启示录 18 – CCB & HCB

Chinese Contemporary Bible (Simplified)

启示录 18:1-24

巴比伦的下场

1之后,我看见另一位执掌大权的天使从天降下,他的荣光照亮了大地。 2他用强有力的声音喊着说:

巴比伦大城倒塌了!倒塌了!

她成了鬼魔的住处、

各样污鬼的监狱和一切可憎的不洁鸟兽的牢笼!

3因为列国都被她荒淫的烈酒灌醉了。

地上的君王曾经与她通奸,

地上的商人也因她穷奢极侈的生活而发了财。”

4我听见天上又有一个声音说:

“我的子民啊,离开那城,

以免沾染她的罪恶,

受她所受的灾祸。

5因为她已经罪恶滔天,

上帝没有忘记她一切的不义。

6她怎样待人,

你们也要怎样待她,

要按她所做的加倍地报应她,

用她调酒的杯加倍地调给她喝。

7她过去怎样自炫自耀、

奢华荒淫,

现在也要让她怎样痛苦哀伤。

因为她心里说,

‘我贵为女王,不是寡妇,

绝不会经历哀伤。’

8所以在一天之内,

她的灾祸,就是死亡、

哀伤和饥荒要同时临到她身上。

她要被火烧尽,

因为审判她的主上帝能力伟大。

9“那些曾与她通奸享乐的君王目睹焚烧她的烟,必为她哭泣哀号。 10他们对她所受的灾祸充满恐惧,就远远地站着说,

“‘强大坚固的巴比伦城啊,

真悲惨!真悲惨!

因为审判顷刻间临到你了。’

11“地上的商人也为她哀伤,因为再也没有人购买他们的货物了。 12他们的金、银、宝石、珍珠、细麻布、紫布、丝绸、朱红布、各样香木、象牙器具,贵重木材、铜、铁、大理石制品, 13以及肉桂、豆蔻、香料、香膏、乳香、酒、油、细面粉、小麦、牛、羊、马、车、仆婢和人口都没有人购买了。 14他们呼喊,‘巴比伦啊!你贪爱的美物已离你而去了,一切珍馐百味、奢侈华丽的东西都消失殆尽,无影无踪。’

15“靠贩卖这些货物给她而致富的商人对她所受的灾祸充满恐惧,就站在远处为她哀伤哭号, 16说,‘身穿紫色和朱红色的细麻布衣服,以黄金、宝石、珍珠为装饰的大城啊,真悲惨!真悲惨! 17因为顷刻间你这一切的繁华都化为乌有了。’所有船主、乘客、水手及靠海为生的人都远远地站着, 18看见烧她的烟,就说,‘有哪一座城能与她相比呢?’ 19他们又把尘土撒在头上,哀伤哭泣,喊着说,

“‘这大城啊,真悲惨!真悲惨!

所有经营航运的都因她的奢华而发了财,

可是顷刻间她却沦为废墟了!’

20上天啊,

众圣徒、众使徒和众先知啊,

为她的下场欢乐吧!

因为上帝已经向她施行报应,

为你们申冤了。”

21这时,有一位大力天使举起一块像大磨石的石头扔进海里,说:

巴比伦大城也必这样被用力扔下去,

消失得无影无踪。

22在你那里,

再也听不见弹琴作乐、

鸣笛吹号的声音了,

再也找不到能工巧匠了,

再也听不到推磨的声音了,

23再也看不到闪耀的灯光了,

再也听不见新婚夫妇的欢笑声了。

因为你的商人曾经趾高气扬,

你的邪术曾经迷惑万国,

24你的城墙内流满了众先知、

众圣徒和地上一切被杀之人的血。”

Hausa Contemporary Bible

Ruʼuya ta Yohanna 18:1-24

Makoki a kan Babilon

1Bayan wannan sai na ga wani mala’ika yana saukowa daga sama. Yana da iko mai girma, aka haskaka duniya da darajarsa. 2Ya yi kira da babbar murya ya ce,

“Ta fāɗi! Babilon Mai Girma ta fāɗi.

Ta zama gidan aljanu

da kuma wurin zaman kowace irin mugun ruhu,

wurin zaman kowane irin tsuntsu marar tsabta da mai banƙyama.

3Gama dukan al’ummai sun sha ruwan inabin

haukan zinace zinacenta.

Sarakunan duniya sun yi zina tare da ita,

attajiran duniya kuma sun arzuta da almubazzarancinta.”

4Sai na ji wata murya daga sama ta ce,

“Ku fita daga cikinta, mutanena,

don kada zunubanta su shafe ku,

don kada wata annobarta ta same ku;

5gama zunubanta sun yi tsororuwa sun kai sama.

Allah kuma ya tuna da laifofinta.

6Ku sāka mata kamar yadda ta sāka muku;

ku sāka mata sau biyu na abin da ta yi.

Ku dama mata sau biyu na abin da yake cikin kwaf nata.

7Ku ba ta isashen azaba da baƙin ciki

kamar daraja da kuma jin daɗin da ta ba wa kanta.

A zuciyarta takan yi taƙama, ta ce,

‘Ina zama kamar sarauniya;

ni ba gwauruwa ba ce,

kuma ba zan taɓa yin makoki ba.’

8Saboda haka a rana ɗaya annobarta za su cim mata,

mutuwa, makoki da kuma yunwa.

Wuta zai cinye ta,

gama Ubangiji Allah mai girma ne, wanda yake shari’anta ta.

9“Sa’ad da sarakunan duniya da suka yi zina da ita suka kuma yi tarayya cikin jin daɗinta suka ga hayaƙin ƙunarta, za su yi kuka da makoki saboda ita. 10Don tsoron ganin azabarta za su tsaya daga nesa, su yi kuka suna cewa,

“ ‘Kaito! Kaito, ya birni mai girma.

Ya ke Babilon, birni mai iko!

Cikin sa’a guda hallakarki ta zo!’

11“Attajiran duniya za su yi kuka su kuma yi makoki a kanta, domin ba wanda yake ƙara sayen kayayyakinsu 12kayayyakin zinariya, azurfa, duwatsu masu daraja da lu’ulu’ai; lallausan lilin, tufa masu ruwan shunayya, siliki da jan tufa; da kowane irin katakai masu ƙanshi da kayayyaki na kowane iri da aka yi da hauren giwa, katakai masu tsada, tagulla, baƙin ƙarfe da dutse mai sheƙi; 13kayayyakin sinnamon da kayan yaji, na turaren wuta, mur da turare, na ruwan inabi da man zaitun, na gari mai laushi da alkama; shanu da tumaki; dawakai da kekunan doki, da jikuna da kuma rayukan mutane.

14“Za su ce, ‘Amfanin da kike marmari ya kuɓuce. Dukan arzikinki da darajarki sun ɓace, ba kuwa za a ƙara samunsu ba.’ 15Attajiran da suka sayar da waɗannan kayayyaki suka kuma sami arzikinsu daga gare ta za su tsaya daga nesa, cike da tsoron ganin azabarta. Za su yi kuka da makoki 16su ce,

“ ‘Kaito! Kaito, ya birni mai girma,

saye da lallausan lilin, shunayya da kuma ja,

mai walƙiya da zinariya, duwatsu masu daraja da kuma lu’ulu’ai!

17Cikin sa’a guda irin wannan dukiya mai yawa ta hallaka!’

“Duk matuƙan jirgin ruwa, da dukan waɗanda suke tafiya a jirgin ruwa, ma’aikatanta, da duk masu samun abin zama gari daga teku za su tsaya daga nesa. 18Sa’ad da suka ga hayaƙin ƙunarta, za su yi ihu su ce, ‘An taɓa samun birni kamar wannan babban birnin kuwa?’ 19Za su zuba ƙura a kawunansu, da kuka da makoki za su yi ta kururuwa,

“ ‘Kaito! Kaito, ya birni mai girma,

inda dukan waɗanda suke da jiragen ruwa a teku

suka arzuta da ɗumbun dukiyarsa!

Cikin sa’a ɗaya ta hallaka!’

20“Ki yi murna a kanta, ya sama!

Ku yi murna, ku tsarkaka!

Ku yi murna, ku manzanni da annabawa!

Allah ya hukunta shi

saboda abin da ya yi muku.”

21Sa’an nan wani mala’ika mai ƙarfi ya ɗauki dutse kamar girman babban dutsen niƙa ya jefa cikin teku ya ce,

“Da wannan irin giggitawa

za a jefar da birnin Babilon mai girma ƙasa,

ba za a ƙara ganin ta ba.

22Ba za a ƙara jin

ƙarar kiɗin masu garaya da muryar mawaƙa, da na masu bushe-bushe, da na masu busan ƙaho

a cikinki ba.

Ba za a ƙara samun ma’aikaci na kowace irin sana’a

a cikinki kuma ba.

Ba za a ƙara jin ƙarar dutsen niƙa

a cikinki kuma ba.

23Hasken fitila ba zai ƙara haskakawa

a cikinki ba.

Ba za a ƙara jin muryar ango da amarya

a cikinki ba.

Attajiranki, dā su ne manyan mutanen duniya.

Ta wurin sihirinki, dukan ƙasashe sun kauce.

24A cikinta aka sami jinin annabawa, da na tsarkaka,

da kuma na dukan waɗanda aka kashe a duniya.”