Ibraniyawa 3 – HCB & NIV

Hausa Contemporary Bible

Ibraniyawa 3:1-19

Yesu ya fi Musa

1Saboda haka, ’yan’uwa tsarkaka, waɗanda suke da rabo a kiran nan na sama, ku kafa tunaninku a kan Yesu, manzo da kuma babban firist wanda muke shaidawa. 2Ya yi aminci ga wanda ya naɗa shi, kamar yadda Musa ya yi aminci ga dukan gidan Allah. 3An ga Yesu ya cancanci girma fiye da Musa, kamar yadda mai ginin gida ya fi gidan daraja. 4Gama kowane gida yana da wanda ya gina shi, amma maginin dukan abu Allah ne. 5Musa ya yi aminci a matsayin bawa cikin dukan gidan Allah, yana ba da shaida a kan abubuwan da za a faɗa nan gaba. 6Amma Kiristi mai aminci ne kamar ɗa a gidan Allah. Mu kuwa gidansa ne, in muka tsaya gabanmu gadi da kuma begen da muke taƙama a kai.

Gargaɗi a kan rashin bangaskiya

7Kamar dai yadda Ruhu Mai Tsarki ya ce,

“Yau, in kuka ji muryarsa,

8kada ku taurare zukatanku,

yadda kuka yi a tawayen nan,

a lokacin gwaji a hamada,

9inda kakanninku suka gwada ni, suka kuma gwada ni,

ko da yake a cikin shekaru arba’in sun ga abin da na yi.

10Shi ya sa na yi fushi da wancan zamani,

na kuma ce, ‘Kullum zukatansu a karkace suke,

ba su kuma san hanyoyina ba.’

11Saboda haka na yi rantsuwa a cikin fushina,

‘Ba za su taɓa shiga hutuna ba.’ ”3.11 Zab 95.7-11

12Ku lura fa, ’yan’uwa, cewa kada waninku yă kasance da zuciya mai zunubi marar bangaskiya da takan juye daga bin Allah mai rai. 13Sai dai ku ƙarfafa juna kullum, muddin akwai lokacin da ana ce da shi Yau, don kada waninku yă zama mai taurin zuciya ta wurin ruɗun zunubi. 14Mu masu tarayya ne da Kiristi idan mun riƙe bangaskiyarmu da ƙarfi daga farko har zuwa ƙarshe. 15Kamar yadda aka faɗa cewa,

“Yau, in kuka ji muryarsa,

kada ku taurare zukatanku

kamar yadda kuka yi a tawayen nan.”3.15 Zab 95.7,8

16Su wane ne suka ji suka kuma yi tawaye? Ba su ne duk waɗanda Musa ya bi da su daga Masar ba? 17Da su wane ne kuwa ya yi fushi har shekaru arba’in? Ba da waɗanda suka yi zunubi, waɗanda suka mutu a hamada ba? 18Kuma ga su wane ne Allah ya rantse cewa ba za su taɓa shiga hutunsa ba, in ba ga marasa biyayyan nan ba? 19Saboda haka mun ga cewa ba su iya shiga ba, saboda rashin bangaskiyarsu ne.

New International Version

Hebrews 3:1-19

Jesus Greater Than Moses

1Therefore, holy brothers and sisters, who share in the heavenly calling, fix your thoughts on Jesus, whom we acknowledge as our apostle and high priest. 2He was faithful to the one who appointed him, just as Moses was faithful in all God’s house. 3Jesus has been found worthy of greater honor than Moses, just as the builder of a house has greater honor than the house itself. 4For every house is built by someone, but God is the builder of everything. 5“Moses was faithful as a servant in all God’s house,”3:5 Num. 12:7 bearing witness to what would be spoken by God in the future. 6But Christ is faithful as the Son over God’s house. And we are his house, if indeed we hold firmly to our confidence and the hope in which we glory.

Warning Against Unbelief

7So, as the Holy Spirit says:

“Today, if you hear his voice,

8do not harden your hearts

as you did in the rebellion,

during the time of testing in the wilderness,

9where your ancestors tested and tried me,

though for forty years they saw what I did.

10That is why I was angry with that generation;

I said, ‘Their hearts are always going astray,

and they have not known my ways.’

11So I declared on oath in my anger,

‘They shall never enter my rest.’ ”3:11 Psalm 95:7-11

12See to it, brothers and sisters, that none of you has a sinful, unbelieving heart that turns away from the living God. 13But encourage one another daily, as long as it is called “Today,” so that none of you may be hardened by sin’s deceitfulness. 14We have come to share in Christ, if indeed we hold our original conviction firmly to the very end. 15As has just been said:

“Today, if you hear his voice,

do not harden your hearts

as you did in the rebellion.”3:15 Psalm 95:7,8

16Who were they who heard and rebelled? Were they not all those Moses led out of Egypt? 17And with whom was he angry for forty years? Was it not with those who sinned, whose bodies perished in the wilderness? 18And to whom did God swear that they would never enter his rest if not to those who disobeyed? 19So we see that they were not able to enter, because of their unbelief.