Mattiyu 15 – HCB & KJV

Hausa Contemporary Bible

Mattiyu 15:1-39

Mai tsabta da marar tsabta

(Markus 7.1-13)

1Sa’an nan waɗansu Farisiyawa da malaman dokoki suka zo wurin Yesu daga Urushalima suka yi tambaya suka ce, 2“Me ya sa almajiranka suke karya al’adun dattawa? Ba sa wanke hannuwansu kafin su ci abinci!”

3Yesu ya amsa ya ce, “Ku ma me ya sa kuke karya dokar Allah saboda al’adarku? 4Gama Allah ya ce, ‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,15.4 Fit 20.12; M Sh 5.16 kuma duk wanda ya zagi mahaifinsa ko mahaifiyarsa dole a kashe shi.’15.4 Fit 21.17; Fir 20.9 5Amma ku kukan ce, in wani ya ce wa mahaifinsa ko mahaifiyarsa, ‘Duk taimakon da dā ya kamata za ku samu daga gare ni an ba wa Allah,’ 6ba zai ‘girmama mahaifinsa’ da shi ba. Ta haka kun yi banza da maganar Allah saboda al’adarku. 7Ku munafukai! Daidai ne Ishaya ya yi annabci a kanku da ya ce,

8“ ‘Waɗannan mutane da baki kawai suke girmama ni,

amma zukatansu suna nesa da ni.

9A banza suke mini sujada,

koyarwarsu, dokoki ne kawai da mutane suke koyarwa.’ ”15.9 Ish 29.13

(Markus 7.14-23)

10Sai Yesu ya kira taron wurinsa ya ce, “Ku saurara ku kuma gane. 11Abin da yake shiga bakin mutum ba ya ƙazantar da shi, sai dai abin da yake fitowa daga bakinsa, shi ne yake ƙazantar da shi.”

12Sai almajiran suka zo wurinsa suka ce, “Ka san cewa Farisiyawa ba su ji daɗi sa’ad da suka ji wannan ba?”

13Ya amsa ya ce, “Duk tsiron da Ubana na sama bai shuka ba, za a tumɓuke shi daga saiwoyi. 14Ku ƙyale su, ai, makafin jagorai ne.15.14 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā suna da jagorai ne na makafi In makaho ya yi wa makaho jagora, dukansu za su fāɗa a rami.”

15Bitrus ya ce, “Ka bayyana mana wannan misali.”

16Yesu ya tambaye su ya ce, “Har yanzu ba ku gane ba ne? 17Ba ku gane cewa duk abin da ya shiga baki yakan wuce ciki ne daga nan kuma yă fita daga jiki ba? 18Amma abubuwan da suke fitowa ta baki suna fitowa ne daga zuciya, su ne kuma suke ƙazantar da mutum. 19Gama daga zuciya ne mugayen tunani, kisankai, zina, fasikanci, sata, shaidar ƙarya, ɓatan suna, suka fitowa. 20Waɗannan su ne suke ƙazantar da mutum; amma cin abinci ba tare da wanke hannuwa ba, ba ya ƙazantar da mutum.”

Bangaskiyar mutuniyar Kan’ana

(Markus 7.24-30)

21Barin wurin ke nan, sai Yesu ya janye zuwa yankin Taya da Sidon. 22Wata mutuniyar Kan’ana daga wajajen ta zo wurinsa, tana ihu tana cewa, “Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai! ’Yata tana shan wahala ƙwarai daga aljanin da yake cikinta.”

23Yesu bai ce mata uffam ba. Saboda haka almajiransa suka zo wurinsa suka roƙe shi suka ce, “Ka kore ta tă tafi, tana ta binmu tana damunmu da ihu.”

24Ya amsa ya ce, “An aiko ni wurin ɓatattun tumakin Isra’ila ne kaɗai.”

25Sai macen ta zo ta durƙusa a gabansa ta ce, “Ubangiji, ka taimake ni!”

26Ya amsa ya ce, “Ba daidai ba ne a ɗauki abincin yara a jefa wa karnukansu.”

27Ta amsa, ta ce, “I, Ubangiji, amma karnuka ma sukan ci gutsattsarin da sukan fāɗi daga teburin maigidansu.”

28Sa’an nan Yesu ya amsa ya ce, “Mace, kina da bangaskiya mai yawa! An biya miki bukatarki.” ’Yarta kuwa ta warke nan take.

Yesu ya ciyar da dubu huɗu

29Yesu ya tashi daga nan ya bi ta gefen Tekun Galili. Sa’an nan ya haura gefen wani dutse ya zauna. 30Taron mutane mai girma kuwa suka zo wurinsa, suna kawo masa guragu, makafi, shanyayyu, kurame da dai waɗansu da yawa, suka kuwa kwantar da su a gabansa; ya kuma warkar da su. 31Mutanen kuwa suka yi mamaki sa’ad da suka ga kurame suna magana, shanyayyu suna samun lafiya, guragu suna takawa, makafi kuma suna ganin gari. Sai suka yabi Allah na Isra’ila.

(Markus 8.1-10)

32Yesu ya kira almajiransa wurinsa ya ce, “Ina jin tausayin mutanen nan; gama kwana uku ke nan suke tare da ni ba abin da za su ci. Ba na so in sallame su da yunwa, don kada su kāsa a hanya.”

33Sai almajiransa suka amsa suka ce, “Ina za mu sami isashen burodi a wannan wurin da babu kowa mu ciyar da irin taron nan?”

34Yesu ya tambaye su, “Burodi guda nawa kuke da shi?”

Suka amsa suka ce, “Guda bakwai da ’yan ƙananan kifaye.”

35Ya sa taron su zazzauna a ƙasa. 36Sa’an nan ya ɗauki burodi guda bakwai da kuma kifayen nan, da ya yi godiya, sai ya kakkarya su ya ba wa almajiran, su kuma suka ba wa mutane. 37Duk kuwa suka ci, suka ƙoshi. Daga baya almajiran suka kwashe ragowar gutsattsarin cike da kwanduna bakwai. 38Yawan waɗanda suka ci kuwa, maza dubu huɗu ne, ban da mata da yara. 39Bayan Yesu ya sallami taron, sai ya shiga jirgin ruwa ya tafi wajajen Magadan.

King James Version

Matthew 15:1-39

1Then came to Jesus scribes and Pharisees, which were of Jerusalem, saying, 2Why do thy disciples transgress the tradition of the elders? for they wash not their hands when they eat bread. 3But he answered and said unto them, Why do ye also transgress the commandment of God by your tradition? 4For God commanded, saying, Honour thy father and mother: and, He that curseth father or mother, let him die the death. 5But ye say, Whosoever shall say to his father or his mother, It is a gift, by whatsoever thou mightest be profited by me; 6And honour not his father or his mother, he shall be free. Thus have ye made the commandment of God of none effect by your tradition. 7Ye hypocrites, well did Esaias prophesy of you, saying, 8This people draweth nigh unto me with their mouth, and honoureth me with their lips; but their heart is far from me. 9But in vain they do worship me, teaching for doctrines the commandments of men.

10¶ And he called the multitude, and said unto them, Hear, and understand: 11Not that which goeth into the mouth defileth a man; but that which cometh out of the mouth, this defileth a man. 12Then came his disciples, and said unto him, Knowest thou that the Pharisees were offended, after they heard this saying? 13But he answered and said, Every plant, which my heavenly Father hath not planted, shall be rooted up. 14Let them alone: they be blind leaders of the blind. And if the blind lead the blind, both shall fall into the ditch. 15Then answered Peter and said unto him, Declare unto us this parable. 16And Jesus said, Are ye also yet without understanding? 17Do not ye yet understand, that whatsoever entereth in at the mouth goeth into the belly, and is cast out into the draught? 18But those things which proceed out of the mouth come forth from the heart; and they defile the man. 19For out of the heart proceed evil thoughts, murders, adulteries, fornications, thefts, false witness, blasphemies: 20These are the things which defile a man: but to eat with unwashen hands defileth not a man.

21¶ Then Jesus went thence, and departed into the coasts of Tyre and Sidon. 22And, behold, a woman of Canaan came out of the same coasts, and cried unto him, saying, Have mercy on me, O Lord, thou Son of David; my daughter is grievously vexed with a devil. 23But he answered her not a word. And his disciples came and besought him, saying, Send her away; for she crieth after us. 24But he answered and said, I am not sent but unto the lost sheep of the house of Israel. 25Then came she and worshipped him, saying, Lord, help me. 26But he answered and said, It is not meet to take the children’s bread, and to cast it to dogs. 27And she said, Truth, Lord: yet the dogs eat of the crumbs which fall from their masters’ table. 28Then Jesus answered and said unto her, O woman, great is thy faith: be it unto thee even as thou wilt. And her daughter was made whole from that very hour. 29And Jesus departed from thence, and came nigh unto the sea of Galilee; and went up into a mountain, and sat down there. 30And great multitudes came unto him, having with them those that were lame, blind, dumb, maimed, and many others, and cast them down at Jesus’ feet; and he healed them: 31Insomuch that the multitude wondered, when they saw the dumb to speak, the maimed to be whole, the lame to walk, and the blind to see: and they glorified the God of Israel.

32¶ Then Jesus called his disciples unto him, and said, I have compassion on the multitude, because they continue with me now three days, and have nothing to eat: and I will not send them away fasting, lest they faint in the way. 33And his disciples say unto him, Whence should we have so much bread in the wilderness, as to fill so great a multitude? 34And Jesus saith unto them, How many loaves have ye? And they said, Seven, and a few little fishes. 35And he commanded the multitude to sit down on the ground. 36And he took the seven loaves and the fishes, and gave thanks, and brake them, and gave to his disciples, and the disciples to the multitude. 37And they did all eat, and were filled: and they took up of the broken meat that was left seven baskets full. 38And they that did eat were four thousand men, beside women and children. 39And he sent away the multitude, and took ship, and came into the coasts of Magdala.