uwana, waɗansu daga iyalin gidan Kulos sun gaya mini cewa, akwai faɗa a cikinku. 12Abin da nake nufi shi ne, ɗaya daga cikinku na cewa, “Ni ina bin Bulus,” wani na cewa, “Ni ina bin Afollos,” wani kuma, “Ni ina bin Kefas,” har wa yau wani kuma, “Ni ina bin Kiristi.”

13Kiristi a rabe ne? Bulus ne aka gicciye dominku? An yi muku baftisma a cikin sunan Bulus ne? 14Ina godiya domin ban yi wa wani baftisma a cikinku ba, sai dai Kirisbus da Gayus kaɗai. 15Don haka, ba wanda na iya cewa an yi muku baftisma a cikin sunana. 16(I, na kuma yi wa iyalin gidan Istifanas baftisma, ban da wannan, ban tuna da wani da na yi masa baftisma ba.) 17Gama Kiristi bai aike ni yin baftisma ba, sai dai wa’azin bishara ba da kalmomin hikimar mutum ba, domin kada gicciyen Kiristi ya rasa ikonsa.

Kiristi hikima da kuma ikon Allah

18Gama saƙon gicciye wauta ne ga waɗanda suke hallaka, amma a gare mu, mu da ake ceto, ikon Allah ne. 19Gama a rubuce yake cewa,

“Zan rushe hikimar mai hikima,

basirar mai azanci kuma zan rikita shi.”1.19 Ish 29.14

20Ina mai hikima? Ina mai zurfin bincike? Ina masana na wannan zamani? Ashe, Allah bai wofinta hikimar duniya ba? 21Gama tun da a cikin hikimar Allah, duniya a cikin hikimarta ba tă san shi ba, Allah ya ji daɗin ceton waɗanda suka ba da gaskiya ta wurin wautar wa’azin bishara. 22Yahudawa suna so su ga alama, Hellenawa kuma suna neman hikima, 23amma mu, muna wa’azin Kiristi wanda aka gicciye ne, wanda ya zama dutsen tuntuɓe ga Yahudawa, wauta kuma ga Al’ummai, 24amma ga su waɗanda Allah ya kira, Yahudawa da Hellenawa, Kiristi ikon Allah ne, da kuma hikimar Allah. 25Gama wautar Allah ta fi hikimar mutum, kuma rashin ƙarfin Allah ya fi ƙarfin mutum.

26’Yan’uwa, ku tuna yadda kuke sa’ad da aka kira ku. Babu masu hikima da yawa a cikinku, bisa ga ganin mutum; babu masu iko da yawa, babu masu martaba da yawa bisa ga haihuwa. 27Amma Allah ya zaɓi abubuwa masu wautata duniya, don yă kunyata masu hikima. Allah ya zaɓi abubuwa marasa ƙarfi na duniya, domin ya ba wa masu ƙarfi kunya. 28Ya zaɓi abubuwa marasa martaba na wannan duniya da kuma abubuwan da aka rena da abubuwan da ba a ɗauka a bakin kome ba, domin a wofinta abubuwan da ake ganinsu da daraja, 29domin kada wani ya yi taƙama a gabansa. 30Saboda Allah ne kuke cikin Kiristi Yesu, shi wanda ya zama hikima a gare mu daga Allah. Kiristi shi ne adalcinmu, da tsarkinmu, da kuma fansarmu. 31Saboda haka, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Duk wanda yake taƙama, ya yi taƙama a cikin Ubangiji.”1.31 Irm 9.24

New International Reader’s Version

1 Corinthians 1:1-31

1I, Paul, am writing this letter. I have been chosen to be an apostle of Christ Jesus just as God planned. Our brother Sosthenes joins me in writing.

2We are sending this letter to you, the members of God’s church in Corinth. You have been made holy because you belong to Christ Jesus. God has chosen you to be his holy people. He has done the same for all people everywhere who pray to our Lord Jesus Christ. Jesus is their Lord and ours.

3May God our Father and the Lord Jesus Christ give you grace and peace.

Paul Gives Thanks

4I always thank my God for you. I thank him because of the grace he has given to you who belong to Christ Jesus. 5You have been blessed in every way because of him. You have been blessed in all your speech and knowledge. 6God has shown that what we have spoken to you about Christ is true. 7There is no gift of the Holy Spirit that you don’t have. You are full of hope as you wait for our Lord Jesus Christ to come again. 8God will also keep you strong in faith to the very end. Then you will be without blame on the day our Lord Jesus Christ returns. 9God is faithful. He has chosen you to share life with his Son, Jesus Christ our Lord.

Taking Sides in the Church

10Brothers and sisters, I make my appeal to you. I do this in the name of our Lord Jesus Christ. I ask that all of you agree with one another in what you say. I ask that you don’t take sides. I ask that you are in complete agreement in all that you think. 11My brothers and sisters, I have been told you are arguing with one another. Some people from Chloe’s house have told me this. 12Here is what I mean. One of you says, “I follow Paul.” Another says, “I follow Apollos.” Another says, “I follow Peter.” And still another says, “I follow Christ.”

13Does Christ take sides? Did Paul die on the cross for you? Were you baptized in the name of Paul? 14I thank God that I didn’t baptize any of you except Crispus and Gaius. 15No one can say that you were baptized in my name. 16It’s true that I also baptized those who live in the house of Stephanas. Besides that, I don’t remember if I baptized anyone else. 17Christ did not send me to baptize. He sent me to preach the good news. He commanded me not to preach with wisdom and fancy words. That would take all the power away from the cross of Christ.

Christ Is God’s Power and Wisdom

18The message of the cross seems foolish to those who are lost and dying. But it is God’s power to us who are being saved. 19It is written,

“I will destroy the wisdom of those who are wise.

I will do away with the cleverness of those who think they are so smart.” (Isaiah 29:14)

20Where is the wise person? Where is the teacher of the law? Where are the great thinkers of our time? Hasn’t God made the wisdom of the world foolish? 21God wisely planned that the world would not know him through its own wisdom. It pleased God to use the foolish things we preach to save those who believe. 22Jews require signs. Greeks look for wisdom. 23But we preach about Christ and his death on the cross. That is very hard for Jews to accept. And everyone else thinks it’s foolish. 24But there are those God has chosen, both Jews and Greeks. To them Christ is God’s power and God’s wisdom. 25The foolish things of God are wiser than human wisdom. The weakness of God is stronger than human strength.

26Brothers and sisters, think of what you were when God chose you. Not many of you were considered wise by human standards. Not many of you were powerful. Not many of you belonged to important families. 27But God chose the foolish things of the world to shame the wise. God chose the weak things of the world to shame the strong. 28God chose the things of this world that are common and looked down on. God chose things considered unimportant to do away with things considered important. 29So no one can boast to God. 30Because of what God has done, you belong to Christ Jesus. He has become God’s wisdom for us. He makes us right with God. He makes us holy and sets us free. 31It is written, “The one who boasts should boast about what the Lord has done.” (Jeremiah 9:24)