Mark 3 – KJV & HCB

King James Version

Mark 3:1-35

1And he entered again into the synagogue; and there was a man there which had a withered hand. 2And they watched him, whether he would heal him on the sabbath day; that they might accuse him. 3And he saith unto the man which had the withered hand, Stand forth. 4And he saith unto them, Is it lawful to do good on the sabbath days, or to do evil? to save life, or to kill? But they held their peace. 5And when he had looked round about on them with anger, being grieved for the hardness of their hearts, he saith unto the man, Stretch forth thine hand. And he stretched it out: and his hand was restored whole as the other. 6And the Pharisees went forth, and straightway took counsel with the Herodians against him, how they might destroy him. 7But Jesus withdrew himself with his disciples to the sea: and a great multitude from Galilee followed him, and from Judæa, 8And from Jerusalem, and from Idumaea, and from beyond Jordan; and they about Tyre and Sidon, a great multitude, when they had heard what great things he did, came unto him. 9And he spake to his disciples, that a small ship should wait on him because of the multitude, lest they should throng him. 10For he had healed many; insomuch that they pressed upon him for to touch him, as many as had plagues. 11And unclean spirits, when they saw him, fell down before him, and cried, saying, Thou art the Son of God. 12And he straitly charged them that they should not make him known. 13And he goeth up into a mountain, and calleth unto him whom he would: and they came unto him. 14And he ordained twelve, that they should be with him, and that he might send them forth to preach, 15And to have power to heal sicknesses, and to cast out devils: 16And Simon he surnamed Peter; 17And James the son of Zebedee, and John the brother of James; and he surnamed them Boanerges, which is, The sons of thunder: 18And Andrew, and Philip, and Bartholomew, and Matthew, and Thomas, and James the son of Alphaeus, and Thaddaeus, and Simon the Canaanite, 19And Judas Iscariot, which also betrayed him: and they went into an house. 20And the multitude cometh together again, so that they could not so much as eat bread. 21And when his friends heard of it, they went out to lay hold on him: for they said, He is beside himself.

22¶ And the scribes which came down from Jerusalem said, He hath Beelzebub, and by the prince of the devils casteth he out devils. 23And he called them unto him, and said unto them in parables, How can Satan cast out Satan? 24And if a kingdom be divided against itself, that kingdom cannot stand. 25And if a house be divided against itself, that house cannot stand. 26And if Satan rise up against himself, and be divided, he cannot stand, but hath an end. 27No man can enter into a strong man’s house, and spoil his goods, except he will first bind the strong man; and then he will spoil his house. 28Verily I say unto you, All sins shall be forgiven unto the sons of men, and blasphemies wherewith soever they shall blaspheme: 29But he that shall blaspheme against the Holy Ghost hath never forgiveness, but is in danger of eternal damnation: 30Because they said, He hath an unclean spirit.

31¶ There came then his brethren and his mother, and, standing without, sent unto him, calling him. 32And the multitude sat about him, and they said unto him, Behold, thy mother and thy brethren without seek for thee. 33And he answered them, saying, Who is my mother, or my brethren? 34And he looked round about on them which sat about him, and said, Behold my mother and my brethren! 35For whosoever shall do the will of God, the same is my brother, and my sister, and mother.

Hausa Contemporary Bible

Markus 3:1-35

(Mattiyu 12.9-14; Luka 6.6-11)

1Wani lokaci, da ya sāke shiga majami’a, sai ga wani mutum mai shanyayyen hannu. 2Waɗansu daga cikin mutane suna neman dalilin zargin Yesu, sai suka zuba masa ido, su ga ko zai warkar da shi a ranar Asabbaci. 3Yesu ya ce wa mutumin mai shanyayyen hannun, “Tashi ka tsaya a gaban kowa.”

4Sai Yesu ya tambaye su ya ce, “Me ya kamata a yi bisa ga doka, a ranar Asabbaci, a aikata alheri, ko a aikata mugunta, a ceci rai, ko a yi kisa?” Amma suka yi shiru.

5Sai ya kalle su da fushi, don taurin zuciyarsu ya ɓata masa rai sosai. Sai ya ce wa mutumin, “Miƙo hannunka.” Sai ya miƙa, hannunsa kuwa ya koma lafiyayye. 6Sai Farisiyawa suka fita, suka fara ƙulla shawara da mutanen Hiridus yadda za su kashe Yesu.

Taron jama’a ya bi Yesu

7Yesu da almajiransa suka janye zuwa tafkin, taro mai yawa kuwa daga Galili ya bi shi. 8Mutane da yawa daga Yahudiya, da Urushalima, da Edom, da kuma yankunan da suke ƙetaren Urdun, da kewayen Taya, da Sidon suka zo wurinsa, don sun ji dukan abubuwan da yake yi. 9Saboda taron, sai ya ce wa almajiransa su shirya masa ƙaramin jirgin ruwa, don kada mutane su matse shi. 10Gama ya warkar da mutane da yawa, masu cututtuka suka yi ta ƙoƙarin zuwa gaba, don su taɓa shi. 11Duk sa’ad da mugayen ruhohi suka gan shi, sai fāɗi a gabansa, su ɗaga murya, su ce, “Kai Ɗan Allah ne.” 12Amma yakan tsawata musu, kada su shaida ko wane ne shi.

Naɗin manzanni sha biyu

(Mattiyu 10.1-4; Luka 6.12-16)

13Yesu ya hau gefen wani dutse, ya kira waɗanda yake so, suka kuma zo wurinsa. 14Ya naɗa sha biyu, ya kira su manzanni3.14 Waɗansu rubuce-rubucen hannu ba su da kira su manzanni. don su kasance tare da shi, domin kuma yă aike su yin wa’azi, 15don kuma su sami ikon fitar da aljanu.

16Ga sha biyun da ya naɗa.

Siman (wanda ya ba shi suna Bitrus);

17Yaƙub ɗan Zebedi da kuma ɗan’uwansa Yohanna (ga waɗannan kuwa ya sa musu suna Buwarnajis, wato, “’ya’yan tsawa”);

18Andarawus,

Filibus,

Bartolomeyu,

Mattiyu,

Toma,

Yaƙub ɗan Alfayus,

Taddayus,

Siman wanda ake kira Zilot,

19da kuma Yahuda Iskariyot, wanda ya bashe Yesu.

Yesu da Be’elzebub

(Mattiyu 12.22-32; Luka 11.14-23; 12.10)

20Sai Yesu ya shiga wani gida, taro kuma ya sāke haɗuwa, har shi da almajiransa ma ba su sami damar cin abinci ba. 21Da ’yan’uwansa suka sami wannan labari, sai suka tafi don su dawo da shi, suna cewa, “Ai, ya haukace.”

22Malaman dokokin da suka zo daga Urushalima suka ce, “Ai, yana da Be’elzebub3.22 Girik Be’ezebowul ko Be’elzebowul! Da ikon sarkin aljanu yake fitar da aljanu.”

23Sai Yesu ya kira su, ya yi musu magana da misalai ya ce, “Yaya Shaiɗan zai fitar da Shaiɗan? 24In mulki yana gāba da kansa, wannan mulki ba zai tsaya ba. 25In gida yana gāba da kansa, wannan gida ba zai tsaya ba. 26In kuwa Shaiɗan yana gāba da kansa, ya kuma rabu biyu, ba zai tsaya ba, ƙarshensa ya zo ke nan. 27Tabbatacce, ba mai shiga gidan mai ƙarfi yă kwashe dukiyarsa, sai bayan ya daure mai ƙarfin, sa’an nan zai iya yin fashin gidansa. 28Gaskiya nake gaya muku, za a gafarta duk zunubai da kuma saɓon mutane suka yi. 29Amma duk wanda ya saɓi Ruhu Mai Tsarki, ba za a taɓa gafara masa ba. Ya aikata madawwamin zunubi ke nan.”

30Ya faɗi haka domin suna cewa, “Yana da mugun ruhu.”

Mahaifiyar Yesu da ’yan’uwansa

(Mattiyu 12.46-50; Luka 8.19-21)

31Sai mahaifiyar Yesu tare da ’yan’uwansa suka iso. Suna tsaye a waje, sai suka aiki wani ciki yă kira shi. 32Taron yana zaune kewaye da shi, sai suka ce masa, “Mahaifiyarka da ’yan’uwanka suna waje, suna nemanka.”

33Ya yi tambaya ya ce, “Su wane ne mahaifiyata, da ’yan’uwana?”

34Sai ya dubi waɗanda suke zaune kewaye da shi ya ce, “Ga mahaifiyata da ’yan’uwana! 35Duk wanda yake aikata nufin Allah, shi ne ɗan’uwana, da ’yar’uwata, da kuma mahaifiyata.”