约翰福音 7 – CCB & HCB

Chinese Contemporary Bible (Simplified)

约翰福音 7:1-52

耶稣的弟弟不信祂

1之后,耶稣周游加利利,不愿去犹太地区,因为犹太人想要杀祂。 2犹太人的住棚节快到了, 3耶稣的弟弟们对祂说:“离开这里,去犹太过节吧,好让你的门徒在那里也看见你所做的啊! 4因为人想出名,都不会暗地里行事,你既然可以做这些事,就把自己显给世人看吧!” 5原来连祂的弟弟们也不信祂。

6耶稣对他们说:“我的时候还没有到,你们什么时候都很方便。 7世人不会恨你们,只会恨我,因为我指证他们行为邪恶。 8你们先去过节吧,我现在还不上去,因为我的时候还没有到。” 9耶稣说完这些话,仍留在加利利

耶稣过住棚节

10他们走了以后,耶稣避开了人们的注意,暗地里上去过节。 11节期到了,犹太人到处查问:“耶稣在哪里?”

12众人对祂议论纷纷,有些人说:“祂是好人,”有些说:“不,祂欺骗民众。” 13不过,没有人敢公开议论祂的事,因为害怕犹太人。

14节期约过了一半,耶稣来到圣殿教导人。 15犹太人感到惊奇,说:“这个人没有受过教育,怎么懂得这么多呢?”

16耶稣说:“我的教导不是出于我自己,而是出于差我来的那位。 17如果你们愿意遵行上帝的旨意,就能分辨这些教导是出于上帝,还是出于我自己。 18凭自己讲论的人是要寻求自己的荣耀,但人子真实无伪,毫无不义,祂是为了使差祂来的那位得荣耀。 19摩西不是把律法传给了你们吗?你们却没有一个人遵守。为什么想要杀我呢?”

20众人回答说:“你一定是被鬼附身了!谁要杀你啊?”

21耶稣说:“我行了一件神迹,你们都感到惊奇。 22摩西把割礼传给你们,你们也在安息日行割礼。其实割礼不是摩西定的,而是从祖先们的时代就有了。 23为了避免违背摩西的律法,行割礼的那一天就算是安息日,你们还是照行。那么,我在安息日使一个病人完全康复,你们为什么责怪我呢? 24不要根据外表来断定是非,要按公义的原则判断。”

耶稣是基督吗

25有些住在耶路撒冷的人说:“这不是他们要杀的那个人吗? 26你看祂这样公开讲道,居然没有人说什么,难道官长也真的认为祂是基督吗? 27可是基督来的时候,根本没有人知道祂从哪里来,我们却知道这个人是从哪里来的。”

28于是,耶稣在圣殿里高声教导人说:“你们知道我是谁,也知道我是从哪里来的。其实我来不是出于自己的意思,差我来的那位是真实的,你们不认识祂。 29但我认识祂,因为我是从祂那里来的,差我来的就是祂。” 30他们听了,想捉拿耶稣,只是没有人下手,因为祂的时候还没有到。

31人群中有许多人信了耶稣,他们说:“基督来的时候所行的神迹,难道会比这个人行得更多吗?”

32法利赛人听见众人这样议论耶稣,就联合祭司长派差役去抓祂。 33耶稣对众人说:“我暂时还会跟你们在一起,不久我要回到差我来的那位那里。 34那时你们要找我却找不到,你们也不能去我所在的地方。”

35犹太人彼此议论说:“祂要去哪里使我们找不着呢?难道祂要到我们犹太人侨居的希腊各地去教导希腊人吗? 36祂说我们找不到祂,又不能去祂所在的地方,是什么意思?”

活水的江河

37节期最后一天,也是整个节期的高潮,耶稣站起来高声说:“人若渴了,可以到我这里来喝。 38正如圣经所言,信我的人,‘从他里面要流出活水的江河来’。” 39耶稣这话是指信祂的人要得到圣灵,但当时圣灵还没有降临,因为耶稣还没有得到荣耀。

40听见这些话后,有些人说:“祂真是那位先知。” 41也有些人说:“祂是基督。”还有些人说:“不会吧,基督怎么会出自加利利呢? 42圣经上不是说基督是大卫的后裔,要降生在大卫的故乡伯利恒吗?” 43众人因为对耶稣的看法不同,就起了纷争。 44有些人想抓祂,只是没有人下手。

犹太官长不信耶稣

45祭司长和法利赛人看见差役空手回来,就问:“你们为什么不把祂带来呢?”

46差役答道:“从未有人像祂那样说话!”

47法利赛人说:“难道你们也被祂迷惑了吗? 48哪有官长和法利赛人信祂呢? 49这群不明白律法的民众该受咒诅!”

50曾经夜访耶稣、属于他们当中一员的尼哥德慕说: 51“难道不听被告申辩,不查明事实真相,我们的律法就定祂的罪吗?”

52他们回答说:“难道你也是加利利人吗?你去查查看,就会知道没有先知是从加利利来的。”

Hausa Contemporary Bible

Yohanna 7:1-53

Yesu ya tafi Bikin Tabanakul

1Bayan wannan, sai Yesu ya yi ta zagawa a cikin Galili, da ganga bai yarda yă je Yahudiya ba domin Yahudawa a can suna nema su kashe shi. 2Amma sa’ad da Bikin Tabanakul na Yahudawa ya yi kusa, 3sai ’yan’uwan Yesu suka ce masa, “Ya kamata ka bar nan ka tafi Yahudiya, don almajiranka su ga ayyukan banmamaki da kake yi. 4Ba wanda yake so a san shi da zai yi abu a ɓoye. Da yake kana yin waɗannan abubuwa, sai ka nuna kanka ga duniya.” 5Domin ko ’yan’uwansa ma ba su gaskata da shi ba.

6Saboda haka Yesu ya ce musu, “Lokacina bai yi ba tukuna; amma a gare ku kowane lokaci daidai ne. 7Duniya ba za tă iya ƙinku ba, amma ni take ƙi domin ina shaida cewa ayyukanta mugaye ne. 8Ku ku tafi Bikin, ba zan haura zuwa wannan Bikin ba yanzu, domin lokacina bai yi ba tukuna.” 9Da ya faɗa haka, sai ya dakata a Galili.

10Amma fa, bayan ’yan’uwansa suka tafi Bikin, shi ma ya tafi, ba a fili ba, amma a ɓoye. 11A Bikin kuwa, Yahudawa suka yi ta nemansa, suna cewa, “Ina mutumin yake?”

12A cikin taron kuwa aka yi ta raɗe-raɗe game da shi. Waɗansu suka ce, “Shi mutumin kirki ne.”

Waɗansu kuwa suka ce, “A’a, ai, ruɗin mutane yake.” 13Amma ba wanda ya ce kome a fili game da shi don tsoron Yahudawa.

Yesu ya koyar a bikin

14Sai bayan da aka kai tsakiyar Bikin, sa’an nan Yesu ya haura zuwa filin haikali ya fara koyarwa. 15Yahudawa suka yi mamaki suna tambaya, “Yaya wannan mutum ya sami wannan sani haka ba tare da ya yi wani karatu ba?”

16Yesu ya amsa ya ce, “Koyarwata ba tawa ba ce, ta fito ne daga wurin wanda ya aiko ni. 17Duk wanda ya zaɓi yin nufin Allah, zai gane ko koyarwata daga Allah ce, ko kuwa don kaina ne nake magana. 18Mai magana don kansa, neman ɗaukakar kansa yake yi. Amma mai neman ɗaukakar wanda ya aiko shi, shi ne mai gaskiya, ba kuwa rashin gaskiya a gare shi. 19Ashe, ba Musa ba ne ya ba ku Doka? Duk da haka ba ko ɗayanku da yake kiyaye Dokar. Me ya sa kuke nema ku kashe ni?”

20Taron suka amsa suka ce, “Kana da aljani, wane ne yake so yă kashe ka?”

21Yesu ya ce musu, “Na yi abin banmamaki ɗaya, dukanku kuwa kuka yi mamaki. 22Duk da haka, domin Musa ya bar muku kaciya (ko da yake a gaskiya, ba daga wurin Musa ne ya fito ba, sai dai daga wurin kakannin kakanninku), ga shi kuna yin wa yaro kaciya a ranar Asabbaci. 23To, in za a iya yin wa yaro kaciya a ranar Asabbaci don kada a karya dokar Musa, don me kuke fushi da ni saboda na warkar da mutum a ranar Asabbaci? 24Ku daina yin shari’a bisa ga ganin ido, sai dai ku yi shari’a bisa ga adalci.”

Shin, Yesu shi ne Kiristi?

25A nan ne fa waɗansu mutane daga Urushalima suka fara tambaya suna cewa, “Ashe, ba wannan mutum ne suke nema su kashe ba? 26Ga shi nan yana magana a fili, su kuma ba su ce masa uffam ba. Ko hukumomi sun yarda cewa shi ne Kiristi? 27Mun dai san inda mutumin nan ya fito; amma sa’ad da Kiristi ya zo ba wanda zai san inda ya fito.”

28Yesu yana cikin koyarwa a filin haikali ke nan, sai ya ɗaga murya ya ce, “I, kun san ni, kun kuma san inda na fito. Ban zo don kaina ba, sai dai shi da ya aiko ni mai gaskiya ne. Ba ku san shi ba, 29amma na san shi, domin ni daga wurinsa ne, kuma shi ya aiko ni.”

30Da jin haka, sai suka yi ƙoƙari su kama shi, sai dai ba wanda ya taɓa shi, don lokacinsa bai yi ba tukuna. 31Duk da haka, da yawa a cikin taron suka ba da gaskiya gare shi. Suka ce, “Sa’ad da Kiristi ya zo, zai yi abubuwan banmamaki fiye da na wannan mutum ne?”

32Farisiyawa suka ji taron suna raɗe-raɗen waɗannan abubuwa game da shi. Sai manyan firistoci da Farisiyawa suka aiki masu gadin haikalin su kama shi.

33Sai Yesu ya ce, “Ina tare da ku na ɗan ƙanƙanin lokaci ne kawai, sa’an nan zan koma wurin wanda ya aiko ni. 34Za ku neme ni, amma ba za ku same ni ba; inda nake kuwa, ba za ku iya zuwa ba.”

35Sai Yahudawa suka ce wa juna, “Ina mutumin nan yake niyyar tafiya da ba za mu iya samunsa ba? Zai je wurin mutanenmu da suke zaune warwatse a cikin Hellenawa, yă kuma koya wa Hellenawa ne? 36Me yake nufi da ya ce, ‘Za ku neme ni, amma ba za ku same ni ba,’ da kuma ‘Inda nake, ba za ku iya zuwa ba’?”

37A rana ta ƙarshe kuma mafi girma ta Bikin, Yesu ya tsaya ya yi magana da babbar murya ya ce, “Duk mai jin ƙishirwa, yă zo wurina yă sha. 38Duk wanda ya gaskata da ni, kamar yadda Nassi ya ce, kogunan ruwa masu rai za su gudana daga cikinsa.” 39Da wannan yana nufin Ruhu ke nan, wanda waɗanda suka gaskata da shi za su karɓa daga baya. Har yă zuwa wannan lokaci ba a ba da Ruhu ba tukuna, da yake ba a riga an ɗaukaka Yesu ba.

40Da jin kalmominsa, waɗansu mutane suka ce, “Ba shakka, mutumin nan shi ne Annabin.”

41Waɗansu suka ce, “Shi ne Kiristi.”

Waɗansu har wa yau suka ce, “Yaya Kiristi zai fito daga Galili? 42Nassi bai ce Kiristi zai fito daga zuriyar Dawuda, daga kuma Betlehem garin da Dawuda ya zauna ba?” 43Sai mutanen suka rabu saboda Yesu. 44Waɗansu suka so su kama shi, sai dai ba wanda ya taɓa shi.

Rashin bangaskiyar shugabannin Yahudawa

45A ƙarshe masu gadin haikali suka koma wurin manyan firistocin da Farisiyawa, waɗanda suka tambaye su cewa, “Don me ba ku kawo shi nan ba?”

46Sai masu gadin suka ce, “Kai, babu wanda ya taɓa magana kamar wannan mutum.”

47Sai Farisiyawa suka amsa cikin fushi suka ce, “Af, kuna nufi har da ku ma ya ruɗe ku ke nan? 48Akwai wani daga cikin masu mulki ko cikin Farisiyawan da ya gaskata da shi? 49A’a! Sai dai wannan taron da ba su san kome game da Doka ba, la’anannu ne.”

50Nikodimus, wanda ya je wurin Yesu dā, wanda kuma yake ɗayansu ya ce, 51“Ashe, dokarmu takan hukunta mutum ba tare da an fara ji daga bakinsa game da abin da yake yi ba?”

52Sai suka amsa suka ce, “Kai ma daga Galili ne? Bincika ka gani, za ka iske cewa ba annabin da zai fito daga Galili.”

[Rubuce-rubucen farko-farko da kuma mafi ingancin da aka fi dogara da su tare da waɗansu shaidu na dā ba su da Yoh 7.53–8.11. Kaɗan daga cikin rubuce-rubucen hannu na dā sun ƙunshi waɗannan ayoyi, ko gaba ɗayansu ko kuma sashensu kawai bayan Yoh 7.36, Yoh 21.25, Luk 21.38 ko kuwa Luk 24.53.]

53Sai kowannensu ya koma gidansa.