Židům 6 – SNC & HCB

Slovo na cestu

Židům 6:1-20

Růst v poznání Krista je nutný

1Přestaňme stále jenom ohledávat základy Kristova učení a usilujme postoupit dále. Nevracejme se pořád jenom k lítosti nad nesprávným jednáním, k víře v Boha, 2k učení o křtu, ke vkládání rukou, k učení o vzkříšení mrtvých a o věčném odsouzení. 3Když Bůh dovolí, postupme k dalším věcem.

4-5Ten, kdo byl jednou osvícen, okusil Božího daru, získal podíl na Duchu svatém, poznal, jak vážná je Boží věc, zakusil moc přicházejícího světa, 6a potom od Boha odpadl, nemůže se vrátit zpátky, protože veřejně potupil a znovu ukřižoval Božího Syna.

7Země, která je často skrápěna deštěm a vydává těm, kdo ji obdělávají, hojnou úrodu, přijímá od Boha požehnání. 8Plodí-li však bodláky a trní, není vhodná k obdělávání, bude vypálena a ponechána svému osudu.

9I když říkám takové věci, milovaní, nemyslím, že by se týkaly vás. Jsem přesvědčen, že přinášíte dobré plody a spočíváte v Boží ochraně. 10Bůh je spravedlivý, nezapomíná na vaši práci a věrnost jeho věci, na vaši minulou i přítomnou službu, kterou prokazujete těm, kteří jsou mu cele oddáni. 11Napomínám každého z vás k horlivosti. Nebuďte leniví a zachovejte si až do konce plnou naději. 12Nebuďte tupí. Řiďte se příkladem těch, kteří vírou a trpělivostí dosáhli splnění Božích slibů.

Boží jisté sliby nám dávají naději

13-14Bůh dal Abrahamovi slib a chtěl ho potvrdit přísahou. A protože nemohl přísahat při nikom větším, přísahal při sobě, že bude Abrahama provázet svou přízní a že rozmnoží jeho rod. 15A Abraham svou trpělivostí skutečně dosáhl splnění tohoto slibu.

16Když se lidé přísahou dovolávají někoho mocnějšího, ukončují tím svůj spor. 17Bůh dědicům zaslíbení svou přísahou nepochybně prokázal nezměnitelnost své vůle. 18Protože je vyloučeno, aby Bůh lhal, můžeme se tedy neochvějně opírat jak o jeho slib, tak o jeho přísahu. Když jsme se k němu uchýlili, smíme čerpat mocné potěšení z nabízené naděje, které jsme se chopili. 19Je to bezpečná a pevná kotva celé naší bytosti, která nás spojuje s Bohem, 20k němuž nás předešel Ježíš, který se stal navždycky knězem podle řádu Malkísedekova. Malkísedek je předobrazem Božího Syna, který je knězem navždycky.

Hausa Contemporary Bible

Ibraniyawa 6:1-20

1Dole mu yi ƙoƙarin zama balagaggu mu kuma fara tunani game da abubuwan da suka fi koyarwan nan mai sauƙi game da Kiristi. Bai kamata mu ci gaba da magana game da me ya sa dole mu juye daga ayyukan da suke kawo mutuwa da kuma me ya sa za mu kasance da bangaskiya a cikin Allah ba. 2Kuma bai kamata mu ci gaba da koyar da umarnai game da baftisma, ɗibiya hannuwa, tashin matattu, da kuma madawwamin hukunci ba. 3Da yardar Allah, za mu ci gaba ga ƙarin ganewa.

4Waɗanda suka taɓa samun haske, waɗanda suka ɗanɗana kyauta ta sama, waɗanda suka sami rabo cikin Ruhu Mai Tsarki, 5waɗanda suka ɗanɗana daɗin maganar Allah da kuma ikokin zamani mai zuwa, 6ba ya yiwuwa a sāke kawo su ga tuba in suka kauce, domin suna sāke gicciye Ɗan Allah ke nan suna kuma kunyata shi a gaban jama’a. 7Ƙasar da take shan ruwan sama da yake fāɗi a kanta kullum da kuma take ba da hatsin da yake da amfani ga waɗanda ake noma dominsu, takan sami albarkar Allah. 8Amma ƙasar da take ba da ƙaya da sarƙaƙƙiya ba ta da amfani tana kuma cikin hatsarin la’ana. A ƙarshe za a ƙone ta.

9Abokaina, ko da yake muna irin maganan nan, mun tabbata kuna yi abubuwan nan masu kyau da waɗanda suka sami ceto suke yi. 10Allah ba marar adalci ba ne. Ba zai manta da aikinku da kuma ƙaunar da kuka nuna masa wajen taimakon mutanensa da kuma ci gaba da taimakonsu da kuke yi ba. 11Muna so kowannenku yă nuna ƙwazon nan har zuwa ƙarshe, domin ku tabbatar da begenku. 12Ba ma so ku zama masu ƙyuya, sai dai ku yi koyi da waɗanda ta wurin bangaskiya da haƙuri suka gāji abin da aka yi alkawari.

Alkawarin Allah tabbatacce ne

13Babu wanda ya fi Allah, saboda haka sa’ad da ya yi alkawari ga Ibrahim, sai ya rantse da sunansa, 14cewa, “Tabbatacce zan albarkace ka in kuma ba ka zuriya mai yawa.”6.14 Far 22.17 15Haka kuwa bayan Ibrahim ya jira da haƙuri, sai ya karɓi abin da aka yi alkawari.

16In mutane za su yi rantsuwa sukan yi haka da wanda ya fi su ne, rantsuwar kuwa takan tabbatar da abin da aka faɗa ta kuma kawo ƙarshen dukan gardama. 17Saboda haka da Allah ya so yă bayyana nufinsa marar canjawa a sarari ga magādan abin da aka yi alkawari, sai ya tabbatar da shi da rantsuwa. 18Allah ba ya karya! Haka ma alkawuransa da rantsuwarsa abubuwa biyu ne da ba a iya canjawa. Mun gudu zuwa wurin Allah domin kāriya. Ya kamata alkawuransa su ƙarfafawa sosai mu riƙe begen nan da yake gabanmu. 19Muna da wannan bege kamar anka na rai, kafaffe da kuma tabbatacce. Yana shiga tsattsarkan wuri na can ciki a bayan labule, 20inda Yesu, wanda ya sha gabanmu, ya shiga a madadinmu. Ya zama babban firist na har abada, bisa ga tsarin Melkizedek.