雅各書 3 – CCBT & HCB

Chinese Contemporary Bible (Traditional)

雅各書 3:1-18

邪惡的舌頭

1我的弟兄姊妹,不要個個當教師,因為你們知道,我們為人師表的將受到更嚴格的評判, 2因為我們在許多方面難免有過失。如果誰在言語上沒有過失,他就是純全的人,也能在各方面保持自制。 3我們如果把嚼環放在馬嘴裡,便可以使牠順服,駕馭牠。 4一艘大船在遭遇暴風吹襲時,船身雖然龐大,但舵手只要操縱一個小小的舵,就能隨意駕駛它。

5同樣,人的舌頭雖然很小,卻能說誇大的話。

看啊,小火星能點燃大森林。 6舌頭就是火,是我們身體上的一個充滿邪惡的世界,能玷污人的全身,足以毀掉人的一生,它是從地獄點燃的火。 7自然界中的各類走獸、飛禽、爬蟲、水族都可以被馴服,也已經被人類馴服了, 8但無人能馴服自己的舌頭,因為舌頭是個無法控制的邪惡之物,充滿了致命的毒氣。 9我們用舌頭來讚美主和天父,也用舌頭來咒詛照著上帝的形像被造的人。 10讚美和咒詛竟然從同一張嘴裡發出來。我的弟兄姊妹,這是不應該的! 11同一個泉源能湧出甜苦兩樣水嗎? 12我的弟兄姊妹,無花果樹能結出橄欖嗎?葡萄樹能結出無花果嗎?一個鹹水泉必流不出甜水來。

天上的智慧

13你們當中誰是有智慧、有見識的呢?請他帶著來自智慧的謙和,在善行上表現出來。 14但如果你們心懷苦毒的嫉妒和自私的野心,就不要自誇說有智慧,也不要違背真理去撒謊。 15這種智慧並非來自天上,而是從世俗、私慾和魔鬼來的。 16哪裡有嫉妒和自私的野心,哪裡就會有混亂和各樣的惡事。

17但從天上來的智慧首先是純潔,然後是愛好和平、溫良柔順、充滿憐憫、多結善果、不存偏見、沒有虛偽。 18使人和睦的人撒下和平的種子,必收穫仁義的果實。

Hausa Contemporary Bible

Yaƙub 3:1-18

Ƙamewa harshe

1Kada yawancinku su so ɗaukan kansu a matsayin malamai, ’yan’uwana, domin kun san cewa mu da muke koyarwa za a yi mana shari’a mafi tsanani. 2Dukanmu mukan yi tuntuɓe a hanyoyi dabam-dabam. In wani bai taɓa yin kuskure a cikin maganarsa ba, shi cikakke ne, yana kuma iya ƙame dukan jikinsa.

3Sa’ad da muka sa linzamai a bakunan dawakai don mu sa su yi mana biyayya, mukan iya bin da dabbar gaba ɗaya. 4Ko kuwa misali, mu dubi jiragen ruwa, mana. Ko da yake suna da girma ƙwarai kuma iska mai ƙarfi ce take tura su, ana tuƙa su da ɗan ƙaramin sandan ƙarfe ne zuwa duk inda mai tuƙin jirgin yake so. 5Haka ma harshe yake, ga shi ɗan ƙanƙanin gaɓar jiki ne, amma sai manyan fariya. Ku dubi yadda ɗan ƙaramin ƙyastu yake ƙuna wa babban jeji wuta mana. 6Harshe ma wuta ne! A cikin duk gaɓoɓinmu, harshe shi ne tushen kowace irin mugunta, mai ɓata mutum gaba ɗaya, mai zuga zuciyar mutum ta tafasa, shi kuwa jahannama ce take zuga shi.

7Kowace irin dabba, tsuntsu, masu ja da ciki da kuma halittun da suke cikin teku an sarrafa su kuma mutum ne ya sarrafa, 8amma ba mutumin da zai iya ya sarrafa harshe. Mugu ne marar hutu, cike da dafi mai kisa.

9Da harshe mukan yabi Ubangijinmu da kuma Ubanmu, da shi kuma muke la’antar mutane, waɗanda aka halitta a kamannin Allah. 10Daga wannan baki guda yabo da la’ana suke fitowa. ’Yan’uwana, wannan bai kamata yă zama haka ba. 11Ruwa mai kyau da kuma ruwan gishiri zai iya fito daga maɓulɓula ɗaya? 12’Yan’uwana, itacen ɓaure yana iya haifar ’ya’yan zaitun, ko kuma itacen inabi yă haifi ’ya’yan ɓaure? Haka ma, maɓulɓular ruwan gishiri ba zai iya ba da ruwa mai kyau ba.

Hikima iri biyu

13Wane ne mai hikima da fahimta a cikinku? Bari yă nuna ta ta wurin rayuwarsa mai kyau, ta wurin ayyukan da aka yi cikin tawali’un da suke fitowa daga hikima. 14Amma in kuna cike da mugun kishi da kuma sonkai a cikin zukatanku, kada ku yi taƙama game da wannan, ko ku danne gaskiya. 15Irin wannan “hikima” ba daga sama ta sauko ba, ta duniya ce, ta rashin ruhaniya, ta Iblis kuma. 16Gama inda akwai kishi da sonkai, a can za a tarar da hargitsi da kowane irin mugun aiki.

17Amma hikimar da ta zo daga sama da fari tana da tsabta gaba ɗaya; sa’an nan mai ƙaunar salama ce, mai sanin ya kamata, mai biyayya, cike da jinƙai da aiki mai kyau, marar nuna bambanci, sahihiya kuma. 18Masu salama da suke shuki cikin salama sukan girbe adalci.