Mattiyu 19 – HCB & NIV

Hausa Contemporary Bible

Mattiyu 19:1-30

Kashen aure

(Markus 10.1-12)

1Sa’ad da Yesu ya gama faɗin waɗannan abubuwa, sai ya bar Galili, ya tafi yankin Yahudiya a ɗaya gefen Urdun. 2Taron mutane mai yawa suka bi shi, ya kuwa warkar da su a can.

3Waɗansu Farisiyawa suka zo wurinsa don su gwada shi. Suka yi tambaya suka ce, “Daidai ne mutum yă saki matarsa saboda wani dalili da kuma a kan kowane dalili?”

4Ya amsa ya ce, “Ba ku taɓa karantawa ba ne cewa, a farkon halitta, Mahalicci ‘ya yi su namiji da ta mace,’19.4 Far 1.27 5ya kuma ce, ‘Saboda wannan dalili, namiji zai bar mahaifinsa da mahaifiyarsa yă manne wa matarsa, biyun kuwa su zama jiki guda’?19.5 Far 2.24 6Ta haka, ba sa ƙara zama biyu, sai dai ɗaya. Saboda haka abin da Allah ya haɗa fa, kada mutum yă raba.”

7Suka yi tambaya, suka ce, “To, me ya sa Musa ya umarta cewa mutum yă ba wa matarsa takardar saki, yă kuma kore ta?”

8Yesu ya amsa ya ce, “Musa ya ba ku izini ku saki matanku saboda taurin zuciyarku ne. Amma ba haka yake ba daga farko. 9Ina faɗa muku cewa duk wanda ya saki matarsa, sai dai a kan rashin aminci a cikin aure, ya kuwa auri wata, ya yi zina ke nan.”

10Almajiran suka ce masa, “In haka yake tsakanin miji da mata, ashe, ya ma fi kyau kada a yi aure.”

11Yesu ya ce, “Ba kowa ba ne zai yarda da wannan magana, sai dai waɗanda aka yarda musu. 12Gama waɗansu bābānni ne domin haka aka haife su; waɗansu kuwa mutane ne suka mai da su haka; waɗansu kuma sun ƙi aure ne saboda mulkin sama. Duk mai iya ɗaukar wannan yă ɗauka.”

Yesu da ƙananan yara

(Markus 10.13-16; Luka 18.15-17)

13Sa’an nan aka kawo yara ƙanana wurin Yesu don yă ɗibiya musu hannuwansa, yă kuma yi musu addu’a. Amma almajirai suka tsawata wa waɗanda suka kawo su.

14Yesu ya ce, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su, gama mulkin sama na irin waɗannan ne.” 15Sa’ad da ya ɗibiya musu hannuwansa, sai ya tafi abinsa.

Saurayi mai arziki

(Markus 10.17-31; Luka 18.18-30)

16To, fa, sai ga wani ya zo wurin Yesu ya tambaye shi ya ce, “Malam, wane abu mai kyau ne ya zama mini dole in yi don in sami rai madawwami?”

17Yesu ya amsa ya ce, “Don me kake tambayata game da abin da yake mai kyau? Akwai Mai kyau Ɗaya kaɗai. In kana so ka sami rai madawwami, ka kiyaye dokokin nan.”

18Mutumin ya yi tambaya ya ce, “Waɗanne?”

Yesu ya amsa ya ce, “ ‘Kada ka yi kisankai, kada ka yi zina, kada ka yi sata, kada ka yi shaidar ƙarya, 19ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,’19.19 Fit 20.12-16; M Sh 5.16-20 ka kuma ‘ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’19.19 Fir 19.18

20Saurayin ya ce, “Duk waɗannan na kiyaye. Me kuma ya rage mini?”

21Yesu ya amsa ya ce, “In kana so ka zama cikakke, ka je, ka sayar da dukan dukiyarka ka kuma ba matalauta, za ka kuwa sami dukiya a sama. Sa’an nan ka zo, ka bi ni.”

22Da saurayin ya ji haka, sai ya tafi rai a ɓace, don yana da arziki sosai.

23Sa’an nan Yesu ya ce wa almajiransa, “Gaskiya nake gaya muku, yana da wuya mai arziki yă shiga mulkin sama. 24Har wa yau ina gaya muku, zai fi sauƙi raƙumi yă shiga ta kafar allura, da mai arziki yă shiga mulkin Allah.”

25Sa’ad da almajiran suka ji wannan, sai suka yi mamaki ƙwarai. Suka yi tambaya suka ce, “To, wa zai sami ceto ke nan?”

26Yesu ya kalle su ya ce, “Ga mutum kam, wannan ba ya yiwuwa, amma ga Allah kuwa, dukan abubuwa masu yiwuwa ne.”

27Sai Bitrus ya amsa masa, “Ga shi mun bar kome don mu bi ka! Me za mu samu ke nan?”

28Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, a lokacin sabunta dukan kome, sa’ad da Ɗan Mutum ya zauna a kan kursiyinsa mai daraja, ku da kuka bi ni, ku ma za ku zauna a kan kursiyoyi goma sha biyu, kuna yi wa kabilu goma sha biyu na Isra’ila shari’a. 29Duk kuma wanda ya bar gidaje ko ’yan’uwa maza ko ’yan’uwa mata ko mahaifi ko mahaifiya ko yara ko gonaki, saboda ni, zai sami abin da ya fi haka riɓi ɗari, yă kuma gāji rai madawwami. 30Amma da yawa da suke na farko, za su zama na ƙarshe, da yawa kuma da suke na ƙarshe, za su zama na farko.

New International Version

Matthew 19:1-30

Divorce

1When Jesus had finished saying these things, he left Galilee and went into the region of Judea to the other side of the Jordan. 2Large crowds followed him, and he healed them there.

3Some Pharisees came to him to test him. They asked, “Is it lawful for a man to divorce his wife for any and every reason?”

4“Haven’t you read,” he replied, “that at the beginning the Creator ‘made them male and female,’19:4 Gen. 1:27 5and said, ‘For this reason a man will leave his father and mother and be united to his wife, and the two will become one flesh’19:5 Gen. 2:24? 6So they are no longer two, but one flesh. Therefore what God has joined together, let no one separate.”

7“Why then,” they asked, “did Moses command that a man give his wife a certificate of divorce and send her away?”

8Jesus replied, “Moses permitted you to divorce your wives because your hearts were hard. But it was not this way from the beginning. 9I tell you that anyone who divorces his wife, except for sexual immorality, and marries another woman commits adultery.”

10The disciples said to him, “If this is the situation between a husband and wife, it is better not to marry.”

11Jesus replied, “Not everyone can accept this word, but only those to whom it has been given. 12For there are eunuchs who were born that way, and there are eunuchs who have been made eunuchs by others—and there are those who choose to live like eunuchs for the sake of the kingdom of heaven. The one who can accept this should accept it.”

The Little Children and Jesus

13Then people brought little children to Jesus for him to place his hands on them and pray for them. But the disciples rebuked them.

14Jesus said, “Let the little children come to me, and do not hinder them, for the kingdom of heaven belongs to such as these.” 15When he had placed his hands on them, he went on from there.

The Rich and the Kingdom of God

16Just then a man came up to Jesus and asked, “Teacher, what good thing must I do to get eternal life?”

17“Why do you ask me about what is good?” Jesus replied. “There is only One who is good. If you want to enter life, keep the commandments.”

18“Which ones?” he inquired.

Jesus replied, “ ‘You shall not murder, you shall not commit adultery, you shall not steal, you shall not give false testimony, 19honor your father and mother,’19:19 Exodus 20:12-16; Deut. 5:16-20 and ‘love your neighbor as yourself.’19:19 Lev. 19:18

20“All these I have kept,” the young man said. “What do I still lack?”

21Jesus answered, “If you want to be perfect, go, sell your possessions and give to the poor, and you will have treasure in heaven. Then come, follow me.”

22When the young man heard this, he went away sad, because he had great wealth.

23Then Jesus said to his disciples, “Truly I tell you, it is hard for someone who is rich to enter the kingdom of heaven. 24Again I tell you, it is easier for a camel to go through the eye of a needle than for someone who is rich to enter the kingdom of God.”

25When the disciples heard this, they were greatly astonished and asked, “Who then can be saved?”

26Jesus looked at them and said, “With man this is impossible, but with God all things are possible.”

27Peter answered him, “We have left everything to follow you! What then will there be for us?”

28Jesus said to them, “Truly I tell you, at the renewal of all things, when the Son of Man sits on his glorious throne, you who have followed me will also sit on twelve thrones, judging the twelve tribes of Israel. 29And everyone who has left houses or brothers or sisters or father or mother or wife19:29 Some manuscripts do not have or wife. or children or fields for my sake will receive a hundred times as much and will inherit eternal life. 30But many who are first will be last, and many who are last will be first.