2 ጢሞቴዎስ 4 – NASV & HCB

New Amharic Standard Version

2 ጢሞቴዎስ 4:1-22

1በእግዚአብሔር ፊት እንዲሁም በሕያዋንና በሙታን ሊፈርድ ባለው በክርስቶስ ኢየሱስ ፊት፣ መገለጡንና መንግሥቱን በማሰብ ይህን ዐደራ እልሃለሁ፤ 2ቃሉን ስበክ፤ ጊዜው ቢመችም ባይመችም ዝግጁ ሁን፤ በታላቅ ትዕግሥትና በማስተማር አቅና፤ ገሥጽ፤ አበረታታም። 3ምክንያቱም ሰዎች ትክክለኛ የሆነውን ትምህርት የማይቀበሉበት ጊዜ ይመጣል፤ ከዚህ ይልቅ ለገዛ ምኞቶቻቸው የሚስማማውን፣ የሚያሳክክ ጆሯቸው ሊሰማ የሚፈልገውን እንዲነግሯቸው በዙሪያቸው ብዙ አስተማሪዎችን ይሰበስባሉ። 4እውነትን ከመስማት ጆሯቸውን ይመልሳሉ፤ ወደ ተረትም ዘወር ይላሉ። 5አንተ ግን በሁኔታዎች ሁሉ የረጋህ ሁን፤ መከራን ታገሥ፤ የወንጌል ሰባኪን ተግባር አከናውን፤ አገልግሎትህን ፈጽም።

6እኔ እንደ መጠጥ ቍርባን መሥዋዕት ለመፍሰስ ተቃርቤአለሁ፤ ተለይቼ የምሄድበትም ጊዜ ደርሷል። 7መልካሙን ገድል ተጋድያለሁ፤ ሩጫውን ጨርሻለሁ፤ ሃይማኖትንም ጠብቄአለሁ። 8ወደ ፊት የጽድቅ አክሊል ተዘጋጅቶልኛል፤ ይህንም ጻድቅ ፈራጅ የሆነው ጌታ በዚያ ቀን ለእኔ ይሰጠኛል፤ ደግሞም ለእኔ ብቻ ሳይሆን፣ የእርሱን መገለጥ ለናፈቁ ሁሉ ነው።

የጳውሎስ ማሳሰቢያ

9በቶሎ ወደ እኔ ለመምጣት የተቻለህን ሁሉ አድርግ፤ 10ዴማስ ይህን ዓለም ወድዶ፣ ትቶኝ ወደ ተሰሎንቄ ሄዷልና። ቄርቂስ ወደ ገላትያ፣ ቲቶ ወደ ድልማጥያ ሄደዋል፤ 11ከእኔ ጋር ያለው ሉቃስ ብቻ ነው። ማርቆስ በአገልግሎቴ ስለሚረዳኝ ከአንተ ጋር ይዘኸው ና። 12ቲኪቆስን ወደ ኤፌሶን ልኬዋለሁ። 13ስትመጣ በጢሮአዳ ከአክርጳ ዘንድ የተውሁትን በርኖስ፣ ጥቅልል መጻሕፍቱን፣ በተለይም የብራና መጻሕፍቱን አምጣልኝ።

14አንጥረኛው እስክንድሮስ ብዙ ጕዳት አድርሶብኛል፤ ጌታ ግን የእጁን ይሰጠዋል። 15መልእክታችንን እጅግ ተቃውሟልና፣ አንተም ከእርሱ ተጠንቀቅ።

16በተከሰስሁበት ነገር የመጀመሪያ መከላከያዬን ሳቀርብ ማንም ሊያግዘኝ አልመጣም፤ ነገር ግን ሁሉ ትተውኝ ሄዱ። ይህንም አይቍጠርባቸው። 17ነገር ግን መልእክቱ በእኔ አማካይነት በሙላት እንዲሰበክና አሕዛብ ሁሉ እንዲሰሙት ጌታ በአጠገቤ ቆሞ አበረታኝ፤ ከአንበሳም መንጋጋ አዳነኝ። 18ጌታ ከክፉ ነገር ሁሉ ያድነኛል፤ ወደ ሰማያዊው መንግሥቱም በሰላም ያደርሰኛል፤ ለእርሱ ከዘላለም እስከ ዘላለም ክብር ይሁን፤ አሜን።

የስንብት ሰላምታ

19ለጵርስቅላና4፥19 ግሪኩ ጵርስቃ ይላል። ለአቂላ፣ ለሄኔሲፎሩም ቤተ ሰዎች ሰላምታ አቅርብልኝ።

20ኤርስጦስ በቆሮንቶስ ቀርቷል፤ ጥሮፊሞስም ስለ ታመመ በሚሊጢን ትቼዋለሁ። 21ከክረምት በፊት እዚህ ለመምጣት የተቻለህን አድርግ።

ኤውግሎስና ጱዴስ እንዲሁም ሊኖስ፣ ቅላውዲያና ወንድሞች ሁሉ ሰላምታ ያቀርቡልሃል።

22ጌታ ከመንፈስህ ጋር ይሁን። ጸጋ ከእናንተ ጋር ይሁን።

Hausa Contemporary Bible

2 Timoti 4:1-22

1A gaban Allah da kuma Kiristi Yesu, wanda zai yi wa masu rai da matattu shari’a, saboda kuma bayyanuwarsa da mulkinsa, ina ba ka umarni. 2Ka yi wa’azin Maganar Allah, ka zama a shirye a kullum, ko da zarafi, ko babu zarafi, ka yi gyara, ka kwaɓe, ka kuma ƙarfafa, da matuƙar haƙuri da koyarwa cikin natsuwa. 3Gama lokaci yana zuwa da mutane ba za su jure da sahihiyar koyarwa ba. A maimako, don cimma burinsu, za su taro wa kansu malamai masu yawa, domin su faɗi abin da kunnuwansu masu ƙaiƙayi suke so su ji. 4Za su juye kunnuwansu daga gaskiya zuwa ga jin tatsuniyoyi. 5Amma kai, ka natsu cikin kowane hali, ka jure shan wahala, ka yi aikin mai bishara, ka cika dukan ayyukan hidimarka.

6Gama an riga an tsiyaye ni kamar hadaya ta sha, kuma lokacin tashina ya yi. 7Na yi fama mai kyau, na gama tseren, na riƙe bangaskiya. 8Yanzu kuwa an ajiye mini rawanin adalci, wanda Ubangiji, Alƙali mai adalci zai ba ni a ranan nan ba kuwa ni kaɗai ba, amma ga duk waɗanda suka yi marmarin bayyanuwarsa.

Maganar ƙarshe

9Ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka zo wurina da sauri, 10gama Demas, saboda ƙaunar wannan duniya, ya yashe ni ya tafi Tessalonika. Kirssens ya tafi Galatiya, Titus kuwa ya tafi Dalmatiya. 11Luka ne kaɗai yake tare da ni. Ka nemi Markus ku zo tare, domin yana da amfani a gare ni cikin hidimata. 12Na aiki Tikikus zuwa Afisa. 13Sa’ad da za ka dawo, ka zo mini da alkyabbar da na bari a wurin Karbus a Toruwas, da kuma naɗaɗɗun littattafaina, tun ba ma fatun nan masu rubutu ba.

14Alekzanda maƙerin ƙarafan nan ya yi mini mugunta ƙwarai. Ubangiji zai sāka masa saboda abin da ya yi. 15Kai ma sai ka lura da shi, domin ya yi gāba sosai da saƙonmu.

16A lokacin da na kāre kaina da farko, ba wanda ya goyi bayana, sai ma kowa ya yashe ni. Ina fata ba za a lasafta wannan laifi a kansu ba. 17Amma Ubangiji ya tsaya tare da ni, ya kuma ba ni ƙarfi, don ta wurina a yi cikakkiyar shelar saƙon har Al’ummai duka su ji. Aka kuma cece ni daga bakin zaki. 18Ubangiji zai cece ni daga kowane mugun hari yă kuma kai ni mulkinsa na sama lafiya. A gare shi ɗaukaka ta tabbata har abada abadin. Amin.

Gaisuwa ta ƙarshe

19Ka gai da Firiskila da Akwila da iyalin Onesiforus.

20Erastus ya dakata a Korint, na kuma bar Turofimus cikin rashin lafiya a Miletus. 21Ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka iso nan kafin damina.

Yubulus yana gaishe ka, haka ma Fuden, Lainus, Kalaudiya da kuma dukan ’yan’uwa.

22Ubangiji yă zama tare da ruhunka. Alheri yă zama tare da ku.