Ibraniyawa 2 – Hausa Contemporary Bible HCB

Hausa Contemporary Bible

Ibraniyawa 2:1-18

Gargaɗi don a mai da hankali

1Dole mu ƙara mai da hankali sosai ga abubuwan da muka ji, don kada mu kauce. 2Gama in saƙon da aka faɗi ta bakin mala’iku ya zama tabbatacce, kuma kowane ƙeta umarni da rashin biyayya suka karɓi sakamakonsu da ya dace, 3yaya za mu tsira in muka ƙyale irin wannan babban ceto? Wannan ceto, wanda Ubangiji ne ya fara sanar, aka kuma tabbatar mana ta bakin waɗanda suka ji shi. 4Allah shi ma ya shaida ta wurin alamu, abubuwan banmamaki da mu’ujizai iri-iri, da kuma baye-bayen Ruhu Mai Tsarki da aka rarraba bisa ga nufinsa.

An yi Yesu kamar ’yan’uwansa

5Ba ga mala’iku ba ne ya sa su yi mulkin duniya mai zuwa, wanda muke magana a kai ba. 6Amma akwai wani wurin da wani ya shaida cewa,

“Mene ne mutum, da kake tuna da shi,

ɗan mutum da kake kula da shi?

7Ka sa shi ƙasa kaɗan da darajar mala’iku;

ka naɗa shi da ɗaukaka da girma,

8ka kuma sa kome a ƙarƙashin ƙafafunsa.”2.8 Zab 8.4-6

Ta wurin sa kome a ƙarƙashinsa, Allah bai bar wani abu da bai sa a ƙarƙashinsa ba. Duk da haka a yanzu ba mu ga kowane abu a ƙarƙashinsa ba. 9Sai dai muna ganin Yesu, wanda aka mai da shi ƙasa kaɗan da darajar mala’iku, yanzu kuwa an naɗa shi da ɗaukaka da girma domin yă sha wahalar mutuwa, domin ta wurin alherin Allah yă ɗanɗana mutuwa saboda kowa.

10Ta wurin kawo ’ya’ya masu yawa zuwa ga ɗaukaka, ya dace cewa Allah, wanda dominsa da kuma ta wurinsa ne kome yake kasancewa, ya sa tushen cetonsu yă zama cikakke ta wurin shan wahala. 11Da shi wanda yake tsarkake mutane da kuma su waɗanda ake tsarkakewa duk ’yan iyali ɗaya ne. Saboda haka Yesu ba ya kunyan kiransu ’yan’uwansa. 12Ya ce,

“Zan sanar da sunanka ga ’yan’uwana;

a gaban jama’a zan rera yabonka.”2.12 Zab 22.22

13Har wa yau ya ce,

“Zan dogara gare shi.”2.13 Ish 8.17

Ya kuma ce,

“Ga ni, da ’ya’yan da Allah ya ba ni.”2.13 Ish 8.18

14Da yake ’ya’yan suna da nama da jini, shi ma sai ya ɗauki kamanninsu na mutum domin ta wurin mutuwarsa yă hallaka wanda yake riƙe da ikon mutuwa, wato, Iblis 15ya kuma ’yantar da waɗanda dukan rayuwarsu tsoron mutuwa ya riƙe su cikin bauta. 16Gama tabbatacce ba mala’iku ne ya taimaka ba, sai dai zuriyar Ibrahim. 17Saboda wannan dole a mai da shi kamar ’yan’uwansa ta kowace hanya, domin yă zama babban firist mai aminci da mai jinƙai cikin hidima ga Allah, yă kuma miƙa hadayar sulhu saboda zunuban mutane. 18Domin shi kansa ya sha wahala sa’ad da aka gwada shi, yana iya taimakon waɗanda ake yi wa gwaji.