Ibraniyawa 7 – Hausa Contemporary Bible HCB

Hausa Contemporary Bible

Ibraniyawa 7:1-28

Melkizedek firist

1Wannan Melkizedek sarkin Salem ne da kuma firist na Allah Mafi Ɗaukaka. Shi ne ya sadu da Ibrahim ya albarkace shi sa’ad da Ibrahim ya dawowa daga cin nasara a bisa sarakuna, 2Ibrahim kuwa ya ba shi kashi ɗaya bisa goma na kome. Ma’anar sunan Melkizedek ita ce, “sarkin adalci.” Amma da yake Salem yana nufin “salama,” shi kuma “Sarkin salama” ne. 3Ba shi da mahaifi ko mahaifiya, ba shi da asali, ba shi da farko ko ƙarshe, shi dai kamar Ɗan Allah ne kuma firist ne har abada.

4Ku dubi irin girman da Melkizedek mana. Ko kakanmu Ibrahim ma ya ba shi kashi ɗaya bisa goma na ganima! 5Yanzu doka ta umarci zuriyar Lawi waɗanda suka zama firistoci su karɓi kashi ɗaya bisa goma daga wurin mutane, wato, ’yan’uwansu, ko da yake ’yan’uwansu zuriyar Ibrahim ne. 6Ko da yake Melkizedek ba daga zuriyar Lawi ba ne, duk da haka Ibrahim ya ba shi kashi ɗaya bisa goma na abin da yake da shi, Melkizedek kuwa ya sa masa albarka, shi da aka yi wa alkawura. 7Kowa ya sani cewa na gaba shi yake sa wa na baya albarka. 8Firistoci ake ba wa kashi ɗaya bisa goma na abin da mutane suke samu. Amma dukan firistoci sukan mutu, sai dai Melkizedek, kuma nassi ya ce yana da rai. 9Ana ma iya cewa zuriyar Lawi, mai karɓar kashi ɗaya bisa goma daga mutane, ya ba da kashi ɗaya bisa goma ta wurin Ibrahim, 10wannan ya kasance haka domin an haifi Lawi daga baya a iyalin Ibrahim wanda ya ba wa Melkizedek kashi ɗaya bisa goma.

Yesu kamar Melkizedek ne

11Ko da yake Dokar Musa ta ce dole firistoci su kasance zuriyar Lawi, waɗannan firistoci ba su iya sa wani yă zama cikakke ba. Saboda akwai bukata wani firist kamar Melkizedek ya zo, a maimakon wani daga iyalin Haruna. 12Gama in aka canja yadda ake zaɓan firist, dole a canja Dokar ita ma. 13Mutumin da muke wannan zance a kai, ai, shi na wata kabila ce dabam, wadda ba wani daga kabilar da ya taɓa yin hidima a bagade. 14Kowa ya san cewa Ubangijinmu ya fito ne daga zuriyar Yahuda ne, kuma Musa bai taɓa ce firistoci za su fito daga wannan kabila ba. 15Canjin nan a Dokar Allah ya ƙara fitowa fili da wani firist dabam wanda yake kamar Melkizedek ya bayyana. 16Ya zama firist ne ba saboda ya cika wata ƙa’ida ta zama zuriyar Lawi ba, sai dai bisa ga ikon ran da ba a iya hallakawa. 17Gama nassi ya ce,

“Kai firist ne na har abada,

bisa ga tsarin Melkizedek.”7.17 Zab 110.4

18Ta haka aka kawar da ƙa’ida marar ƙarfi da kuma marar amfani 19(gama doka ba tă mai da wani abu cikakke ba), yanzu kuwa bege mafi kyau ya ɗauki matsayinta. Ta haka kuma muka matso kusa da Allah.

20Ba kuwa da rashin rantsuwa aka yi haka ba. Waɗansu sun zama firistocin ba tare da wata rantsuwa ba, 21shi wannan ya zama firist ta wurin rantsuwar da Allah ya yi da ya ce masa,

“Ubangiji ya rantse,

ba kuwa zai canja zuciyarsa ba,

‘Kai firist ne na har abada.’ ”7.21 Zab 110.4

22Saboda wannan rantsuwa, Yesu ya zama tabbacin alkawari mafi kyau.

23To, akwai waɗannan firistoci da yawa, da yake mutuwa ta hana su cin gaba da aikin zaman firist; 24amma Yesu ba zai mutu ba, don haka zai zama firist har abada. 25Saboda haka ya iya ba da ceto gaba ɗaya ga masu zuwa wurin Allah ta wurinsa, gama kullum a raye yake saboda yă yi roƙo dominsu.

26Irin wannan babban firist ne muke bukata, shi mai tsarki ne, marar aibi, mai tsabta, ba kamar mu masu zunubi ba sam. An ɗaukaka shi fiye da kome a sama. 27Ba ya bukata yă yi ta miƙa hadayu kowace rana saboda zunubansa, sa’an nan saboda zunuban mutane kamar sauran firistoci. Ya miƙa hadaya sau ɗaya tak, sa’ad da ya miƙa kansa. 28Gama doka takan naɗa babban firist a cikin mutane masu kāsawa; amma rantsuwar da ta zo bayan dokar, ta naɗa Ɗan, wanda aka mai da shi cikakke har abada.