Galatiyawa 3 – HCB & CCB

Hausa Contemporary Bible

Galatiyawa 3:1-29

Bangaskiya ko kiyaye doka

1Ya ku Galatiyawa marasa azanci! Wa ya ruɗe ku? A idanunku aka bayyana Yesu Kiristi gicciyeyye a sarari. 2Zan so in san abu guda tak daga gare ku. Kun karɓi Ruhu ta wurin kiyaye Doka ne, ko kuwa ta wurin gaskata abin da kuka ji? 3Ashe, rashin azancinku har ya kai ga haka? Bayan kun fara da Ruhu, a yanzu kuma da halin mutuntaka za ku ƙarasa? 4Ashe, wahaloli dabam-dabam da kuka sha sun zama a banza ke nan? Haka zai yiwu kuwa? 5Allah ya ba ku Ruhunsa yana kuma aikata ayyukan banmamaki a cikinku saboda kuna kiyaye Doka ne, ko kuwa domin kuna gaskatawa abin da kuka ji ne? 6Ku dubi Ibrahim mana, “Ya gaskata Allah, aka kuwa lissafta wannan adalci ne a gare shi.”3.6 Far 15.6

7Ku sani fa, waɗannan waɗanda suka gaskata, ’ya’yan Ibrahim ne. 8Nassi ya hanga cewa Allah zai kuɓutar da Al’ummai ta wurin bangaskiya, ya kuwa sanar wa Ibrahim wannan bisharar tun kafin lokaci yă yi cewa, “Dukan al’ummai za su sami albarka ta wurinka.”3.8 Far 12.3; Far 18.18; Far 22.18 9Saboda haka waɗanda suke da bangaskiya sun sami albarka tare da Ibrahim, mutumin bangaskiya.

10Dukan waɗanda suka dogara ga kiyaye Doka la’anannu ne, gama a rubuce yake cewa, “La’ananne ne duk wanda bai ci gaba da yi dukan abubuwan da aka rubuta a Littafin Doka ba.”3.10 M Sh 27.26 11A fili yake ba wanda zai kuɓuta a gaban Allah ta wurin Doka, domin “Mai adalci zai rayu ta wurin bangaskiya.”3.11 Hab 2.4 12Doka ba tă dangana ga bangaskiya ba; a maimakon haka, “Mutumin da ya aikata waɗannan abubuwa zai rayu ta wurinsu.”3.12 Fir 18.5 13Kiristi ya fanshe mu daga la’anar Doka ta wurin zama la’ana saboda mu, gama a rubuce yake cewa, “La’ananne ne duk wanda aka rataye a kan itace.”3.13 M Sh 21.23 14Ya fanshe mu domin albarkar da aka yi wa Ibrahim yă zo ga Al’ummai, ta wurin Kiristi Yesu, domin ta wurin bangaskiya mu karɓi alkawarin Ruhu.

Doka da kuma alkawari

15’Yan’uwa, bari in yi muku misali da rayuwarmu ta yau da kullum. Kamar dai yadda ba mai kawarwa ko yă ƙara wani abu cikin alkawarin da mutane suka kafa, haka yake a wannan batu. 16Alkawaran nan fa ga Ibrahim ne aka faɗa da kuma wani zuriyarsa. Nassi bai ce, “da zuriyoyi ba” wanda ya nuna kamar mutane da yawa, amma “ga zuriyarka,”3.16 Far 12.7; Far 13.15; Far 24.7 wanda yake nufin mutum ɗaya, wanda shi ne Kiristi. 17Abin da nake nufi shi ne, Dokar da aka shigar ita bayan shekaru 430, ba tă kawar da alkawarin da Allah ya yi tun dā ba. 18Gama da a ce gādon yă dangana a kan doka ne, ai, da ba zai dangana a kan alkawari ba; amma Allah cikin alherinsa ya ba wa Ibrahim gādon ta wurin alkawari.

19To, don me aka kawo Doka? An yi ƙari da Doka ne don fitowa da laifi fili har kafin na zuriyan nan ya zo, wanda aka yi wa alkawarin, an ba da doka ta wurin mala’iku ne, aka kuma danƙa ta a hannun matsakanci. 20Kuma akan bukaci wani a tsakani ne idan da mutum biyu ake zance, Allah kuwa ɗaya ne.

21To, Dokar ce tana gāba da alkawaran Allah ke nan? Sam, ko kaɗan! Gama da a ce an ba da Dokar da tana iya ba da rai, tabbatacce, da sai a sami adalci ta wurin Doka. 22Amma Nassi ya kulle kome a ƙarƙashin ikon zunubi, domin abin da aka yi alkawarin nan, da ake bayar ta wurin bangaskiya a cikin Yesu Kiristi, a ba da shi ga waɗanda suka gaskata.

’Ya’yan Allah

23Kafin bangaskiyan nan tă zo, mun kasance a daure a kurkuku a ƙarƙashin Doka, a kulle sai da bangaskiyar da za tă zo ta bayyana. 24Ta haka aka sa Dokar ta zama jagorarmu zuwa ga Kiristi don mu sami kuɓuta ta wurin bangaskiya. 25Yanzu da bangaskiya ta zo, ba sauran zamanmu a ƙarƙashin Doka.

26Dukanku ’ya’yan Allah ne ta wurin bangaskiya cikin Kiristi Yesu. 27Gama dukanku da aka yi muku baftisma cikin Kiristi, kuna sanye da Kiristi ke nan. 28Babu bambanci tsakanin mutumin Yahuda da mutumin Al’ummai, bawa da ’yantacce, namiji da ta mace, gama dukanku ɗaya ne cikin Kiristi Yesu. 29In kuwa ku na Kiristi ne, to, ku zuriyar Ibrahim ne, magāda kuma bisa ga alkawarin nan.

Chinese Contemporary Bible (Simplified)

加拉太书 3:1-29

行律法与信基督

1无知的加拉太人啊!谁又迷惑了你们呢?耶稣基督被钉在十字架上的事早就像一幅画一样展现在你们眼前了。 2我只想问,你们领受了圣灵是靠遵行律法呢,还是因为相信所听见的福音呢? 3你们既然靠圣灵开始了基督徒的生活,现在却想靠肉体达到纯全吗?你们就这么无知吗? 4你们受了许多苦,难道都是徒然的吗?都白受了吗? 5上帝将圣灵赐给你们又在你们中间行神迹,是因为你们遵行律法呢,还是因为你们相信所听到的福音呢?

6圣经上说:“亚伯拉罕信上帝,就被算为义人。” 7因此,你们要明白,那些信上帝的人才是亚伯拉罕的子孙。 8圣经早就指明,上帝要叫外族人因信而被称为义人,祂预先将福音传给亚伯拉罕,说:“万国必因你而蒙福。” 9所以那些信上帝的人必和有信心的亚伯拉罕一同得到祝福。

10凡以遵行律法为本的人都在咒诅之下,因为圣经上说:“凡不遵行律法书上一切命令的人必受咒诅。” 11非常明显,没有人能靠遵行律法在上帝面前被称为义人,因为圣经上说:“义人必靠信心而活。” 12律法却不是以信心为本,而是说:“遵行的人必存活。”

13但基督替我们受了咒诅,从而救赎我们脱离了律法的咒诅,因为圣经上说:“凡挂在木头上的人都是受咒诅的。” 14这样,赐给亚伯拉罕的祝福可以借着基督耶稣临到外族人,使我们也可以借着信得到上帝应许赐给我们的圣灵。

律法与应许

15弟兄姊妹,我举个日常生活中的例子。世人的合约一经双方签订之后,就不能作废,也不能加添。 16上帝曾向亚伯拉罕和他的后裔赐下应许,不过这里没有说“后裔们”——指许多人,而是说“你的后裔”——指一个人,就是基督。 17我的意思是:四百三十年后颁布的律法不会废除上帝先前立下的约,以致应许落空。 18倘若我们是靠守律法去承受产业,我们就不是倚靠上帝的应许。但上帝是凭应许把产业赐给了亚伯拉罕

19那么,为什么会有律法呢?律法是为了使人知罪而颁布的,等那位承受应许的后裔来到后,律法的任务就完成了。律法是通过天使交给一位中间人颁布的。 20中间人代表双方,但上帝则单方面赐下应许。

21这样看来,上帝的律法和上帝的应许是否互相矛盾呢?当然不是!如果赐下的律法能带给人生命,人就可以靠律法成为义人了。 22但圣经说万物都在罪的权势下,为要使那些相信的人因为相信耶稣基督而得到应许3:22 因为相信耶稣基督而得到应许”或译“因为耶稣基督的信实而得到应许”。

23信耶稣的时代3:23 信耶稣的时代”希腊文是“信心”,下同25节。还没有来临以前,律法暂时监管我们。等到信耶稣之道显明出来后,律法就不再监管我们。 24因此,律法是我们的监护人,负责引领我们归向基督,使我们可以因信而被称为义人。 25现在信耶稣的时代已经来临,我们不再受律法监管。 26你们都借着信基督耶稣而成为上帝的儿女, 27因为你们受洗归入基督就是披戴基督3:27 披戴基督”是个隐喻,主要的意思是“像基督”,象征有基督的生命与品格。28从此不再分犹太人和希腊人,自由人和奴隶,男人和女人,因为你们都在基督耶稣里合而为一了。 29你们若属于基督,就是亚伯拉罕的后裔,都是照着上帝的应许承受产业的人。