Yaƙub 4 – HCB & NUB

Hausa Contemporary Bible

Yaƙub 4:1-17

Miƙa kanku ga Allah

1Me yake jawo faɗace-faɗace da gardandami a tsakaninku? Ashe, ba sha’awace-sha’awacenku da suke yaƙi a zukatanku ba ne? 2Kukan nemi abu ku rasa, sai ku yi kisa da ƙyashi. In kuka rasa abin da kuke nema sai ku shiga yin gardama da faɗa. Kukan rasa ne, domin ba ku roƙi Allah ba. 3Sa’ad da kuka roƙa, ba kwa samu, don kun roƙa da mugun nufi, don ku kashe abin da kuka samu a kan sha’awace-sha’awacenku.

4Ku mazinata, ba ku san cewa abokantaka da duniya gāba ce da Allah ba? Duk wanda ya zaɓa yă zama abokin duniya ya zama abokin gāban Allah ke nan. 5Ko kuna tsammani a banza ne Nassi ya ce ruhun da ya sa yă zauna a cikinmu yana kishi sosai? 6Amma yakan ba mu alheri a yalwace. Shi ya sa Nassi ya ce,

“Allah yana gāba da masu girman kai

amma yakan ba da alheri ga masu tawali’u.”4.6 K Mag 3.34

7Saboda haka, ku miƙa kanku ga Allah. Ku yi tsayayya da Iblis, zai kuwa guje ku. 8Ku matso kusa da Allah shi kuwa zai matso kusa da ku. Ku wanke hannuwanku, ku masu zunubi, ku kuma tsarkake zukatanku, ku masu zuciya biyu. 9Ku yi baƙin ciki, ku yi makoki ku kuma yi kuka. Ku mai da dariyarku ta zama makoki, farin cikinku kuma yă zama ɓacin zuciya. 10Ku ƙasƙantar da kanku a gaban Ubangiji, zai kuwa ɗaukaka ku.

11’Yan’uwa, kada ku ɓata wa juna suna. Duk wanda ya zargi ɗan’uwansa ko ya ɗora masa laifi, yana gāba da doka ne yana kuma yin mata shari’a ke nan. In kuwa ka ɗora wa shari’a laifi, kai ba mai binta ba ne, mai ɗora mata laifi ne. 12Akwai Mai ba da doka da kuma Alƙali guda ɗaya tak, shi ne yake da ikon ceto da kuma hallakarwa. Amma kai, wane ne da za ka hukunta maƙwabcinka?

Yin fahariya game da gobe

13Yanzu fa sai ku saurara, ku da kuke cewa, “Yau ko gobe za mu je wannan ko wancan birni, mu yi shekara a can, mu yi kasuwanci, mu ci riba.” 14Alhali kuwa ba ku ma san abin da zai faru gobe ba. Wane iri ne ranku? Ku kamar hazo ne da yake bayyana na ɗan lokaci sa’an nan yă ɓace. 15A maimakon haka, ya kamata ku ce, “In Ubangiji ya yarda, muna kuma a raye, za mu yi wannan ko wancan.” 16Ga shi, kuna fariya da taƙama. Duk irin wannan taƙama mugun abu ne. 17Saboda haka, duk wanda ya san abu mai kyan da ya kamata yă yi, bai kuwa yi ba, ya yi zunubi ke nan.

Swedish Contemporary Bible

Jakob 4:1-17

Lev nära Gud

1Vad är det som orsakar gräl och strider ibland er? Är det inte de själviska begär som vill ta makten över er kropp? 2Ni vill ha, men ni får ingenting. Ni dödar och är avundsjuka, men får inte vad ni vill ha. Ni grälar och strider men blir ändå inte tillfredsställda, eftersom ni inte ber. 3Och när ni ber, får ni ändå inget, eftersom ni har felaktiga motiv. Ni är bara ute efter att tillfredsställa era egna begär.

4Ni trolösa, förstår ni inte att vänskap med världen innebär fiendskap med Gud? Den som vill vara vän med världen blir fiende till Gud. 5Tror ni att det är utan grund som det står i Skriften: ”Svartsjukt vakar han över anden som han har låtit bo i oss?”4:5 Citatet är inte ordagrant. 5 Mos 4:24. 6Men han ger oss en större nåd. Därför heter det:

”Gud står emot de stolta,

men de ödmjuka visar han nåd.”4:6 Se Ords 3:34.

7Underordna er alltså Gud. Stå emot djävulen, så ska han fly ifrån er. 8Håll er nära Gud, så ska han hålla sig nära er. Rengör era händer, ni syndare. Rena era hjärtan, ni kluvna. 9Klaga, sörj och gråt. Vänd ert skratt i tårar och er glädje i sorg. 10Ödmjuka er inför Herren, så ska han upphöja er.

Varning för att döma andra

11Tala inte illa om varandra, syskon, för den som talar illa om andra och dömer dem, han talar illa om lagen och dömer ut den.4:11 Jfr 3 Mos 19:16. Men om du dömer lagen håller du den inte utan gör dig till domare över den. 12Det finns bara en lagstiftare och domare, han som ensam har makt att rädda eller förinta. Men vilken rätt har du att döma andra?

Varning för falsk säkerhet

13Ni som säger: ”Idag eller i morgon ska vi åka till den eller den staden, stanna där ett år och göra goda affärer”, 14ni kan ju inte veta vad som ska hända i morgon, eller hur ert liv ska bli. Ni är en dimma som i ena stunden syns och nästa stund är borta.4:14 Jfr Ps 144:4. 15Ni borde i stället säga: ”Om Herren vill och vi får leva, ska vi göra det eller det.” 16Men nu skryter ni med era egna planer, och allt sådant skryt är ont.

17Den som vet om det goda han borde göra men inte gör det, han syndar.