Romawa 15 – HCB & JCB

Hausa Contemporary Bible

Romawa 15:1-33

1Mu da muke da ƙarfi ya kamata mu yi haƙuri da kāsawar marasa ƙarfi ba kawai mu gamshi kanmu ba. 2Ya kamata kowannenmu yă faranta wa maƙwabcinsa rai don kyautata zamansa domin kuma yă gina shi. 3Gama ko Kiristi ma bai gamshi kansa ba, amma kamar yadda yake a rubuce cewa, “Zage-zagen da waɗansu suka yi maka, duk sun fāɗo a kaina.”15.3 Zab 69.9 4Gama duk abin da aka rubuta a dā an rubuta ne domin yă koya mana, don ta wurin jimrewa da kuma ƙarfafawar Nassosi mu kasance da bege.

5Bari Allah mai ba da haƙuri da kuma ƙarfafawa yă ba ku ruhun haɗinkai da juna yayinda kuke bin Kiristi Yesu, 6don da zuciya ɗaya da kuma baki ɗaya kuke ɗaukaka Allah da kuma Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi.

7Ta haka sai ku karɓi juna kamar yadda Kiristi ya karɓe ku, don a yabi Allah. 8Ina dai gaya muku cewa Kiristi ya zama bawan Yahudawa a madadin gaskiyar Allah, don yă tabbatar da alkawaran da aka yi wa kakannin kakanninmu 9domin Al’ummai su ɗaukaka Allah saboda jinƙansa, kamar yadda yake a rubuce,

“Saboda haka zan yabe ka a cikin Al’ummai;

zan rera waƙoƙi ga sunanka.”15.9 2Sam 22.50; Zab 18.49

10Ya kuma ce,

“Ku yi farin ciki, ya Al’ummai, tare da mutanensa.”15.10 M Sh 32.43

11Da kuma,

“Ku yabi Ubangiji, dukanku Al’ummai,

ku kuma rera masa yabo, dukanku mutanen duniya.”15.11 Zab 117.1

12Kuma Ishaya ya ce,

“Tushen Yesse zai tsiro,

wanda zai taso yă yi mulkin al’ummai;

al’ummai za su sa bege a gare shi.”15.12 Ish 11.10

13Bari Allah na bege yă cika ku da matuƙar farin ciki da salama yayinda kuke dogara gare shi, domin ku yalwata cikin bege ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.

Bulus mai hidima ga al’ummai

14Ni kaina na tabbata, ’yan’uwana, cewa ku kanku kuna cike da kirki, cikakku cikin sani da kuma ƙwararru don yin wa juna gargaɗi. 15Na rubuta muku gabagadi a kan waɗansu batuttuwa, don in sāke tuna muku su, saboda alherin da Allah ya ba ni 16in zama mai hidimar Kiristi Yesu ga Al’ummai da aikin firist na yin shelar bisharar Allah, don Al’ummai su zama hadaya mai karɓuwa ga Allah, tsattsarka ta wurin Ruhu Mai Tsarki.

17Saboda haka ina taƙama cikin Kiristi Yesu a cikin hidimata ga Allah. 18Ba zan yi karambani in faɗi kome ba sai dai abin da Kiristi ya aikata ta wurina a jagorantar da Al’ummai su yi biyayya ga Allah ta wurin abin da na faɗa da kuma aikata 19ta wurin ikon alamu da ayyukan banmamaki, da kuma ikon Ruhun Allah. Ta haka daga Urushalima har yă zuwa kewayen Illirikum, na yi wa’azin bisharar Kiristi. 20Labudda, burina shi ne in yi wa’azin bishara inda ba a san Kiristi ba, don kada yă zama ina gini ne a kan tushen da wani ya kafa. 21Sai dai kamar yadda yake a rubuce,

“Waɗanda ba a faɗa musu labarinsa ba za su gani,

waɗanda kuma ba su ji ba za su fahimta.”15.21 Ish 52.15

22Wannan ne ya sa sau da yawa aka hana ni zuwa wurinku.

Shirin Bulus yă ziyarci Roma

23Amma yanzu da babu sauran wurin da ya rage mini in yi aiki a waɗannan yankuna, da yake kuma shekaru masu yawa ina da marmari in gan ku, 24ina shirin yin haka in na tafi Sifen. Ina fata in ziyarce ku yayinda nake wucewa don ku raka ni can, bayan na ji daɗin zama tare da ku na ɗan lokaci. 25Yanzu kam, ina hanyata zuwa Urushalima don in kai gudummawa ga tsarkaka a can. 26Gama Makidoniya da Akayya sun ji daɗin yin gudummawa domin matalautan da suke cikin tsarkakan da suke a Urushalima. 27Sun kuwa ji daɗin yin haka, gama ya zama kamar bashi ne a gare su. Da yake Al’ummai sun sami rabo cikin albarkun ruhaniyar Yahudawa, ya zama musu kamar bashi su ma su taimaki Yahudawa da albarkunsu na kayan duniya. 28Saboda haka in na kammala wannan aiki na kuma tabbata cewa sun karɓi wannan amfani, zan tafi Sifen in kuma ziyarce ku a hanyata. 29Na san cewa sa’ad da na zo wurinku, zan zo ne cikin yalwar albarkar Kiristi.

30Ina roƙonku ’yan’uwa, saboda Ubangijinmu Yesu Kiristi da kuma saboda ƙaunar Ruhu, ku haɗa kai tare da ni cikin famata ta wurin yin addu’a ga Allah saboda ni. 31Ku yi addu’a don in kuɓuta daga hannun marasa bi a Yahudiya don kuma gudummawar da nake kaiwa Urushalima ta zama abar karɓa ga tsarkaka a can, 32don da yardar Allah, in iso wurinku da farin ciki in kuma wartsake tare da ku. 33Allah na salama yă kasance tare da ku duka. Amin.

Japanese Contemporary Bible

ローマ人への手紙 15:1-33

15

1-2何かをする場合、ただ自分の喜びのためにするのはよくありません。それは悪いことではないかと疑問や不安を持つ人を思いやり、そういう弱さを持つ人々の「重荷」を軽くしてあげなさい。そして、人の益になることをし、その人が主にあって成長できるよう支えましょう。

3キリストも、ご自分を喜ばせようとはなさいませんでした。「彼が来られたのは、実に、敵対する者たちの侮辱を受けて苦しむためであった」と、詩篇の作者が言っているとおりです。 4ずっと昔に書かれたこのことばは、私たちに忍耐を教え、励ますためのものです。また、神が死と罪の力とを打ち破ってくださる時を、私たちが待ち望むためのものです。 5どうか、強い忍耐力と励ましを与える神が、あなたがたが一つ思いとなって暮らしていけるよう、助けてくださいますように。一人一人がキリストの模範にならって互いに接することができますように。 6そうして初めて、私たちはみな、主イエス・キリストの父なる神をほめたたえ、声を合わせて賛美できるのです。

すべての人が神をたたえる

7そういうわけですから、キリストがあなたがたを受け入れてくださったように、あなたがたも互いにあたたかく受け入れ合いなさい。そうすれば、神がほめたたえられるのです。 8イエス・キリストが来られたのは、神がご自分の約束に対して誠実な方であることを示すため、また、ユダヤ人を助けるためであったことを思い出してください。 9それはまた、外国人も救われて、自分たちに対する神のあわれみのゆえに神をほめたたえるためでもあったことを、思い出してください。次のように書かれているとおりです。

「私は外国人の中で、あなたを賛美し、

あなたの御名をほめ歌おう。」詩篇18・49

10また、ほかの箇所にはこうあります。

「外国人よ。主の民であるユダヤ人と共に喜べ。」申命32・43

11「外国人よ。主をほめたたえよ。

すべての人よ。主をほめたたえよ。」詩篇117・1

12また、預言者イザヤはこう言っています。

「エッサイの家系に一人の世継ぎが生まれる。

その方は外国人を治める王となる。

彼らは、ただこの方だけに望みをかける。」イザヤ11・10

13そこで、私はあなたがた外国人のために祈ります。どうか、希望を与えてくださる神があなたがたを幸せにし、平安で満たしてくださいますように。どうかあなたがたを、聖霊の力によって希望にあふれさせてくださいますように。

14私の兄弟たちよ。あなたがたが知恵に満ち、善意にあふれていること、そして、これらを他の人々に教えることができるほどよくわきまえていることを、私は知っています。 15-16それにもかかわらず、私が所々かなり大胆に強調して書いたのは、あなたがたにそのことを思い起こしてもらいたかったからです。私は神の恵みにより、あなたがた外国人のためにキリスト・イエスに仕える者であって、福音を伝え、かおり高い供え物として、あなたがたを神にささげる務めを果たしているのです。あなたがたは聖霊によって、きよい者、神に喜ばれる者とされています。

17それで、キリスト・イエスが私を用いてなしてくださったことを、誇りに思っています。 18私は、ただ外国人を神に導くために、キリストが私を役立ててくださったということだけを話します。他のことについて、何も言うつもりはありません。私は、ことばと活動、 19および、私を通してなされた奇跡と御霊の力によって、外国人を神に導いてきました。このようにして私は、エルサレムからイルリコに至るまで、キリストの福音をくまなく伝えてきました。 20すでに、だれかほかの人によって伝道がなされている所ではなく、むしろ、キリストの名をまだ一度も聞いたことがない人々の所で、福音を宣べ伝えたいと切に望みました。 21イザヤが、「彼(キリスト)の名を一度も聞いたことのない人々が見て理解するようになる」イザヤ52・15と言っているとおりに働いてきたのです。

22このような事情のもとで、私はこれまで、あなたがたの所に行けませんでした。 23しかし、もうこちらでの働きも終わり、長いあいだ待ったかいがあって、とうとうそちらに行けそうです。 24実は今、スペインでの伝道を計画しています。その途中、ローマに立ち寄るつもりです。そして、わずかな間でも、共に心の満たされた時を過ごしてから、あなたがたに送られて、旅を続けたいと願っています。

困った時には助け合う

25しかし、その前に、エルサレムに行かなければなりません。そこにいるユダヤ人のクリスチャンに、献金を届けるためです。 26ご存じのように、マケドニヤとアカヤのクリスチャンが、いま困難に会っているエルサレムのクリスチャンのために、募金することにしたからです。 27彼らは、それを喜んでしてくれました。エルサレムのクリスチャンには大きな借りがあると思っているのです。どうしてかわかりますか。福音がエルサレムの教会から伝えられたからです。彼らはエルサレム教会から、福音というすばらしい霊の贈り物を受けました。そこで、いくらかでも物質的な援助をして恩返しができればと願っているのです。 28それで私は、この献金を渡し終えてから、スペインに行く途中で、あなたがたを訪ねたいと思っています。 29その時にはきっと、主からの大きな祝福を分かち合えるでしょう。

30どうか、私の祈りの友になってください。主イエス・キリストのゆえに、また、聖霊によってあなたがたが私を愛する愛のゆえに、私の働きのため、共に精一杯祈ってください。 31エルサレムにいる、クリスチャンでないユダヤ人から、私が守られるよう祈ってください。また、私の持って行くお金を、エルサレムの教会が喜んで受け取ってくれるようにも祈ってください。 32そうすれば私は、神の御心により、喜びにあふれてあなたがたの所に行き、互いに励まし合うことができます。 33どうか、平安を与えてくださる神が、あなたがた一同と共にいてくださいますように。アーメン。