Yaƙub 2 – HCB & NIVUK

Hausa Contemporary Bible

Yaƙub 2:1-26

Kada a nuna bambanci

1’Yan’uwana, a matsayinmu cikin Ubangiji Yesu Kiristi maɗaukaki, kada ku nuna bambanci. 2A ce wani ya shigo cikin taronku saye da zoben zinariya da riguna masu tsada, wani matalauci kuma saye da tsummoki shi ma ya shigo, 3in kuka mai da hankali na musamman ga mutumin da yake da riguna masu tsadan nan kuka kuma ce, “Ga wurin zama mai kyau dominka,” amma kuka ce wa matalaucin nan, “Kai tsaya daga can,” ko kuwa, “Ka zauna a ƙasa kusa da ƙafafuna,” 4ashe, ba ku nuna bambanci a tsakaninku ke nan ba, kuka kuma zama alƙalai masu mugayen tunani?

5Ku saurara, ’yan’uwana ƙaunatattu. Ashe, Allah bai zaɓi waɗanda suke matalauta a idon duniya don su zama masu wadata cikin bangaskiya, su kuma gāji mulkin da ya yi wa masu ƙaunarsa alkawari ba? 6Ga shi kun wulaƙanta matalauta. Ashe, ba masu arziki ne suke cutarku ba? Ba su ba ne suke jan ku zuwa kotu? 7Ba su ba ne suke ɓata sunan nan mai martaba wanda aka san ku da shi ba?

8In fa kun kiyaye dokan nan ta mulki wadda take cikin Nassi mai cewa, “Ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka,”2.8 Fir 19.18 kun yi daidai. 9Amma in kuka nuna bambanci, kun yi zunubi ke nan shari’a kuma ta same ku da laifi a matsayin masu karya doka. 10Gama duk wanda ya kiyaye dukan doka amma ya yi tuntuɓe a kan abu ɗaya kaɗai, ya zama mai laifin karya dukansu ke nan. 11Gama shi da ya ce, “Kada ka yi zina,”2.11 Fit 20.14; M Sh 5.18 shi ne kuma ya ce, “Kada ka yi kisankai.”2.11 Fit 20.13; M Sh 5.17 In kuwa ba ka zina amma kana kisankai, ka zama mai karya doka ke nan.

12Ku yi magana ku kuma yi aiki kamar waɗanda za a yi musu shari’a bisa ga doka mai ba da ’yanci, 13gama za a yi wa duk wanda bai nuna jinƙai ba hukunci babu jinƙai. Jinƙai yakan yi nasara a kan hukunci!

Bangaskiya da ayyuka

14Wanda amfani ne, ’yan’uwana, a ce wani yă ce yana da bangaskiya, amma ba shi da ayyuka? Anya, wannan bangaskiya za tă iya cetonsa kuwa? 15A ce wani ɗan’uwa ko ’yar’uwa ba shi da riguna ko abincin yini, 16sai waninku yă ce masa, “Sauka lafiya, Allah ya ba da ci da sha da kuma sutura,” amma bai yi wani abu game da bukatunsa na jiki ba, ina amfani? 17Haka ma bangaskiya ita kaɗai, in ba tare da ayyuka ba, matacciya ce.

18Amma wani zai ce, “Kai kana da bangaskiya; ni kuma ina da ayyuka.”

Ka nuna mini bangaskiyarka ba tare da ayyuka ba, ni kuma zan nuna maka bangaskiyata ta wurin abin da nake yi. 19Ka gaskata cewa Allah ɗaya ne. To, da kyau! Ai, ko aljanu ma sun gaskata wannan, har da rawan jiki.

20Kai wawa, kana son tabbaci cewa bangaskiya marar ayyuka banza ce? 21Ashe, ba a mai da kakanmu Ibrahim mai adalci saboda abin da ya yi ba ne sa’ad da ya miƙa ɗansa Ishaku a bisa bagade? 22Ai, ka gani cewa bangaskiyarsa da ayyukansa sun yi aiki tare, bangaskiyarsa kuma ta zama cikakkiya ta wurin abin da ya yi. 23Aka kuma cika nassin nan da ya ce, “Ibrahim ya gaskata Allah, aka kuma lissafta wannan adalci ne gare shi,”2.23 Far 15.6 aka kuma ce da shi abokin Allah. 24Kun ga cewa ashe mutum zai sami kuɓuta ta wurin abin da ya yi ne ba ta wurin bangaskiya kaɗai ba.

25Ta haka kuma ashe, Rahab karuwan nan ba a ɗauke ta mai adalci ce saboda abin da ta yi ba ne sa’ad da ta ba wa ’yan leƙen asirin nan masauƙi ta kuma sallame su suka tafi ta wata hanya dabam? 26Kamar yadda jikin da babu ruhu matacce ne, haka ma bangaskiyar da babu ayyuka matacciya ce.

New International Version – UK

James 2:1-26

Favouritism forbidden

1My brothers and sisters, believers in our glorious Lord Jesus Christ must not show favouritism. 2Suppose a man comes into your meeting wearing a gold ring and fine clothes, and a poor man in filthy old clothes also comes in. 3If you show special attention to the man wearing fine clothes and say, ‘Here’s a good seat for you,’ but say to the poor man, ‘You stand there’ or ‘Sit on the floor by my feet,’ 4have you not discriminated among yourselves and become judges with evil thoughts?

5Listen, my dear brothers and sisters: has not God chosen those who are poor in the eyes of the world to be rich in faith and to inherit the kingdom he promised those who love him? 6But you have dishonoured the poor. Is it not the rich who are exploiting you? Are they not the ones who are dragging you into court? 7Are they not the ones who are blaspheming the noble name of him to whom you belong?

8If you really keep the royal law found in Scripture, ‘Love your neighbour as yourself,’2:8 Lev. 19:18 you are doing right. 9But if you show favouritism, you sin and are convicted by the law as law-breakers. 10For whoever keeps the whole law and yet stumbles at just one point is guilty of breaking all of it. 11For he who said, ‘You shall not commit adultery,’2:11 Exodus 20:14; Deut. 5:18 also said, ‘You shall not murder.’2:11 Exodus 20:13; Deut. 5:17 If you do not commit adultery but do commit murder, you have become a law-breaker.

12Speak and act as those who are going to be judged by the law that gives freedom, 13because judgment without mercy will be shown to anyone who has not been merciful. Mercy triumphs over judgment.

Faith and deeds

14What good is it, my brothers and sisters, if someone claims to have faith but has no deeds? Can such faith save them? 15Suppose a brother or a sister is without clothes and daily food. 16If one of you says to them, ‘Go in peace; keep warm and well fed,’ but does nothing about their physical needs, what good is it? 17In the same way, faith by itself, if it is not accompanied by action, is dead.

18But someone will say, ‘You have faith; I have deeds.’

Show me your faith without deeds, and I will show you my faith by my deeds. 19You believe that there is one God. Good! Even the demons believe that – and shudder.

20You foolish person, do you want evidence that faith without deeds is useless2:20 Some early manuscripts dead? 21Was not our father Abraham considered righteous for what he did when he offered his son Isaac on the altar? 22You see that his faith and his actions were working together, and his faith was made complete by what he did. 23And the scripture was fulfilled that says, ‘Abraham believed God, and it was credited to him as righteousness,’2:23 Gen. 15:6 and he was called God’s friend. 24You see that a person is considered righteous by what they do and not by faith alone.

25In the same way, was not even Rahab the prostitute considered righteous for what she did when she gave lodging to the spies and sent them off in a different direction? 26As the body without the spirit is dead, so faith without deeds is dead.