Mattiyu 11 – HCB & CCB

Hausa Contemporary Bible

Mattiyu 11:1-30

Yesu da Yohanna Mai Baftisma

(Luka 7.18-35)

1Bayan Yesu ya gama yi wa almajiransa sha biyun nan umarni, sai ya yi gaba daga can don yă koyar yă kuma yi wa’azi a garuruwan Galili.11.1 Da Girik a cikin garuruwansu

2Sa’ad da Yohanna Mai Baftisma ya ji a kurkuku abin da Kiristi yake yi, sai ya aiki almajiransa 3su tambaye shi, “Kai ne wanda zai zo, ko kuwa mu sa ido ga wani?”

4Yesu ya amsa ya ce, “Ku koma ku gaya wa Yohanna abin da kuka ji, kuka kuma gani. 5Makafi suna gani, guragu suna tafiya, ana warkar da waɗanda suke da kuturta, kurame suna ji, ana tā da matattu, ana kuma yi wa matalauta wa’azin labari mai daɗi. 6Mai albarka ne mutumin da bai yi tuntuɓe ba saboda ni.”

7Sa’ad da almajiran Yohanna suke barin wurin, sai Yesu ya fara yi wa taron magana game da Yohanna. “Me kuka je kallo a hamada? Ciyawar da iska take kaɗawa ne? 8In ba haka ba, to, me kuka je kallo? Mutum mai sanye da riguna masu kyau ne? A’a, masu sa riguna masu kyau, ai, a fadan sarakuna suke. 9To, me kuka je kallo ne? Annabi? I, ina gaya muku, ya ma fi annabi. 10Wannan shi ne wanda aka rubuta game da shi cewa,

“ ‘Zan aiki ɗan saƙona yă sha gabanka,

wanda zai shirya hanyarka a gabanka.’11.10 Mal 3.1

11Gaskiya nake gaya muku. A cikin dukan waɗanda mata suka haifa, ba wani da ya taso da ya fi Yohanna Mai Baftisma girma; duk da haka mafi ƙanƙanta a mulkin sama ya fi shi girma. 12Tun daga kwanakin Yohanna Mai Baftisma har yă zuwa yanzu, mulkin sama yana sha da ƙyar, fitanannu kuma sun kama mulkin sama sun riƙe gam. 13Gama dukan Annabawa da kuma Doka sun yi ta annabci har yă zuwa kan Yohanna. 14In kuna niyya ku yarda da wannan, to, shi ne Iliya da dā ma zai zo. 15Duk mai kunnen ji, yă ji.

16“Da me zan kwatanta wannan zamani? Suna kama da yara da suke zaune a kasuwa, suna kiran juna, suna cewa,

17“ ‘Mun yi muku busa,

ba ku kuwa yi rawa ba,

mun rera waƙar makoki,

ba ku kuwa yi makoki ba.’

18Gama Yohanna Mai Baftisma ya zo ba ya ciye-ciye, ba ya shaye-shaye, sai suka ce, ‘Ai, yana da aljani.’ 19Ɗan Mutum ya zo yana ciye-ciye, yana shaye-shaye, sai suka ce, ‘Ga mai haɗama da kuma mashayi, abokin masu karɓar haraji da masu zunubi.’ Amma akan tabbatar da hikima ta wurin ayyukanta.”

Kaiton biranen da ba su tuba ba

(Luka 7.18-35)

20Sai Yesu ya fara yin tir da biranen da aka yi yawancin ayyukansa na banmamaki, don ba su tuba ba. 21“Kaitonki, Korazin! Kaitonki, Betsaida! Da a ce ayyukan banmamakin da aka yi a cikinki ne aka yi a Taya da Sidon, da tuni sun tuba sanye da rigar makoki da toka. 22Amma ina gaya muku, za a fi jin tausayin Taya da Sidon a ranar shari’a, fiye da ku. 23Ke kuma Kafarnahum, za a ɗaga ki sama ne? A’a, za ki gangara zuwa zurfafa ne. Da a ce ayyukan banmamakin da aka yi a cikinki ne a aka yi a Sodom, da tana nan har yă zuwa yau. 24Amma ina gaya miki, za a fi jin tausayin Sodom fiye da ke a ranar shari’a.”

Hutu domin waɗanda suka gaji

(Luka 10.13-15)

25A wannan lokaci sai Yesu ya ce, “Ina yabonka, Uba, Ubangijin sama da ƙasa, gama ka ɓoye waɗannan abubuwa ga masu hikima da masu ilimi, ka kuma bayyana su ga ƙananan yara. 26I, Uba, gama wannan shi ne abin da ka ji daɗin yi.

27“Dukan kome Ubana ya danƙa mini. Ba wanda ya san Ɗan sai dai Uban, ba kuma wanda ya san Uban, sai dai Ɗan da kuma waɗanda Ɗan ya so yă bayyana musu shi.

28“Ku zo gare ni, dukanku da kuka gaji kuke kuma fama da kaya, zan kuwa ba ku hutu. 29Ku ɗauki karkiyata a kanku, ku kuma yi koyi da ni, gama ni mai tawali’u ne marar girman kai, za ku kuwa sami hutu don rayukanku. 30Gama karkiyata mai sauƙi ce, kayana kuma marasa nauyi ne.”

Chinese Contemporary Bible (Simplified)

马太福音 11:1-30

耶稣和施洗者约翰

1耶稣嘱咐完十二个门徒,就离开那里,到附近的城镇传道和教导人。

2约翰在监狱中听到基督所做的事,就差两个门徒去问祂: 3“你就是那位我们所等候的救主吗?还是我们要等别人呢?”

4耶稣回答说:“你们回去把所见所闻告诉约翰5就是瞎子看见,瘸子走路,麻风病人得洁净,聋子听见,死人复活,穷人听到福音。 6凡对我没有失去信心的人有福了!”

7他们离开后,耶稣对众人谈起约翰,说:“你们从前去旷野要看什么呢?看随风摇动的芦苇吗? 8如果不是,你们到底想看什么?是看穿绫罗绸缎的人吗?那些穿绫罗绸缎的人生活在王宫里。 9你们究竟想看什么?看先知吗?是的,我告诉你们,他不只是先知。 10圣经上说,‘看啊,我要差遣我的使者在你前面为你预备道路’,这里所指的就是约翰11我实在告诉你们,凡妇人所生的,没有一个兴起来比施洗者约翰大,然而天国里最微不足道的也比他大。

12“从施洗者约翰到现在,天国一直在强劲地扩展着,强劲的人要抓住它。 13因为到约翰为止,所有的先知和律法都在预言天国的事。 14如果你们愿意接受,约翰就是那要来的以利亚15有耳可听的都应该留心听。

16“这个世代的人好像什么呢?他们好像一群在街上玩耍的儿童对别的孩子说,

17“‘我们吹娶亲的乐曲,

你们不跳舞;

我们唱送葬的哀歌,

你们不悲伤。’

18约翰来了,也不吃也不喝,他们就说他被鬼附身。 19人子来了,又吃又喝,他们就说祂是贪吃好酒之徒,与税吏和罪人为友。然而智慧会在她的作为上得到验证。”

不肯悔改的城

20那时,耶稣开始责备一些城镇,因为祂在那里行了许多神迹,当地的居民仍不肯悔改。 21祂说:“哥拉汛啊,你大祸临头了!伯赛大啊,你大祸临头了!我在你们当中所行的神迹,如果行在泰尔西顿,那里的人早就身披麻衣,头蒙灰尘,悔改了。 22所以我告诉你们,在审判之日,你们将比泰尔西顿受更重的刑罚!

23迦百农啊,你将被提升到天上吗?不!你将被打落到阴间。因为若把在你那里所行的神迹行在所多玛,它肯定会存留到今天。 24所以我告诉你们,在审判之日,你们将比所多玛受更重的刑罚!”

劳苦者得安息

25那时,耶稣说:“父啊,天地的主,我颂赞你,因为你把这些事向聪明、有学问的人隐藏起来,却启示给像孩童一般的人。 26父啊,是的,这正是你的美意。 27我父将一切交给了我。除了父,没有人认识子;除了子和受子启示的人,没有人认识父。

28“所有劳苦困乏、背负重担的人啊,到我这里来吧!我要赐给你们安息。 29我心柔和谦卑,你们要负我的轭,向我学习,这样你们的心灵必得享安息。 30因为我的轭容易负,我的担子很轻省。”