罗马书 13 – CCB & HCB

Chinese Contemporary Bible (Simplified)

罗马书 13:1-14

服从政府的权柄

1人人都要服从政府的权柄,因为所有的权柄都是出于上帝。现存的政权都是上帝设立的。 2所以,抗拒权柄,就是抗拒上帝的命令,抗拒的人必自招惩罚。 3掌权者不是叫行善的惧怕,而是叫作恶的惧怕。你想不怕掌权的吗?就要行得正,这样你会得到称赞。 4要知道掌权者是上帝差遣的,对行得正的人有益处。然而,你若作恶,就该惧怕,因为他必将你绳之以法13:4 他必将你绳之以法”希腊文是“他配剑,不只是作作样子的”。。他是上帝的仆人,代表上帝秉公行义,惩奸罚恶。 5所以,你们必须服从,不单是为了避免受到惩罚,也是为了良心无愧。

6你们纳税也是为了同样的缘故,因为官长是上帝的仆人,负责管理这类事务。 7凡是别人该得的,都要给他。该得米粮的,就纳粮给他;该得税款的,就缴税给他;该惧怕的,就惧怕他;该尊敬的,就尊敬他。

爱邻如己

8凡事都不可亏欠人,但在彼此相爱方面要常常觉得做得不够。一个人爱别人,就成全了律法。 9因为“不可通奸、不可杀人、不可偷窃、不可贪婪”以及其他诫命,都可以总结成一句话——“爱邻如己”。 10人若有爱心,就不会作恶害人,所以爱成全了律法。

11还有,要知道现今是你们该醒过来的时候了!因为与初信的时候相比,我们得救的日子更近了。 12黑夜已深,天将破晓,我们要除掉黑暗的行为,穿上光明的盔甲13:12 穿上光明的盔甲”或译“带上光明的兵器”。13我们要为人端正,光明磊落,不可荒宴醉酒、好色邪荡、嫉妒纷争。 14你们要活出主耶稣基督的荣美13:14 活出主耶稣基督的荣美”希腊文是“穿上主耶稣基督”。,不要只顾放纵罪恶本性的私欲。

Hausa Contemporary Bible

Romawa 13:1-14

Biyayya ga masu mulki

1Dole kowa yă yi biyayya ga masu mulki, gama babu wani iko sai ko in Allah ya yarda. Duk hukumomin da muke su, naɗin Allah ne. 2Saboda haka, duk wanda ya yi tawaye ga hukuma yana yin tawaye da abin da Allah ya naɗa ne, waɗanda kuwa suke aikata haka, za su jawo wa kansu hukunci. 3Gama masu mulki ba abin tsoro ba ne ga waɗanda suke yin abin da yake daidai, sai dai ga waɗanda suke aikata laifi. Kana so ka rabu da jin tsoron wanda yake mulki? To, sai ka aikata abin da yake daidai, zai kuwa yabe ka. 4Gama shi bawan Allah ne don kyautata rayuwarka. Amma in ka aikata mugunta, to, sai ka ji tsoro, don ba a banza ne shugaba yake ɗaukan takobinsa ba. Shi fa bawan Allah ne, ta wurinsa ne fushin Allah yakan hukunta masu laifi. 5Saboda haka, dole a yi biyayya ga hukumomi, ba don gudun horo kawai ba amma don lamirinku.

6Shi ne ma ya sa kuke biyan haraji, gama hukumomin nan bayin Allah ne, waɗanda suke ba da dukan lokacinsu don aikin shugabanci. 7Ku ba wa kowa hakkinsa. In kuna da bashin haraji, sai ku biya; in kuɗin shiga ne, ku biya kuɗin shiga; in ladabi ne, ku yi ladabi; in kuma girmamawa ne, ku ba da girma.

Ku yi ƙauna, gama ranar ta yi kusa

8Kada hakkin kowa yă zauna a kanku, sai dai na ƙaunar juna, don mai ƙaunar maƙwabcinsa ya cika Doka ke nan. 9Umarnan nan, “Kada ka yi zina.” “Kada ka yi kisankai.” “Kada ka yi sata.” “Kada kuma ka yi ƙyashi.”13.9 Fit 20.13-15,17; M Sh 5.17-19; M Sh 5.21 Da dai duk sauran umarnai an ƙunshe su ne a wannan kalma “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.” 10Ƙauna ba ta cutar da maƙwabci. Saboda haka ƙauna cika Doka ce.

11Ku yi wannan domin kun san irin zamanin da kuke ciki. Lokaci ya yi da za ku farka daga barcinku, don cetonmu ya yi kusa yanzu fiye da lokacin da muka fara ba da gaskiya. 12Dare fa ya kusan ƙarewa; gari kuma yana gab da wayewa. Saboda haka bari mu kawar da ayyukan duhu mu kuma yafa kayan yaƙi na haske. 13Bari mu tafiyar da al’amuranmu yadda ya dace a yi da rana, ba a cikin shashanci da buguwa ba, ba cikin fasikanci da rashin kunya ba, ba kuma cikin faɗa da kishi ba. 14A maimakon haka, ku ɗauki halin Ubangiji Yesu Kiristi, kada kuma ku yi tunani game da yadda za ku gamsar da sha’awace-sha’awacen mutuntaka.