1 Corintios 8 – NVI & HCB

Nueva Versión Internacional

1 Corintios 8:1-13

Lo sacrificado a los ídolos

1En cuanto a lo sacrificado a los ídolos, es cierto que todos tenemos conocimiento. El conocimiento trae orgullo, mientras que el amor edifica. 2El que cree que sabe algo, todavía no sabe como debiera saber. 3Pero el que ama a Dios es conocido por él.

4De modo que, en cuanto a comer lo sacrificado a los ídolos, sabemos que un ídolo no tiene ningún valor en este mundo y que hay un solo Dios. 5Aunque haya los así llamados dioses, en el cielo o en la tierra (y por cierto que hay muchos «dioses» y muchos «señores»), 6para nosotros no hay más que un solo Dios, el Padre, de quien todo procede y para el cual vivimos; y no hay más que un solo Señor, Jesucristo, por quien todo existe y por medio del cual vivimos.

7Pero no todos tienen conocimiento de esto. Algunos siguen tan acostumbrados a los ídolos que, cuando comen carne a sabiendas de que ha sido sacrificada a un ídolo, su conciencia se contamina por ser débil. 8Pero lo que comemos no nos acerca a Dios; no somos peores por no comer ni mejores por comer.

9Sin embargo, tengan cuidado de que su libertad no se convierta en motivo de tropiezo para los débiles. 10Porque, si alguien de conciencia débil te ve a ti, que tienes este conocimiento, comer en el templo de un ídolo, ¿no se sentirá animado a comer lo que ha sido sacrificado a los ídolos? 11Entonces ese hermano débil, por quien Cristo murió, se perderá a causa de tu conocimiento. 12Al pecar así contra los hermanos, hiriendo su débil conciencia, pecan ustedes contra Cristo. 13Por lo tanto, si la comida va a hacer pecar a mi hermano, no comeré carne jamás, para no hacerlo caer en pecado.

Hausa Contemporary Bible

1 Korintiyawa 8:1-13

Abincin da aka miƙa wa gumaka

1To, game da abincin da aka miƙa hadaya ga gumaka kuwa. Mun san cewa dukanmu muna da ilimi. Ilimi yakan kawo girman kai, amma ƙauna takan gina. 2Mutumin da yake tsammani ya san abu, sanin da yake da shi bai isa ba. 3Amma mutumin da yake ƙaunar Allah, Allah yana sane da shi.

4To, game da cin abincin da aka miƙa hadaya ga gumaka kuwa, mun san cewa “Gunki ba kome ba ne a duniya”, kuma “Babu wani Allah sai dai ɗaya.” 5Gama ko da akwai abubuwan da ake ce da su alloli, a sama ko a ƙasa (don kuwa akwai “alloli” da “iyayengiji” da yawa), 6duk da haka a gare mu dai akwai Allah ɗaya kaɗai, Uba, wanda dukan abubuwa suke daga gare shi, wanda kuma saboda shi ne muke rayuwa, kuma akwai Ubangiji ɗaya, Yesu Kiristi, wanda ta wurinsa ne aka yi dukan abu, ta wurinsa ne kuma muke rayuwa.

7Amma ba kowa ne ya san wannan ba. Har yanzu, waɗansu mutane sun saba da tunani cewa gumaka ainihi ne, saboda haka sa’ad da suka ci irin abincin nan, sukan ɗauka cewa kamar an miƙa wa ga gunki ne, kuma da yake lamirinsu ba ƙarfi, yakan ƙazantu. 8Gaskiya ne cewa ba ma samun yardar Allah ta wurin abin da muke ci. Ba ma rasa wani abu idan ba mu ci ba, kuma ba ma ƙaru da wani abu in muka ci.

9Sai dai ku yi hankali, kada yin amfani da ’yancinku yă zama abin sa tuntuɓe ga marasa ƙarfi. 10Gama in wani wanda lamirinsa ba shi da ƙarfi ya gan ka, kai da kake da wannan sani, kana ci a haikalin gumaka, ashe, ba zai sami ƙarfin halin cin abin da aka miƙa wa gumaka ba? 11Saboda haka ta wurin sanin nan naka sai ka sa wannan ɗan’uwa marar ƙarfi wanda Kiristi ya mutu dominsa yă hallaka. 12Sa’ad da ka rushe lamiri mai bi marar ƙarfi, ka yi wa Kiristi zunubi ke nan. 13Saboda haka, in abin da nake ci zai sa ɗan’uwana yă yi zunubi, ba zan ƙara cin nama ba, don kada in sa shi yă yi tuntuɓe.