2 Timoteo 2 – NVI & HCB

Nueva Versión Internacional

2 Timoteo 2:1-26

1Así que tú, hijo mío, fortalécete por la gracia que tenemos en Cristo Jesús. 2Lo que me has oído decir en presencia de muchos testigos, encomiéndalo a creyentes dignos de confianza, que a su vez estén capacitados para enseñar a otros. 3Comparte nuestros sufrimientos, como buen soldado de Cristo Jesús. 4Ningún soldado que quiera agradar a su superior se enreda en cuestiones civiles. 5Así mismo, el atleta no recibe la corona de vencedor si no compite según el reglamento. 6El labrador que trabaja duro tiene derecho a recibir primero parte de la cosecha. 7Reflexiona en lo que te digo y el Señor te dará una mayor comprensión de todo esto.

8No dejes de recordar a Jesucristo, descendiente de David, levantado de entre los muertos. Este es mi evangelio, 9por el que sufro al extremo de llevar cadenas como un criminal. Pero la palabra de Dios no está encadenada. 10Así que todo lo soporto por el bien de los elegidos, para que también ellos alcancen la gloriosa y eterna salvación que tenemos en Cristo Jesús.

11Este mensaje es digno de crédito:

Si morimos con él,

también viviremos con él;

12si resistimos,

también reinaremos con él.

Si lo negamos,

también él nos negará;

13si somos infieles,

él sigue siendo fiel,

ya que no puede negarse a sí mismo.

Un obrero aprobado por Dios

14No dejes de recordarles esto. Adviérteles delante de Dios que eviten las discusiones inútiles, pues no sirven nada más que para destruir a los oyentes. 15Esfuérzate por presentarte a Dios aprobado, como obrero que no tiene de qué avergonzarse y que interpreta rectamente la palabra de verdad. 16Evita las discusiones profanas, porque los que se dan a ellas se alejan cada vez más de la vida piadosa, 17y sus palabras se extienden como gangrena. Entre ellos están Himeneo y Fileto, 18que se han desviado de la verdad. Andan diciendo que la resurrección ya tuvo lugar y así trastornan la fe de algunos. 19A pesar de todo, el fundamento de Dios es sólido y se mantiene firme, pues está sellado con esta inscripción: «El Señor conoce a los suyos»,2:19 Nm 16:5, según LXX. y esta otra: «Que se aparte de la maldad todo el que invoca el nombre del Señor».2:19 Véase Jl 3:5.

20En una casa grande no solo hay vasos de oro y de plata, sino también de madera y de barro, unos para usos especiales y otros para fines ordinarios. 21Si alguien se mantiene limpio, llegará a ser un vaso noble, santificado, útil para el Señor y preparado para toda obra buena.

22Huye de las malas pasiones de la juventud y esmérate en seguir la justicia, la fe, el amor y la paz, junto con los que invocan al Señor con un corazón limpio. 23No tengas nada que ver con discusiones necias y sin sentido, pues ya sabes que terminan en pleitos. 24Y un siervo del Señor no debe andar peleando; más bien, debe ser amable con todos, capaz de enseñar y no propenso a irritarse. 25Así, humildemente, debe corregir a los adversarios, con la esperanza de que Dios les conceda el arrepentimiento para conocer la verdad, 26de modo que se despierten y escapen de la trampa en que el diablo los tiene cautivos, sumisos a su voluntad.

Hausa Contemporary Bible

2 Timoti 2:1-26

1Kai kuma, ɗana, ka yi ƙarfi cikin alherin da yake cikin Kiristi Yesu. 2Abubuwan da ka ji na faɗa a gaban shaidu masu yawa kuwa ka danƙa wa amintattun mutane waɗanda su ma za su iya koya wa waɗansu. 3Ka jure wa shan wahala tare da mu kamar soja mai kyau na Kiristi Yesu. 4Ba wanda yake aikin soja da zai sa kansa a sha’anin mutumin da ba ya aikin soja, domin yakan so yă gamshi wanda ya ɗauke shi soja. 5Haka ma, in wani ya yi gasa a matsayi shi ɗan wasa ne, ba ya sami rawanin nasara, sai in ya yi gasar bisa ga dokoki. 6Manomi mai aiki sosai ya kamata yă zama na fari wajen samun rabon amfanin gona. 7Ka yi tunani a kan abin da nake faɗi, gama Ubangiji zai ba ka ganewa cikin dukan wannan.

8Ka tuna da Yesu Kiristi, wanda aka tā da shi daga matattu, zuriyar Dawuda, wanda shi ne bisharata, 9wadda nake shan wahala har ga daurin sarƙa kamar mai laifi. Amma Maganar Allah ba a daure take ba. 10Saboda haka nake jure kome saboda zaɓaɓɓu, domin su ma su sami ceton da yake cikin Kiristi Yesu, tare da madawwamiyar ɗaukaka.

11Ga wata magana tabbatacciya,

“In muka mutu tare da shi,

za mu rayu tare da shi;

12in muka jimre,

za mu yi mulki tare da shi.

In muka yi mūsunsa,

shi ma zai yi mūsunmu;

13in ba mu da aminci,

shi dai mai aminci ne,

domin shi ba zai iya mūsun kansa ba.”

Ma’aikacin da Allah ya amince

14Ka riƙa tuna masu da haka, ka kuma gama su da Allah, kada su yi jayayya a kan maganganu, don ba ta da wani amfani, sai ɓad da masu ji kawai take yi. 15Ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka gabatar da kanka a gaban Allah a matsayin wanda aka amince da shi, ma’aikaci wanda ba shi da dalilin jin kunya wanda kuma yake fassara kalmar gaskiya daidai. 16Ka yi nesa da maganganun banza na rashin tsoron Allah, gama waɗanda suka mai da hankali ga yin waɗannan za su ƙara zama marasa tsoron Allah. 17Koyarwarsu za tă bazu kamar ruɓaɓɓen gyambo. A cikinsu akwai Himenayus da Filetus, 18waɗanda suka bauɗe daga gaskiya. Suna cewa tashin matattu ya riga ya faru, suna kuma ɓata bangaskiyar waɗansu. 19Duk da haka, ƙaƙƙarfan tushen nan na Allah yana nan daram, an hatimce shi da wannan rubutu, “Ubangiji ya san waɗanda suke nasa,”2.19 Ƙid 16.5 (dubi Seftuwajin) da kuma, “Duk wanda ya bayyana yarda ga sunan Ubangiji, to, dole yă yi nesa da aikata mugunta.”

20A babban gida akwai kayayyakin da ba na zinariya da na azurfa kaɗai ba, amma har da na katako da na yumɓu ma; waɗansu domin hidima mai daraja waɗansu kuwa domin hidima marar daraja. 21In mutum ya tsabtacce kansa daga na farkon zai zama kayan aikin hidima mai daraja, mai amfani ga Maigida, kuma shiryayye domin yin kowane aiki mai kyau.

22Ka yi nesa da mugayen sha’awace-sha’awace na ƙuruciya, ka kuma bi adalci, bangaskiya, ƙauna da kuma salama, tare da waɗanda suke kira ga Ubangiji daga zuciya mai tsabta. 23Kada wani abu yă haɗa ka da gardandamin banza da wofi, domin ka san yadda suke jawo faɗa. 24Bai kamata bawan Ubangiji yă zama mai neman faɗa ba; a maimako, dole yă nuna alheri ga kowa, mai iya koyarwa, mai haƙuri kuma. 25Waɗanda suke gāba da shi kuwa dole yă yi musu gargaɗi cikin hankali, da fata Allah zai sa su tuba su kai ga sanin gaskiya, 26su kuma dawo cikin hankulansu su kuɓuta daga tarkon Iblis, wanda ya sa suka zama kamammu don su aikata nufinsa.