路加福音 5 – CCB & HCB

Chinese Contemporary Bible (Simplified)

路加福音 5:1-39

呼召门徒

1一天,耶稣站在革尼撒勒湖边,众人团团围着祂,要听上帝的道。 2祂看见湖边停着两条船,渔夫离了船正在洗网, 3就上了西门的那条船,请西门把船稍微划离岸边,然后坐在船上教导众人。 4耶稣讲完之后对西门说:“把船划到水深的地方去撒网捕鱼。”

5西门说:“老师,我们劳碌了一整夜,一无所获,但既然你这样吩咐,我就照你的话做。” 6他们把网撒下去,果然捕获很多鱼,差点把网撑破了, 7于是招呼另一条船上的同伴来帮忙。他们一起把两条船都装满了鱼,船几乎要沉下去了。

8西门·彼得见状,便跪倒在耶稣膝前说:“主啊,离开我,我是个罪人!” 9他和所有同伴们对捕到这么多鱼感到非常惊讶, 10包括西庇太的两个儿子雅各约翰。耶稣对西门说:“不要怕,从今以后,你将成为得人的渔夫。” 11于是他们把船靠岸后,撇下一切跟从了耶稣。

洁净麻风病人

12有一次,耶稣在一个小镇遇见一个浑身患麻风病的人,那人一看见耶稣,就俯伏在地上恳求说:“主啊,如果你肯,一定能使我洁净。”

13耶稣伸手摸他,说:“我肯,你洁净了吧!”他身上的麻风病立刻消失了。

14耶稣又嘱咐他:“不要把这事告诉别人,要去让祭司察看你的身体,照摩西的规定献上祭物,向众人证明你已经洁净了。”

15结果耶稣的名声传得更广了,成群的人聚集到祂那里听祂讲道、求祂医病。 16不过,祂还是常常退到旷野去祷告。

叫瘫子行走

17有一天,耶稣在教导人,旁边坐着来自加利利犹太耶路撒冷各地的法利赛人和律法教师,主的能力伴随着耶稣,使祂能医治病人。

18有人用担架抬着一个瘫痪的人想进到屋里,把他放在耶稣面前。 19可是人太挤了,无法进去,他们就爬上屋顶,掀开瓦片,把那病人连人带担架缒到耶稣面前。 20耶稣看见他们那么有信心,就对瘫子说:“朋友,你的罪得到赦免了!”

21那些法利赛人和律法教师开始议论起来:“这个说话亵渎上帝的人是谁啊?除了上帝以外,谁能够赦罪?”

22耶稣知道他们的想法,就问:“你们为什么心里议论呢? 23说‘你的罪得到赦免了’容易呢,还是说‘你起来行走’容易呢? 24如今我要让你们知道人子在世上有赦罪的权柄。”于是对瘫子说:“我吩咐你起来!收拾你的担架回家去吧。”

25那人立刻当众站了起来,拿起他躺卧的担架回家去了,不住地赞美上帝。 26众人都十分惊奇,一同赞美上帝,心里充满了敬畏,说:“今天我们看到神迹了!”

呼召利未

27后来耶稣外出时,看见一个名叫利未的税吏坐在收税站里,就对他说:“跟从我!” 28利未就起来,撇下一切跟从了耶稣。

29随后,他在家设宴款待耶稣,赴宴的人中有许多税吏和其他人。 30法利赛人和律法教师就向耶稣的门徒抱怨说:“你们为什么跟税吏和罪人一起吃喝呢?”

31耶稣答道:“健康的人不需要医生,有病的人才需要。 32我来不是要召义人悔改,乃是召罪人悔改。”

论禁食

33他们说:“约翰的门徒常常禁食祷告,法利赛人的门徒也是一样,可是你的门徒却又吃又喝。”

34耶稣说:“新郎还跟宾客在一起的时候,岂能让宾客禁食? 35但有一天新郎将被带走,那时他们就要禁食了。” 36耶稣又给他们讲了一个比喻,说:“没有人会从新衣服上撕下一块布来,补在旧衣服上。否则,不但新衣服撕破了,旧衣服和新补丁也不相称。 37同样,没有人把新酒装进旧皮囊里,否则新酒会把旧皮囊胀破,酒也漏了,皮囊也毁了。 38所以新酒一定要装在新皮囊里。 39但是,没有人喝过陈年老酒后,还愿意喝新酒,因为他会说,‘还是陈年老酒好。’”

Hausa Contemporary Bible

Luka 5:1-39

Kiran almajirai na farko

(Mattiyu 8.14-17; Markus 1.29-34)

1Wata rana, Yesu yana tsaye a bakin Tafkin Gennesaret, mutane kuma suna ta matsawa kewaye da shi, domin su ji maganar Allah, 2sai ya hangi jiragen ruwa biyu a bakin tafkin, waɗanda masu kamun kifi suka bari suna wankin abin kamun kifinsu. 3Sai ya shiga ɗaya jirgin ruwan da yake na Siman, ya kuma roƙe shi yă tura shi kaɗan daga gaci. Sai ya zauna a jirgin ruwan, ya koyar da mutane daga ciki.

4Da ya gama magana, sai ya ce wa Siman, “Ka tuƙa jirgin zuwa inda akwai zurfi, ka saukar da abin kamun kifinka ka kama kifi.”

5Siman ya amsa ya ce, “Ranka yă daɗe, duk dare mun yi ta fama ba mu kama kome ba, amma tun da ka ce haka, zan saki abin kamun kifin.”

6Da suka yi haka, sai suka kama kifi da yawa, har abin kamun kifinsu suka fara tsintsinkewa. 7Sai suka kira abokansu a ɗaya jirgin, su zo su taimake su, suka kuwa zo. Suka cika jiragen biyu da kifi cif, har jiragen suka fara nutsewa.

8Da Siman Bitrus ya ga wannan, sai ya fāɗi a gaban Yesu ya ce, “Rabu da ni, Ubangiji. Ni mai zunubi ne!” 9Gama mamaki ya kama shi da abokansa duka, saboda yawan kifin da suka kama. 10Yaƙub da Yohanna, ’ya’yan Zebedi, abokan aikin Siman su ma suka yi mamaki.

Sai Yesu ya ce wa Siman, “Kada ka ji tsoro, daga yanzu za ka riƙa kama mutane ne.” 11Sai suka jawo jiragen ruwansu zuwa gaci, suka bar kome da kome, suka bi shi.

Warkar da kuturu

(Mattiyu 8.1-4; Markus 1.40-45)

12Yayinda Yesu yake ɗaya daga cikin garuruwan nan, sai ga wani mutum wanda kuturta ta ci ƙarfinsa. Da ganin Yesu, sai ya fāɗi da fuskarsa a ƙasa, ya roƙe shi ya ce, “Ubangiji, in ka yarda, kana iya ka tsabtacce ni.”

13Yesu ya miƙa hannunsa ya taɓa mutumin ya ce, “Na yarda, ka zama da tsabta!” Nan da nan, sai kuturtar ta rabu da shi.

14Sai Yesu ya umarce shi ya ce, “Kada ka gaya wa kowa, amma ka tafi ka nuna kanka ga firist, ka kuma miƙa hadayu da Musa ya umarta, saboda tsarkakewarka ta zama shaida a gare su.”

15Duk da haka, labarinsa ya ƙara bazuwa sosai, har taron mutane suka dinga zuwa don jinsa, da kuma neman warkarwa daga cututtukansu. 16Amma Yesu sau da yawa, yakan keɓe kansa zuwa wuraren da ba kowa, yă yi addu’a.

Yesu ya warkar da shanyayye

(Mattiyu 9.1-8; Markus 2.1-12)

17Wata rana, da yake cikin koyarwa, waɗansu Farisiyawa da malaman dokoki waɗanda suka zo daga kowane ƙauye a Galili, Yahudiya da Urushalima kuwa suna zaune. Ikon Ubangiji yana nan don yă warkar da masu ciwo. 18Sai ga waɗansu mutane suka kawo wani shanyayye a kan tabarma. Suka yi ƙoƙari su shigar da shi cikin gidan, domin su kwantar da shi a gaban Yesu. 19Da suka ga babu hanyar da za su bi saboda taron, sai suka haura rufin, suka saukar da shi a kan tabarmarsa, ta bakin ramin da suka huda a rufin, suka ajiye shi a tsakiyar taron, a gaban Yesu.

20Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce, “Saurayi, an gafarta maka zunubanka.”

21Farisiyawa da malaman dokoki suka fara yin tunani a zukatansu, “Wane ne wannan mutum da yake saɓo haka? Wa zai iya gafarta zunubai, in ba Allah kaɗai ba?”

22Yesu ya san abin da suke tunani, sai ya yi tambaya ya ce, “Don me kuke tunanin waɗannan abubuwa a zukatanku? 23Wanne ya fi sauƙi, a ce, ‘An gafarta maka zunubanka,’ ko kuma a ce, ‘Tashi, ka yi tafiya’? 24Amma domin ku san cewa Ɗan Mutum yana da iko a duniya ya gafarta zunubai.” Sai ya ce wa shanyayyen, “Na ce maka, tashi, ɗauki tabarmarka ka tafi gida.” 25Nan da nan, ya tashi tsaye a gabansu, ya ɗauki tabarmar da yake kwance a kai, ya tafi gida, yana yabon Allah. 26Kowa ya yi mamaki, ya kuma yabi Allah. Suka cika da tsoro, suna cewa, “Mun ga abubuwan banmamaki yau.”

Kiran Lawi

(Mattiyu 9.9-13; Markus 2.13-17)

27Bayan wannan, sai Yesu ya fita, ya ga wani mai karɓar haraji, mai suna Lawi, yana zaune a wurin da ake karɓar haraji. Yesu ya ce masa, “Bi ni.” 28Sai Lawi ya tashi, ya bar kome da kome, ya bi shi.

29Sai Lawi ya shirya wa Yesu wani babban liyafa a gidansa. Wani babban taron na masu karɓar haraji, tare da waɗansu suna cin abinci tare da su. 30Amma Farisiyawa da malaman dokokin da suke a ƙungiyarsu, suka yi wa almajiransa gunaguni, suna cewa, “Don me kuke ci, kuke sha tare da masu karɓar haraji da masu zunubi?”

31Yesu ya amsa musu ya ce, “Ai, masu lafiya ba sa bukatar likita, sai dai marasa lafiya. 32Ban zo don in kira masu adalci ba, sai dai masu zunubi zuwa ga tuba.”

An tuhumi Yesu a kan azumi

(Mattiyu 9.14-17; Markus 2.18-22)

33Suka ce masa, “Almajiran Yohanna sukan yi azumi da addu’a, haka ma almajiran Farisiyawa, amma naka sai ci da sha.”

34Yesu ya amsa ya ce, “Za ku iya sa abokan ango yin azumi yayinda yake tare da su? 35Amma lokaci yana zuwa, da za a ɗauke ango daga gare su. A waɗancan kwanakin ne za su yi azumi.”

36Sai ya faɗa musu wannan misali ya ce, “Ba wanda yakan yage ƙyalle daga sabuwar riga ya yi wa tsohuwar riga faci. In ya yi haka, zai yage sabuwar rigar, kuma facin daga sabuwar ba zai dace da tsohuwar rigar ba. 37Kuma ba wanda yakan zuba sabon ruwan inabi a cikin tsofaffin salkuna. In ya yi haka, sabon ruwan inabi zai farfashe salkunan, ruwan inabin yă zube, salkunan kuma su lalace. 38A’a, sai dai a zuba sabon ruwan inabi a sababbin salkuna. 39Kuma ba wanda yakan so shan sabon ruwan inabi bayan ya sha tsohon, don yakan ce, ‘Ai, tsohon ya fi kyau.’ ”