Efezským 4 – SNC & HCB

Slovo na cestu

Efezským 4:1-32

Kristův dar věřícím: rozličné schopnosti pro budování církve

1-2Prosím vás tedy ze svého vězení: žijte a jednejte způsobem důstojným lidí povolaných k tak slavné budoucnosti. Buďte pokorní a mírní, trpěliví a shovívaví k sobě navzájem. 3Za všech okolností pozorně zkoumejte, co vám napovídá Boží Duch. Tak se vyhnete třenicím. 4Všichni patříme k jednomu tělu a jsme vedeni týmž společným Duchem k jediné slavné budoucnosti. 5Máme jednoho Pána, jednu víru, jeden křest; 6máme jednoho Boha Otce nad sebou a v sobě a vše, co máme a jsme, je od něho.

7Každému z nás dal Kristus ze své bohaté zásoby zvláštních schopností právě tolik, kolik uznal za potřebné.

8Tak promluvil prorocky o Kristu již David: Když se po svém vzkříšení a vítězství nad satanem triumfálně vrátil do nebe, obdaroval lidi skvělými dary. 9Všimněte si, že je tu řeč o návratu. To znamená, že musela předcházet cesta opačným směrem, z nebeských výšin do nejhlubších končin země. 10Ten, kdo sestoupil dolů, je tentýž, kdo vystoupil vzhůru, aby naplnil celý vesmír.

Církev není pouhá organizace, ale živý organismus

11Tak jsme se někteří stali apoštoly, jiní dostali dar výřečnosti; někdo má schopnost úspěšně získávat lidi pro Krista, další umí pečovat o jejich potřeby, tak jako se pastýř stará o své ovce, a jiný zase dovede dobře vyučovat. 12Jejich úkolem je připravovat věřící ke službě, aby církev zdravě prospívala, 13abychom ve své víře a vztahu k Božímu Synu postupně dosáhli stejné úrovně, plné lidské zralosti, dokonalého naplnění Kristem.

14Pak už nebudeme jako malé děti podléhat kdejakému módnímu názoru svého okolí, jeho falši a prohnaným svodům. 15Místo toho se budeme vždy s láskou držet pravdy, opravdově mluvit, jednat a žít a tak budeme stále podobnější Kristu, který je naší hlavou. 16Z něho roste dokonale skloubené tělo a každá jeho část slouží svým způsobem všem ostatním, aby tělo zdravě rostlo a žilo v lásce.

Kristus vede k novému životu

17Rád bych vám proto předložil Kristovým jménem tuto výzvu: nežijte už jako ti, kteří neznají Boží vůli. 18Jejich myšlení je zavádí 19a v jejich srdci je tma, protože o Bohu nechtějí nic vědět. Takoví nepoznali pravý život. Mezi zlým a dobrým nevidí rozdíl a vrhají se do prostopášností. Před ničím se nezastaví, tak je ženou vášně a chamtivost. Ale Kristus nás učí něco docela jiného! 20-21Pokud jste opravdu slyšeli jeho hlas a poznali v něm pravdu, 22je vám jistě jasné, že musíte odhodit svůj dřívější způsob života – honbu za požitkem vlastního zkaženého „já“, na jejímž konci číhá záhuba – 23a stále znovu nechat provětrávat své srdce Božím vanutím. 24Ano, musíte se stávat novými odlišnými osobnostmi, dobrými a svatými, které zrcadlí Boží tvář.

25Nechte tedy lhaní a říkejte si navzájem pravdu, patříte přece všichni k sobě jako údy v jednom těle. 26Někdy je těžké ubránit se hněvu, ale nehřešte tím, že byste ho v sobě rozdmýchávali. Když vás už někdo rozzlobil, nechoďte s tou zlostí spát; 27nezahrávejte si s ďáblem.

28Kdo kradl, ať toho hned nechá a přiloží ruce k pořádné práci, aby měl čím přispět potřebnějším. 29Nevypusťte z úst žádnou jedovatost. Hleďte raději, aby vaše slova byla každému v pravou chvíli pomocí a povzbuzením. 30Nezbavujte se svým jednáním Ducha svatého, kterého vám dal Bůh. Nemáte jinou propustku pro vstup do nebeského domova.

31Pryč s tvrdostí, náladovostí a vznětlivostí. Hádky, urážky a jízlivost ať jsou vám naprosto cizí. 32Buďte k sobě navzájem laskaví a shovívaví a odpouštějte si, jako vám odpustil Bůh kvůli Kristu.

Hausa Contemporary Bible

Afisawa 4:1-32

Tarayya a cikin jikin Kiristi

1A matsayina na ɗan kurkuku saboda Ubangiji, ina roƙonku ku yi rayuwar da ta dace da kiran da aka yi muku. 2Kullum ku kasance masu sauƙinkai da kuma hankali; ku zama masu haƙuri, kuna jimrewa da juna cikin ƙauna. 3Ku yi ƙoƙari sosai ku kiyaye zaman ɗayan nan da Ruhu ya ba ku, ku yi haka ta wurin zaman lafiya da juna. 4Dukanku jiki ɗaya ne, kuna kuma da Ruhu guda. An ba ku bege guda sa’ad da aka kira ku. 5Ubangiji ɗaya, bangaskiya ɗaya, baftisma kuma ɗaya, 6Allah ɗaya Uban duka, wanda yake a bisa duka, ta wurin duka, a cikin duka kuma.

7Amma ga kowannenmu an ba da alheri bisa ga yadda Kiristi ya rarraba. 8Shi ya sa aka4.8 Ko kuwa Allah ce,

“Sa’ad da ya hau sama,

ya bi da kamammu kamar tawagarsa

ya kuma ba da baye-baye ga mutane.”4.8 Zab 68.18

9(Me ake nufin da “ya hau,” in ba cewa dā ya sauka can ƙarƙashin ƙasa ba? 10Shi wannan da ya sauka ɗin, shi ne kuma ya hau zuwa can sama, kai, gaba da sammai, don mulkinsa yă cika duniya gaba ɗaya.) 11Saboda haka Kiristi kansa ya ba wa waɗansu baiwa su zama manzanni, waɗansu su zama annabawa, waɗansu su zama masu wa’azi, waɗansu kuma su zama fastoci, da kuma malamai. 12Ya yi haka don yă shirya mutanensa saboda ayyukan hidima, don a gina jikin Kiristi. 13Wannan zai ci gaba har sai mun zama ɗaya a cikin bangaskiya da kuma ta wurin fahimtarmu na Ɗan Allah. Sa’an nan za mu zama balagaggu, kamar yadda Kiristi yake, mu kuma zama gaba ɗaya cikakku kamar sa.

14An yi wannan kuwa don kada mu koma zama kamar yara, muna ta canja zukatanmu game da abin da muka gaskata don kawai wani ya faɗa mana wani abu dabam, ko domin wani ya yi wayo ya ruɗe mu, ya sa ƙarya ta zama kamar gaskiya. 15Ya kamata kullum ƙauna tă sa mu faɗa gaskiya. Ta haka za mu yi girma a kowace hanya, mu kuma zama kamar Kiristi, wanda yake kan 16dukan jiki. Shi ne ya haɗe jiki duka, ya kuma sa dukan gaɓoɓin jiki suna aiki daidai, yayinda kowace gaɓa take aikinta cikin ƙauna.

Yin rayuwa kamar ’ya’yan haske

17To, ina dai faɗa muku, ina kuma nace faɗa muku a cikin Ubangiji, cewa kada ku ci gaba da yin rayuwa kamar yadda Al’ummai suke yi, masu banzan tunani. 18Suna a cikin duhu a fahimtarsu, kuma a rabe suke daga ran Allah saboda jahilcin da yake cikinsu ta dalilin taurarewar zukatansu. 19Ba sa damu da wani abu ko mai kyau ko marar kyau. Rayukansu sun cika da kowace irin ƙazanta da haɗama.

20Amma ba abin da aka koya muku ke nan ba sa’ad da kuka zo ga sanin Kiristi. 21Da yake kun ji duka game da shi, kuka kuma koyi gaskiyar da take cikin Yesu, 22sai ku tuɓe tsohon mutumin nan naku da kuma rayuwarku ta dā, wadda take lalacewa saboda sha’awace-sha’awacen da suke ruɗe ku. 23A maimakon haka, bari Ruhu yă sabunta tunaninku da kuma halayenku. 24Ku sanya sabon halin nan da aka halitta bisa ga kamannin Allah, halin nan kuwa, yă bayyana cikin adalci, da zaman tsarki.

25Saboda haka dole kowannenku yă bar yin ƙarya, yă kuma riƙa faɗa wa maƙwabcinsa gaskiya, gama dukanmu gaɓoɓi jiki ɗaya ne. 26“Cikin fushinku kada ku yi zunubi.”4.26 Zab 4.4 Kada ku bar rana ta fāɗi kuna fushi, 27kada kuma ku ba wa Iblis dama. 28Duk wanda yake sata, sai yă daina sata, dole kuma yă yi aiki, yă yi wani abu mai amfani da hannuwansa, don yă sami abin da zai iya raba da masu bukata.

29Kada wata ƙazamar magana ta fita daga bakunanku, sai dai abin da yake da amfani don gina waɗansu bisa ga bukatunsu. Ta haka maganarku za tă zama da amfani ga masu jinta. 30Kada kuma ku ɓata wa Ruhu Mai Tsarki na Allah rai, wanda da shi aka hatimce ku da shi don ranar fansa. 31Ku rabu da kowane irin ɗacin rai, haushi da hasala, faɗa da ɓata suna, ku rabu da kowace irin ƙeta. 32Ku yi alheri, ku kuma ji tausayin juna, kuna gafarta wa juna, kamar yadda a cikin Kiristi, Allah ya gafarta muku.