1 Peter 2 – KJV & HCB

King James Version

1 Peter 2:1-25

1Wherefore laying aside all malice, and all guile, and hypocrisies, and envies, and all evil speakings, 2As newborn babes, desire the sincere milk of the word, that ye may grow thereby: 3If so be ye have tasted that the Lord is gracious. 4To whom coming, as unto a living stone, disallowed indeed of men, but chosen of God, and precious, 5Ye also, as lively stones, are built up a spiritual house, an holy priesthood, to offer up spiritual sacrifices, acceptable to God by Jesus Christ. 6Wherefore also it is contained in the scripture, Behold, I lay in Sion a chief corner stone, elect, precious: and he that believeth on him shall not be confounded. 7Unto you therefore which believe he is precious: but unto them which be disobedient, the stone which the builders disallowed, the same is made the head of the corner, 8And a stone of stumbling, and a rock of offence, even to them which stumble at the word, being disobedient: whereunto also they were appointed. 9But ye are a chosen generation, a royal priesthood, an holy nation, a peculiar people; that ye should shew forth the praises of him who hath called you out of darkness into his marvellous light: 10Which in time past were not a people, but are now the people of God: which had not obtained mercy, but now have obtained mercy.

11Dearly beloved, I beseech you as strangers and pilgrims, abstain from fleshly lusts, which war against the soul; 12Having your conversation honest among the Gentiles: that, whereas they speak against you as evildoers, they may by your good works, which they shall behold, glorify God in the day of visitation.

13Submit yourselves to every ordinance of man for the Lord’s sake: whether it be to the king, as supreme; 14Or unto governors, as unto them that are sent by him for the punishment of evildoers, and for the praise of them that do well. 15For so is the will of God, that with well doing ye may put to silence the ignorance of foolish men: 16As free, and not using your liberty for a cloke of maliciousness, but as the servants of God. 17Honour all men. Love the brotherhood. Fear God. Honour the king. 18Servants, be subject to your masters with all fear; not only to the good and gentle, but also to the froward. 19For this is thankworthy, if a man for conscience toward God endure grief, suffering wrongfully. 20For what glory is it, if, when ye be buffeted for your faults, ye shall take it patiently? but if, when ye do well, and suffer for it, ye take it patiently, this is acceptable with God. 21For even hereunto were ye called: because Christ also suffered for us, leaving us an example, that ye should follow his steps: 22Who did no sin, neither was guile found in his mouth: 23Who, when he was reviled, reviled not again; when he suffered, he threatened not; but committed himself to him that judgeth righteously: 24Who his own self bare our sins in his own body on the tree, that we, being dead to sins, should live unto righteousness: by whose stripes ye were healed. 25For ye were as sheep going astray; but are now returned unto the Shepherd and Bishop of your souls.

Hausa Contemporary Bible

1 Bitrus 2:1-25

1Saboda haka, ku rabu da kowace ƙeta da dukan ruɗu, munafunci, kishi, da kuma kowace irin ɓata suna. 2Kamar sababbin jarirai, ku yi marmarin madara zalla ta ruhaniya, domin ta wurinta za ku yi girma cikin cetonku, 3yanzu da kuka ɗanɗana alherin Ubangiji.

Dutse mai rai da kuma zaɓaɓɓun mutane

4Da kuka zo gare shi, rayayyen Dutse, da mutane suka ƙi amma Allah ya zaɓa, kuma mai daraja a gare shi 5ku ma, a matsayinku na duwatsu masu rai, ana gina ku ga zama gidan ruhaniya don ku zama tsattsarkar ƙungiyar firistoci, kuna miƙa hadayun ruhaniya, abin karɓa ga Allah ta wurin Yesu Kiristi. 6Gama a cikin Nassi an ce,

“Ga shi, na kafa dutse a Sihiyona,

zaɓaɓɓen dutse na kusurwar gini mai daraja,

wanda kuma ya dogara gare shi

ba zai taɓa kunyata ba.”2.6 Ish 28.16

7A gare ku da kuka gaskata, wannan dutse mai daraja ne. Amma ga waɗanda ba su gaskata ba,

“Dutsen da magina suka ƙi

ya zama dutsen kusurwar gini,2.7 Zab 118.22

8kuma,

“Dutse ne da yake sa mutane tuntuɓe

kuma fā ne da yake sa su fāɗi.”2.8 Ish 8.14

Sun yi tuntuɓe domin sun ƙi su yi biyayya da saƙon, wanda kuma yake abin da aka ƙaddara musu.

9Amma ku zaɓaɓɓu ne, ƙungiyar firistocin babban Sarki, al’umma mai tsarki, jama’a mallakar Allah, domin ku shaida yabon shi wanda ya kira ku daga cikin duhu zuwa haskensa mai banmamaki. 10Dā ku ba mutane ba ne, amma yanzu ku mutanen Allah ne; Dā ba ku karɓi jinƙai ba, amma yanzu kun karɓi jinƙai.

11Abokaina ƙaunatattu, ina roƙonku, a matsayin bare da kuma baƙi a duniya, ku rabu da sha’awace-sha’awacen zunubin da suke yaƙi da ranku. 12Ku yi irin rayuwa mai kyau a cikin masu bautar gumaka, yadda ko da sun zarge ku da yin laifi, za su iya ganin ayyukanku nagari, su ɗaukaka Allah a ranar da zai ziyarce mu.

Biyayya ga masu mulki da iyayengiji

13Saboda Ubangiji, ku yi biyayya ga kowace hukumar da aka kafa cikin mutane, ko ga sarki, a matsayi wanda ya fi iko, 14ko ga gwamnoni, waɗanda ya aika domin su hukunta masu laifi su kuma yabi masu aikata abin da yake daidai. 15Gama nufin Allah ne cewa ta wurin yin nagarta za ku toshe jahilcin marasa azanci. 16Ku yi rayuwa kamar mutanen da aka ’yantar, sai dai kada ku yi amfani da ’yancinku a matsayin hujjar aikata mugunta; ku yi rayuwa kamar bayin Allah. 17Ku nuna ladabin da ya dace ga kowa. Ku ƙaunaci ’yan’uwantakar masu bi, ku ji tsoron Allah, ku girmama sarki.

18Bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku da matuƙar ladabi, ba kawai ga waɗanda suke da kirki da masu sauƙinkai ba, amma har ga masu zafin rai ma. 19Gama abin yabo ne in mutum ya yi haƙuri cikin zafin wahalar rashin adalci saboda yana sane da Allah. 20Amma ina abin taƙama in kuka sha duka saboda kun yi laifi kuka kuma jimre? Sai dai in kuka sha wahala saboda yin nagari kuka kuma jimre, abin yabo ne a gaban Allah. 21Ga wannan ne aka kira ku, domin Kiristi ya sha wahala dominku, ya bar muku gurbin da ya kamata ku bi.

22“Bai taɓa yin laifi ba sam,

ba a kuma sami ƙarya a bakinsa ba.”2.22 Ish 53.9

23Sa’ad da suka zazzage shi, bai rama ba; sa’ad da ya sha wahala, bai yi barazana ba. A maimakon haka, ya miƙa kansa ga wanda yake shari’ar adalci. 24Shi kansa ya ɗauki zunubanmu a jikinsa a kan itace, domin mu mutu ga zunubai mu kuma rayu ga adalci; ta wurin raunukansa ne kuka sami warkarwa. 25Gama dā kuna kama da tumakin da suka ɓace, amma yanzu kun dawo ga Makiyayi da kuma Mai lura da rayukanku.