Kolossiyawa 4 – HCB & CRO

Hausa Contemporary Bible

Kolossiyawa 4:1-18

1Masu bayi, ku riƙe bayinku da kyau da kuma daidai, domin kun san cewa ku ma kuna da Ubangiji a sama.

Ƙarin umarnai

2Ku nace da yin addu’a, kuna zaman tsaro da kuma godiya. 3Ku kuma yi mana addu’a, mu ma, don Allah yă buɗe ƙofa saboda saƙonmu, don mu iya yin shelar asirin Kiristi, wanda saboda shi nake cikin sarƙoƙi. 4Ku yi addu’a yadda zan yi shelarsa, yadda ya kamata. 5Ku zama masu hikima a yadda kuke ma’amala da waɗanda suke ba masu bi ba; ku kuma yi amfani da kowane zarafi. 6Bari maganarku kullum ta zama da ladabi da kuma daɗin ji, domin ku san amsar da ta dace ku ba wa kowa.

Gaisuwa ta ƙarshe

7Tikikus shi ne ƙaunataccen ɗan’uwan nan, wanda ya yi aiki da aminci a hidimar Ubangiji tare da mu, zai kuwa faɗa muku dukan labari game da ni. 8Ina aikansa shi a gare ku musamman domin ku san yadda muke, yă kuma ƙarfafa muku zuciya. 9Yana zuwa tare da Onesimus, ƙaunatacce da kuma amintaccen mai bin nan, wanda yake ɗaya daga cikinku. Za su gaya muku dukan abin da yake faruwa a nan.

10Aristarkus yana a kurkuku tare da ni. Yana gaishe ku, haka ma Markus, wanda kakansa ɗaya ne da Barnabas. (Shi ne na riga na yi magana a kansa, na ce muku in ya zo, ku karɓe shi hannu biyu-biyu.)

11Yesu, wannan da muke kira Yustus, shi ma yana gaisuwa. Waɗannan ne kaɗai Yahudawa masu bi a cikin abokan aikina saboda mulkin Allah. Sun kuma zama da taimako a gare ni.

12Efafaras naku, mai hidimar Kiristi Yesu, yana gaisuwa. Kullum yana addu’a dominku sosai, don ku san cikakken abin da Allah yake so ku yi don kuma ku yi shi cikakke. 13Na tabbatar muku, cewa yana aiki ƙwarai dominku da kuma domin waɗanda suke a Lawodiseya da Hiyerafolis.

14Luka ƙaunataccen likitan nan, da kuma Demas suna gaishe ku.

15Ku miƙa gaisuwata ga ’yan’uwan da suke a Lawodiseya, musamman ga Nimfa da kuma ikkilisiyar da take taru a gidanta.

16Bayan an karanta muku wannan wasiƙa, ku tabbata an karanta ta kuma a ikkilisiyar Lawodiseyawa; ku ma ku karanta wasiƙar da ta zo daga Lawodiseya.

17Ku faɗa wa Arkiffus yă tabbata ya ƙarasa aikin da ya karɓa cikin Ubangiji.

18Ni Bulus ne nake rubuta muku wannan gaisuwa da hannuna. Ku tuna da sarƙoƙina. Alherin Allah yă kasance tare da ku.

Knijga O Kristu

Kološanima 4:1-18

1Gospodari, postupajte pravedno i pošteno prema svojim robovima. Ne zaboravite da i vi imate Gospodara—na nebu!

Poticaj na molitvu

2Molite se ustrajno i budno, sa zahvalnošću. 3Molite se i za nas, da nam Bog otvori vrata kako bismo mogli navješćivati Kristovo otajstvo zbog kojega sam u okovima 4te da ga navijestim onako kako treba.

5Mudro postupajte prema onima koji su vani; koristite svaku prigodu da činite dobro. 6Neka vaše riječi uvijek budu ljubazne, solju začinjene, da znate što kome treba reći.

Posljednje napomene i pozdravi

7Moj voljeni brat Tihik, vjerni sluga Gospodnji, ispričat će vam sve o meni. 8Šaljem ga k vama baš zato da znate kako smo i da vas ohrabri. 9Šaljem vam i vjernoga, dragog brata Onezima, vašega zemljaka. On i Tihik ispričat će vam kako je ovdje.

10Pozdravlja vas Aristarh, koji je sa mnom u zatvoru, te Barnabin nećak Marko, za kojega sam vas već prije uputio da ga lijepo primite dođe li k vama. 11Pozdravlja vas i Isus, kojega zovemo Just. To su jedini moji suradnici na kraljevstvu Božjemu koji su židovskoga podrijetla. Oni su mi bili utjeha.

12Pozdravlja vas vaš zemljak Epafra, sluga Krista Isusa. On se uvijek žarko moli za vas da, prema Božjoj volji, budete zreli i čvrsti u vjeri. 13Zaista vam mogu reći da se svojski trudi za vas, kao i za kršćane u Laodiceji i u Hierapolu.

14Pozdravljaju vas dragi liječnik Luka i Dema. 15Pozdravite braću i sestre u Laodiceji te Nimfu i Crkvu koja se sastaje u njezinu domu.

16Kad pročitate ovo pismo, neka ga pročitaju i u laodicejskoj Crkvi, a vi pročitajte ono koje sam njima napisao. 17Arhipu recite da obavlja službu koju mu je Gospodin dao.

18Evo i pozdrava mojom, Pavlovom rukom.

Sjećajte se mojih okova.

Neka je s vama Božja milost.