Marek 9 – SNC & HCB

Slovo na cestu

Marek 9:1-50

1Někteří z vás, jak tu stojíte, se ještě dočkají mocných projevů Božího království.“

Ježíš se proměňuje na hoře

2Po šesti dnech vzal s sebou Ježíš Petra, Jakuba a Jana a vystoupili na vršek hory.

Tam, daleko od lidí, se před očima učedníků stala s Ježíšem zvláštní proměna. 3Jeho tvář ozářila nadpozemská sláva a oděv se skvěl oslnivou bělostí, nedosažitelnou lidskými prostředky. Tu uviděli dva muže, jak s Ježíšem rozmlouvají; 4byli to Elijáš a Mojžíš.

5Petr zvolal: „Mistře, jak je dobře, žes nás vzal s sebou! Hned vám třem postavíme přístřeší.“

6Ani si vzrušením neuvědomoval, co říká; tak byli tím viděním vyvedeni z míry.

7Vtom je všechny zahalil oblak a z něho se ozval hlas: „Toto je můj milovaný Syn, toho poslouchejte!“

8Když se mrak rozplynul, učedníci se rozhlédli, ale kromě Ježíše už nikoho neviděli.

9Cestou dolů jim Ježíš přikázal, aby o té události nikomu nevyprávěli dříve, než vstane z mrtvých. 10Slíbili, že o tom zatím budou mlčet, ale vůbec nechápali, co myslel tím, že „vstane z mrtvých“.

11„Proč učitelé zákona říkají, že dříve než Kristus musí znovu přijít prorok Elijáš?“ otázali se Ježíše.

12-13„Ano, nejprve měl přijít Elijáš, aby dal vše do pořádku. A on také přišel a připravil mi cestu. Ovšem, jak je v Bibli předpověděno, naložili s ním, jak se jim zlíbilo. Ale všimněte si, že Písmo hovoří také o Synu člověka, jak musí velmi trpět a upadnout do opovržení.“

Ježíš uzdravuje chlapce posedlého démonem

14Když sestoupili k ostatním učedníkům, našli je obklopené množstvím lidí; mezi nimi byli i učitelé zákona, kteří se s učedníky o něčem dohadovali. 15Když však uviděli Ježíše, uctivě ztichli a šli mu naproti, aby ho uvítali.

16„O čem se dohadujete?“ zeptal se jich.

17Z davu vystoupil jeden muž:

„Mistře, přivedl jsem k tobě svého syna; je posedlý démonem, který ho připravuje o řeč i sluch. 18Kdykoliv se ho ten duch zmocní, svíjí se v křeči, skřípe zuby, z úst mu jde pěna a upadá do bezvědomí. Žádal jsem tvé učedníky, aby ho od toho osvobodili, ale nedokázali to.“

19„Ach, vy lidé,“ zvolal Ježíš, „jak dlouho bude trvat, než uvěříte? Jak dlouho vás budu ještě snášet a mít s vámi trpělivost? Přiveďte toho hocha ke mně!“

20Šli pro něj. Sotva se s však přiblížil k Ježíšovi, chlapec se svalil na zem a svíjel se s pěnou u úst.

21„Jak dlouho tím trpí?“ otázal se Ježíš otce.

„Už od malička. 22Často byl ve smrtelném nebezpečí, protože ten démon jím smýkal do ohně i do vody. Jestliže je to možné, slituj se a pomoz!“

23„Jestli je to možné?“ podivil se Ježíš. „Všechno je možné pro toho, kdo věří.“

24„Věřím, Pane, ale pomoz mi věřit víc!“ zvolal otec se slzami v očích:

25Ježíš si všiml, že se sbíhají další lidé, a tak přikázal: „Duchu, který ovládáš jeho smysly, vyjdi z něho – jednou provždy!“

26Mladík vykřikl, ještě jednou se zkroutil křečí a pak ztichl. Démon ho opustil. Hoch však zůstal ležet bez známek života. Davem proběhl šepot, že je mrtvý. 27Ale Ježíš ho vzal za ruku, zvedl jej a on se postavil. 28Když pak Ježíš vešel do domu a jeho učedníci s ním byli sami, zeptali se ho: „Proč jsme toho démona nemohli vyhnat my?“

29„Zde pomůže jen modlitba a půst,“ odpověděl jim.

Ježíš podruhé předpovídá svou smrt

30Když se odtamtud vydali na další cestu, procházeli Galileou, ale Ježíš si nepřál, aby se o něm lidé dozvěděli. 31Chtěl mít čas pro své učedníky. Znovu je připravoval na to, že Syn člověka – totiž on sám – bude vydán na pospas lidem, kteří ho zabijí. Ale třetí den po smrti zase vstane k životu.

32Oni tomu sice stále nerozuměli, styděli se však zeptat se ho.

Učedníci se přou o to, kdo z nich je větší

33Potom se vrátili do Ježíšova příbytku v Kafarnaum. Tam se Ježíš zeptal svých učedníků, o čem se to cestou dohadovali.

34Oni však mlčeli. Přeli se totiž, kdo z nich je významnější.

35Ježíš se posadil a shromáždil je kolem sebe. „Kdo chce být na prvním místě u mne, bude u lidí jako ten poslední a všem bude sloužit,“ řekl.

36Pak k sobě zavolal malé děcko a vzal je před nimi do náruče se slovy: 37„Kdo se zastane takového dítěte a přijme ho v mém jménu, přijímá mne. Nepřijímá však jenom mne, ale i toho, který mne poslal.“

Učedníci brání jiným mluvit v Ježíšově jménu

38„Mistře,“ hlásil mu Jan, „viděli jsme člověka, který tvým jménem vyhání démony, a nebyl to nikdo z našich. Zakázali jsme mu to, když mezi nás nepatří.“

39„Neměli jste mu bránit,“ odpověděl Ježíš. „Vždyť přece žádný, kdo v mém jménu učiní zázrak, nemůže se hned po tom obrátit proti mně. 40Kdo není proti nám, je s námi. 41A kdyby vám někdo podal sklenici vody jen proto, že jste moji – říkám vám, nepřijde o svou odměnu.

42Kdo by však připravil o víru někoho, kdo mi důvěřuje jako toto dítě, lépe by mu bylo uvázat mlýnský kámen na krk a hodit ho do moře.

Ježíš varuje před pokušením

43-44Svádí-li tě tvá ruka k činění zla, utni ji! Je pro tebe rozhodně lépe být bez ruky a mít jistotu, že budeš žít věčně, než mít obě ruce a jít do neuhasitelného ohně, odkud není vysvobození.

45-46Podobně – svádí-li tě ke zlému tvá noha, zbav se jí. Je lépe být chromý a mít jistý věčný život, než s oběma nohama navěky zahynout.

47-48A tak i oko: je-li původcem zla ve tvém životě, zbav se ho. Lépe je vejít do Božího království jednooký, než s oběma očima do věčného zahynutí.

49Ke každé oběti patří sůl.

50Sůl je dobrá věc. Ztratí-li však svou chuť a schopnost bránit rozkladu, čím ji nahradíte? Nebraňte se proto zkouškám a držte spolu.“

Hausa Contemporary Bible

Markus 9:1-50

1Ya kuma ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, waɗansu da suke tsattsaye a nan ba za su mutu ba, sai sun ga mulkin Allah ya bayyana da iko.”

Sāke kamannin Yesu

(Mattiyu 17.1-13; Luka 9.28-36)

2Bayan kwana shida, sai Yesu ya ɗauki Bitrus, Yaƙub da Yohanna tare da shi, ya kai su kan wani dutse mai tsawo, suka kasance su kaɗai a wurin. A can aka sāke kamanninsa a gabansu. 3Tufafinsa suka zama fari suna ƙyalli, fiye da yadda wani a duniya zai iya yi su. 4Iliya da Musa suka bayyana a gabansu, suna magana da Yesu.

5Bitrus ya ce wa Yesu, “Rabbi, ya yi kyau da muke nan. Bari mu kafa bukkoki guda uku, ɗaya dominka, ɗaya domin Musa, ɗaya kuma domin Iliya.” 6(Bai san abin da zai faɗa ba ne, gama sun tsorata ƙwarai.)

7Sai wani girgije ya bayyana, ya rufe su, wata murya kuma ta fito daga girgijen, ta ce, “Wannan Ɗana ne, wanda nake ƙauna, ku saurare shi!”

8Farat ɗaya, da suka waiwaya, ba su ƙara ganin kowa tare da su ba, sai dai Yesu.

9Da suna saukowa daga dutsen, Yesu ya umarce su kada su gaya wa kowa abin da suka gani, sai bayan Ɗan Mutum ya tashi daga matattu. 10Suka riƙe wannan zance a ɓoye tsakaninsu, suna tattaunawa ko mece ce ma’anar “tashi daga matattu.”

11Suka tambaye shi, suka ce, “Don me malaman dokoki suke cewa, sai Iliya ya fara zuwa?”

12Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya ne, Iliya zai zo da fari, yă kuma mayar da dukan abubuwa. Don me kuma aka rubuta cewa, dole Ɗan Mutum yă sha wahala sosai, kuma a ƙi shi? 13Amma ina faɗa muku, Iliya ya riga ya zo, kuma suka yi duk abin da suka ga dama da shi, kamar yadda aka rubuta game da shi.”

Warkar da yaro mai mugun ruhu

(Mattiyu 17.14-20; Luka 9.37-43)

14Da suka dawo wurin sauran almajiran, sai suka ga babban taro kewaye da su, malaman dokoki suna gardama da su. 15Nan take da dukan mutanen suka ga Yesu, sai suka cika da mamaki, suka ruga da gudu don su gai da shi.

16Ya tambaye su ya ce, “Gardamar me kuke yi da su?”

17Wani mutum a cikin taron ya amsa ya ce, “Malam, na kawo maka ɗana mai wani ruhun da yake hana shi magana. 18Duk lokacin da mugun ruhun ya kama shi, yakan jefa shi a ƙasa. Bakinsa yakan yi kumfa, yă cije haƙorarsa, yakan sa jikinsa ya sandare, yă zama da ƙarfi. Na roƙi almajiranka su fitar da ruhun, amma ba su iya ba.”

19Yesu ya ce, “Ya ku zamani marar bangaskiya, har yaushe zan kasance tare da ku? Har yaushe zan yi haƙuri da ku? Kawo mini yaron.”

20Sai suka kawo shi. Da ruhun ya ga Yesu, nan da nan sai ya buge yaron da farfaɗiya. Ya fāɗi a ƙasa, yana birgima, bakinsa yana kumfa.

21Yesu ya tambayi mahaifin yaron ya ce, “Tun yaushe yake haka?”

Ya ce, “Tun yana ƙarami. 22Ya sha jefa shi cikin wuta, ko ruwa don yă kashe shi. Amma in za ka iya yin wani abu, ka ji tausayinmu ka taimake mu.”

23Yesu ya ce, “ ‘In za ka iya’? Ai, kome mai yiwuwa ne ga wanda ya gaskata.”

24Nan da nan mahaifin yaron ya faɗa da ƙarfi ya ce, “Na gaskata, ka taimake ni in sha kan rashin bangaskiyata!”

25Da Yesu ya ga taron suna zuwa can a guje, sai ya tsawata wa mugun ruhun ya ce, “Kai ruhun kurma, da na bebe, na umarce ka, ka fita daga cikinsa, kada kuma ka ƙara shigarsa.”

26Sai ruhun ya yi ihu, ya buge shi da ƙarfi da farfaɗiya, ya fita. Yaron ya kwanta kamar matacce, har mutane da yawa suka ce, “Ai, ya mutu.” 27Amma Yesu ya kama shi a hannu ya ɗaga, ya kuwa tashi tsaye.

28Da Yesu ya shiga gida, almajiransa suka tambaye shi a ɓoye, suka ce, “Me ya sa ba mu iya fitar da shi ba?”

29Ya amsa ya ce, “Sai da addu’a9.29 Waɗansu rubuce-rubucen hannu suna da addu’a da azumi kaɗai irin wannan yakan fita.”

30Suka bar wurin suka bi ta Galili. Yesu bai so wani yă san inda suke ba, 31gama yana koya wa almajiransa. Ya ce musu, “Za a ci amanar Ɗan Mutum, a ba da shi ga hannun mutane. Za su kashe shi, bayan kwana uku kuma zai tashi.” 32Amma ba su fahimci abin da yake nufi ba, suka kuma ji tsoro su tambaye shi game da wannan.

Wane ne mafi girma?

(Mattiyu 18.1-5; Luka 9.46-48)

33Suka iso Kafarnahum. Da yana cikin gida, sai ya tambaye su ya ce, “Gardamar me kuke yi a hanya?” 34Amma suka yi shiru, don a hanya suna gardama ne, a kan ko wane ne a cikinsu ya fi girma?

35Da Yesu ya zauna, sai ya kira Sha Biyun ya ce, “In wani yana so yă zama na fari, dole yă zama na ƙarshe duka, da kuma bawan kowa.”

36Ya ɗauki wani ƙaramin yaro ya sa yă tsaya a tsakiyarsu. Ya ɗauke shi a hannunsa, ya ce musu, 37“Duk wanda ya karɓi ɗaya daga cikin waɗannan ƙananan yara a cikin sunana, ni ya karɓa. Duk wanda kuma ya karɓe ni, ba ni ya karɓa ba, amma wanda ya aiko ni ne ya karɓa.”

Wanda ba ya gāba da mu, namu ne

(Luka 9.49,50)

38Yohanna ya ce, “Malam mun ga wani mutum yana fitar da aljanu a cikin sunanka, sai muka ce yă daina, domin shi ba ɗaya daga cikinmu ba ne.”

39Yesu ya ce, “Kada ku hana shi. Ba wanda yake yin ayyukan banmamaki a cikin sunana, nan take yă faɗi wani abu mummuna game da ni. 40Gama duk wanda ba ya gāba da mu, namu ne. 41Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ya ba ku ruwan sha a sunana, saboda ku na Kiristi ne, lalle, ba zai rasa ladarsa ba.

Sanadin yin zunubi

(Mattiyu 18.6-9; Luka 17.1,2)

42“Idan kuma wani yă sa ɗaya daga cikin waɗannan ’yan yara masu gaskatawa da ni yă yi laifi, zai fiye masa a rataya wani babban dutsen niƙa a wuyarsa, a jefa shi cikin teku. 43In hannunka yana sa ka yin zunubi, yanke shi. Ai, gwamma ka shiga rai da hannu ɗaya, da ka shiga jahannama ta wuta, inda ba a iya kashe wutar ba, da hannuwanka biyu.9.43 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā suna da fita, 44 inda “tsutsotsi masu cinsu ba sa mutuwa, wutar kuma ba a kashe ta.” 45In kuma ƙafarka tana sa ka yin zunubi, yanke ta. Ai, gwamma ka shiga rai da ƙafa ɗaya, da a jefa ka cikin jahannama ta wuta, da ƙafafunka biyu.9.45 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā suna da lahira, 46 inda “tsutsotsi masu cinsu ba sa mutuwa, wutar kuma ba a kashe ta.” 47In kuma idonka yana sa ka zunubi, ƙwaƙule shi. Ai, gwamma ka shiga mulkin Allah da ido ɗaya, da a jefa ka cikin jahannama ta wuta, da idanu biyu, 48inda

“ ‘tsutsotsinsu ba sa mutuwa,

wutar kuma ba a iya kashewa.’9.48 Ish 66.24

49Za a tsarkake kowa da wuta.

50“Gishiri yana da daɗi, amma in ya rabu da ɗanɗanonsa, ta yaya za a sāke mai da ɗanɗanonsa? Ku kasance da gishiri a cikinku, ku kuma yi zauna lafiya da juna.”