使徒行传 1 – CCB & HCB

Chinese Contemporary Bible (Simplified)

使徒行传 1:1-26

应许圣灵降临

1提阿非罗啊,在前一封信中,我从耶稣的生平和教导开始, 2一直谈到祂借着圣灵吩咐了自己选立的使徒,然后被接回天上。 3祂受难后用许多确凿的证据证实自己活着,在四十天之内屡次向使徒显现,与他们谈论上帝的国。 4有一次,耶稣和他们在一起吃饭的时候,叮嘱他们:“你们不要离开耶路撒冷,要在那里等候我对你们说过的天父的应许。 5因为从前约翰用水给你们施洗,但再过几天,你们要受圣灵的洗。”

6他们跟耶稣在一起的时候问祂:“主啊,你要在这时候复兴以色列国吗?” 7耶稣回答说:“天父照祂的权柄定下的时间、日期不是你们可以知道的。 8但圣灵降临在你们身上后,你们必得到能力,在耶路撒冷犹太全境和撒玛利亚,直到地极,做我的见证人。”

9耶稣说完这番话,就在他们眼前被提升天,被一朵云彩接去,离开了他们的视线。 10祂上升时,他们都定睛望着天空,忽然有两个身穿白衣的人站在他们身旁, 11说:“加利利人啊!你们为什么站在这里望着天空呢?这位离开你们被接到天上的耶稣,你们看见祂怎样升天,将来祂还要怎样回来。”

选立新使徒

12于是,他们从橄榄山回到耶路撒冷。橄榄山距离耶路撒冷不远,约是安息日允许走的路程1:12 按犹太人的传统,在安息日只能走约一公里远。13他们进城后,来到楼上自己住的房间。当时有彼得约翰雅各安得烈腓力多马巴多罗买马太亚勒腓的儿子雅各、激进党人西门雅各的儿子犹大14他们和耶稣的母亲玛丽亚、耶稣的弟弟们及几个妇女在一起同心合意地恒切祷告。

15那时,约有一百二十人在聚会,彼得站起来说: 16“弟兄们,关于带人抓耶稣的犹大,圣灵借着大卫的口早已预言,这经文必须要应验。 17这人原本是我们中间的一员,与我们同担使徒的职分。”

18犹大用作恶得来的钱买了一块田,他头朝下栽倒在那里,肚破肠流。 19这消息很快传遍了耶路撒冷,当地人称那块田为“亚革大马”,就是“血田”的意思。

20彼得继续说:“诗篇上写道,‘愿他的家园一片荒凉,无人居住’,又说,‘愿别人取代他的职位。’ 21-22所以,我们必须另选一个人代替犹大,与我们一同为主耶稣的复活做见证。他必须是从主耶稣接受约翰的洗礼起一直到主升天,始终与我们在一起的人。”

23被提名的有别号巴撒巴又叫犹士都约瑟马提亚两个人。 24-25大家便祷告说:“主啊!你洞悉人的内心,求你指明这两个人中你要拣选哪一个来担负使徒的职分。犹大丢弃了这职分,去了他该去的地方。” 26然后,他们抽签,抽中了马提亚,就把他列入十一使徒中。

Hausa Contemporary Bible

Ayyukan Manzanni 1:1-26

An ɗauki Yesu zuwa sama

1A littafina na farko, Tiyofilus, na rubuta game da dukan abin da Yesu ya fara yi, da abin da ya koyar 2har zuwa ranar da aka ɗauke shi zuwa sama, bayan ya ba da umarnai ta wurin Ruhu Mai Tsarki ga manzannin da ya zaɓa. 3Bayan wahalarsa, ya bayyana kansa ga waɗannan mutane ya kuma ba da tabbatattun alamu masu yawa cewa yana da rai. Ya bayyana a gare su har kwana arba’in ya kuma yi musu magana game da mulkin Allah. 4A wani lokaci, yayinda yake ci tare da su, ya ba su wannan umarni, “Kada ku bar Urushalima, amma ku jira kyautar da Ubana ya yi alkawari, wadda kuka ji na yi magana a kai. 5Gama Yohanna ya yi baftisma da1.5 Ko kuwa a cikin ruwa, amma a cikin ’yan kwanaki za a yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki.”

6Saboda haka, sa’ad da suka taru, sai suka tambaye shi, “Ubangiji, a wannan lokaci za ka mayar da mulki ga Isra’ila?”

7Ya ce musu, “Ba naku ba ne ku san lokuta ko ranakun da Uban ya shirya cikin ikonsa. 8Amma ku za ku karɓi iko sa’ad da Ruhu Mai Tsarki ya sauka a kanku; za ku kuma zama shaiduna cikin Urushalima, da kuma cikin dukan Yahudiya da Samariya, zuwa kuma iyakar duniya.”

9Bayan ya faɗi wannan, sai aka ɗauke shi sama a idanunsu sai wani girgije ya rufe shi daga ganinsu.

10Suna zuba ido a bisa, zuwa cikin sararin sama yayinda yake tafiya, nan da nan, sai ga mutane biyu saye da fararen riguna tsaye kusa da su. 11Sai suka ce, “Mutanen Galili, don me kuke tsaye a nan kuna duban sararin sama? Wannan Yesu, wanda aka ɗauke daga gare ku zuwa sama, zai komo daidai yadda kuka ga ya tafi sama.”

An zaɓi Mattiyas yă ɗauki matsayin Yahuda

12Sai suka koma Urushalima daga tudun da ake kira Dutsen Zaitun, tafiyar ranar Asabbaci guda daga birnin. 13Da suka iso, sai suka hau gidan sama, zuwa ɗakin da suke zama. Waɗanda suka kasance kuwa su ne,

Bitrus, Yohanna, Yaƙub da Andarawus;

Filibus da Toma;

Bartolomeyu da Mattiyu;

Yaƙub ɗan Alfayus da Siman Zilot, da kuma Yahuda ɗan Yaƙub.

14Waɗannan duka suka duƙufa cikin addu’a, tare da waɗansu mata da Maryamu mahaifiyar Yesu, da kuma tare da ’yan’uwansa.

15A waɗancan kwanakin Bitrus ya miƙe tsaye cikin ’yan’uwa masu bi (taron da ya yi kusan mutum ɗari da ashirin) 16ya ce, “’Yan’uwana, dole a cika Nassin nan da Ruhu Mai Tsarki ya yi magana tun da daɗewa ta bakin Dawuda game da Yahuda, wanda ya zama jagora ga waɗanda suka kama Yesu 17dā shi ɗaya ne cikinmu, ya kuma yi hidima a cikin aikin nan.”

18(Da ladar da ya samu saboda muguntarsa Yahuda ya sayi wani fili; a can ya fāɗi da kā, jikinsa ya fashe, hanjinsa kuma duk suka zubo. 19Kowa a Urushalima ya ji game da wannan, saboda haka suka kira wannan filin Akeldama, da yarensu, wato, Filin Jini.)

20Bitrus ya ce, “Gama yana a rubuce a cikin Littafin Zabura cewa,

“ ‘Bari wurinsa yă zama babu kowa;

kada kowa ya zauna a cikinsa,’1.20 Zab 69.25

kuma,

“ ‘Bari wani ya ɗauki matsayinsa na shugabanci.’1.20 Zab 109.8

21Saboda haka dole a zaɓi ɗaya daga cikin mutanen da suke tare da mu duk lokacin da Ubangiji Yesu yake shiga da fita a cikinmu, 22farawa daga baftisma ta Yohanna har zuwa sa’ad da aka ɗauke Yesu daga gare mu. Gama dole ɗaya daga waɗannan ya zama shaidar tashinsa daga matattu tare da mu.”

23Saboda haka suka gabatar da mutane biyu. Yusuf mai suna Barsabbas (da aka kuma sani da Yustus) da kuma Mattiyas. 24Sai suka yi addu’a suka ce, “Ubangiji, ka san zuciyar kowa. Nuna mana wanne a cikin waɗannan biyu da ka zaɓa 25ya karɓi wannan aikin manzanci, wanda Yahuda ya bari don yă tafi wurin da yake nasa.” 26Sa’an nan suka jefa ƙuri’u, ƙuri’ar kuwa ta fāɗo a kan Mattiyas; sai aka sa shi cikin manzannin nan goma sha ɗaya.