启示录 19 – CCB & HCB

Chinese Contemporary Bible (Simplified)

启示录 19:1-21

天上的赞美

1这事以后,我听见天上好像有一大群人在呼喊:“哈利路亚19:1 哈利路亚”意思是“要赞美上帝”。!救赎、荣耀和权能都归于我们的上帝! 2因为祂的审判真实公义,祂惩罚了那用淫乱败坏世界的大淫妇,为那些被她杀害的奴仆申冤。” 3他们又欢呼说:“哈利路亚!焚烧大淫妇的烟不断上腾,直到永永远远。” 4那二十四位长老和四个活物也俯伏敬拜坐在宝座上的上帝,说:“阿们!哈利路亚!”

5这时从宝座那里发出声音,说:“上帝所有的奴仆和一切敬畏祂的人,无论尊卑老少,都要赞美我们的上帝!” 6我听见有声音好像一大群人的呼喊声,又像洪涛,也像雷鸣,说:“哈利路亚!因为我们的主——全能的上帝已经执掌王权了。 7我们应当欢喜快乐,归荣耀给祂,因为羔羊的婚期到了,祂的新娘已预备妥当, 8获准穿上光亮洁白的细麻衣。”这细麻衣代表圣徒的义行。

9天使吩咐我说:“你要写下来,被邀请参加羔羊婚宴的人有福了!”他又说:“这是上帝亲口说的,千真万确。” 10我俯伏在他脚前要拜他,他却说:“千万不可!我和你并那些为耶稣做见证的弟兄姊妹同是上帝的奴仆。你要敬拜上帝,因为预言的真谛就是为耶稣做见证。”

白马骑士

11我看见天开了,有一匹白马出来,马上的骑士名叫“诚信真实”,祂凭公义审判、作战。 12祂的双目如火焰,头上戴了许多冠冕,写着一个只有祂自己才明白的名字。 13祂穿着被鲜血浸透的衣服,祂的名字是“上帝的道”。 14众天军穿着洁白的细麻衣,骑着白马跟随祂。 15祂口中吐出一把利剑,可以攻击列国。祂必用铁杖统治他们,踩踏盛满全能上帝之烈怒的榨酒池。 16祂的衣服和大腿上都写着祂的名号:“万王之王,万主之主。”

17我又看见一位天使站在太阳里,对空中飞翔的鸟大声呼唤: 18“来吧!一起来参加上帝的盛宴,一同享用君王、将军、勇士、马匹、骑士、自由人、奴隶和尊卑老少的肉吧!”

19我看见那怪兽、地上的众王及其军队聚集起来,要与白马骑士和祂的军队作战。 20后来,怪兽被俘虏了,在怪兽面前行奇迹的假先知也一同被擒了。这假先知曾用奇迹欺骗那些盖了兽印、敬拜兽像的人。他和怪兽一同被活活地扔进硫磺火湖里。 21怪兽的残兵纷纷被白马骑士口中的利剑所杀,飞鸟饱餐了他们的肉。

Hausa Contemporary Bible

Ruʼuya ta Yohanna 19:1-21

Halleluya sau uku a kan fāɗuwar Babilon

1Bayan wannan sai na ji abin da ya yi kamar ƙasaitaccen taron mutane a sama, suna cewa,

“Halleluya!

Ceto da ɗaukaka da iko sun tabbata ga Allahnmu,

2gama hukuncinsa daidai ne, mai adalci kuma.

Ya hukunta babbar karuwan nan

wadda ta ɓata duniya da zinace zinacenta.

Ya rama jinin bayinsa a kanta.”

3Suka sāke tā da murya suka ce,

“Halleluya!

Hayaƙin yake fitowa daga wurinta ya yi ta tashi sama har abada abadin.”

4Dattawan nan ashirin da huɗu da halittu huɗun nan masu rai suka fāɗi suka yi wa Allah sujada, wannan da yake zaune a kursiyi. Suka tā da murya suka ce,

“Amin, Halleluya!”

5Sa’an nan wata murya ta fito daga kursiyin, tana cewa,

“Ku yabi Allahnmu,

dukanku da kuke bayinsa,

ku da kuke tsoronsa,

babba da yaro!”

6Sai na ji wani abu mai ƙara kamar ƙasaitaccen taron mutane, kamar rurin ruwaye masu gudu da kuma kamar bugun tsawa mai ƙarfi, suna tā da murya suna cewa,

“Halleluya!

Gama Ubangiji Allahnmu Maɗaukaki ne yake mulki.

7Bari mu yi farin ciki mu kuma yi murna

mu kuma ɗaukaka shi!

Domin lokacin auren Ɗan Ragon ya yi,

amaryarsa kuwa ta shirya kanta.

8Aka ba ta lallausan lilin, mai haske da tsabta

ta sanya.”

(Lallausan lilin yana misalta ayyukan adalci na tsarkaka.)

9Sai mala’ikan ya ce mini, “Rubuta, ‘Masu albarka ne waɗanda aka gayyace su zuwa bikin auren Ɗan Ragon!’ ” Sai ya ƙara da cewa, “Waɗannan su ne kalmomin Allah da gaske.”

10Da wannan sai na fāɗi a gabansa, don in yi masa sujada. Amma ya ce mini, “Kada ka yi haka! Ni ma abokin bauta ne da kai da kuma ’yan’uwanka waɗanda suke riƙe da shaidar Yesu. Ka yi wa Allah sujada! Domin shaidar Yesu ita ce ruhun annabci.”

Mahayi a kan farin doki

11Sai na ga sama a buɗe can kuwa a gabana ga farin doki, sunan mahayinsa Mai Aminci da Mai Gaskiya ne. Da adalci yake shari’a yake kuma yaƙi. 12Idanunsa sun yi kamar harshen wuta, a kansa kuwa akwai rawani masu yawa. Yana da suna rubuce a kansa da babu wanda ya sani sai dai shi. 13Yana saye da rigar da aka tsoma a jini, sunansa kuwa Kalman Allah ne. 14Mayaƙan sama suna biye da shi, suna hawan fararen dawakai, saye da fararen tufafi masu tsabta na lallausan lilin. 15Daga bakinsa takobi mai kaifi ya fito. Da shi zai karkashe al’ummai. “Zai yi mulkinsu da sandan sarautar ƙarfe.” Yana tattake wurin matsin ruwan inabi na fushin Allah Maɗaukaki. 16A rigarsa da kuma a cinyarsa akwai wannan suna a rubuce,

Sarkin sarakuna da Ubangijin iyayengiji.

17Na kuma ga wani mala’ika tsaye a cikin rana, wanda ya yi kira da babbar murya ga dukan tsuntsaye da suke tashi sama a tsakiyar sararin sama cewa, “Ku zo, ku taru don babban bikin nan na Allah, 18don ku ci naman sarakuna, jarumawa, da kuma manyan mutane, na dawakai da mahayansu, da kuma naman dukan mutane, ’yantacce da bawa, babba da yaro.”

19Sa’an nan na ga dabbar da sarakunan duniya da mayaƙansu sun taru don su yi yaƙi da wannan wanda yake kan farin dokin da kuma mayaƙansa. 20Amma aka kama dabbar tare da annabin ƙaryan nan wanda ya aikata alamu masu banmamaki a madadinta. Da waɗannan alamun ne ya ruɗe waɗanda suka sami alamar dabbar suka kuma bauta wa siffarta. Aka jefa dukansu biyu da rai cikin tafkin wuta ta da farar wuta mai ci. 21Sauran kuma aka kashe su da takobin da ya fito daga bakin wannan wanda yake kan dokin. Dukan tsuntsaye kuwa suka ci namansu iyakar iyawarsu.