Filibbiyawa 4 – HCB & JCB

Hausa Contemporary Bible

Filibbiyawa 4:1-23

1Saboda haka ’yan’uwana, ku da nake ƙauna, nake kuma marmarin ganinku, ku da kuke farin cikina da kuma rawanina, ku dāge ga Ubangiji, ya ku ƙaunatattuna!

2Ina roƙon Yuwodiya ina kuma roƙon Sintike, su yi zaman lafiya da juna saboda su na Ubangiji ne. 3I, ina kuma roƙonka, abokin famata, ka taimaki matan nan waɗanda suka yi fama aikin bishara tare da ni, haka ma Kilemen da kuma sauran abokan aikina, waɗanda sunayensu suna cikin littafin rai.

Gargaɗi

4Ku yi farin ciki a cikin Ubangiji kullum. Ina sāke gaya muku ku yi farin ciki! 5Bari kowa yă kasance da sauƙinkai. Ubangiji ya yi kusan zuwa. 6Kada ku damu game da kome sai dai a cikin abu duka, ku gabatar da roƙe-roƙenku ga Allah ta wurin addu’a da roƙo, tare da godiya. 7Salamar Allah, wadda ta wuce dukan fahimta, za tă tsai da zukatanku da tunaninku cikin Kiristi Yesu.

8A ƙarshe, ’yan’uwa, duk abin da yake na gaskiya, duk abin da yake na girmamawa, duk abin da yake daidai, duk abin da yake da tsarki, duk abin da yake kyakkyawa, duk abin da yake na sha’awa, in ma wani abu mafifici ne, ko ya cancanci yabo, ku yi tunani a kan irin abubuwan nan. 9Duk abin da kuka koya ko kuka karɓa ko kuka ji daga wurina, ko kuka gani a cikina, ku yi aiki da shi. Allah na salama kuma zai kasance tare da ku.

Godiya saboda kyautansu

10Na yi farin ciki sosai ga Ubangiji don yanzu kun sāke nuna kun kula da ni. Ko da yake dā ma kun kula da ni sai dai ba ku sami dama ku nuna mini ba. 11Ba na faɗin haka domin ina cikin bukata, gama na koya yadda zan gamsu a cikin kowane hali. 12Na san mene ne zaman rashi, na kuma san mene ne zaman samu. Zan iya zama cikin kowane hali, ko cikin ƙoshi ko cikin yunwa, ko cikin yalwa ko kuma cikin fatara. 13Ina iya yin kome ta wurin wannan wanda yake ba ni ƙarfi.

14Duk da haka kun kyauta da kuka yi tarayya da ni cikin wahalolina. 15Ban da haka, kamar yadda ku Filibbiyawa kuka sani, a farkon kwanakin da kuka ji bishara, sa’ad da na tashi daga Makidoniya, babu wata ikkilisiyar da tă yi tarayya da ni a fannin bayarwa da karɓa, sai ku kaɗai; 16gama ko sa’ad da nake a Tessalonika ma, kun aiko mini da taimako sau da sau sa’ad da nake cikin bukata. 17Ba cewa ina neman kyauta ba ne, sai dai ina neman abin da za a ƙara a kan ribarku. 18An biya ni duka, biyan da ya wuce misali. Bukatata ta biya, da yake na karɓi kyautarku da kuka aiko ta hannun Afaforiditus. Baiwa mai ƙanshi, hadaya abar karɓa, mai faranta wa Allah rai. 19Allahna kuma zai biya dukan bukatunku bisa ga ɗaukakar wadatarsa cikin Kiristi Yesu.

20Ɗaukaka ta tabbata ga Allahnmu da Ubanmu har abada abadin. Amin.

Gaisuwa ta ƙarshe

21Ku gai da dukan tsarkaka cikin Kiristi Yesu.

’Yan’uwan da suke tare da ni suna gaishe ku.

22Dukan tsarkaka suna gaishe ku, musamman waɗanda suke na gidan Kaisar.

23Alherin Ubangiji Yesu Kiristi yă kasance da ruhunku. Amin.4.23 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā ba su da Amin.

Japanese Contemporary Bible

ピリピ人への手紙 4:1-23

4

主にあって喜びなさい

1愛する兄弟(信仰を同じくする者)たち。私はあなたがたに、ぜひ会いたいと願っています。あなたがたは私の喜びであり、私の働きが結んだ実なのですから。愛する皆さん。どうかいつまでも、主に対して真実であってください。

2ここで、愛する二人の女性ユウオデヤとスントケにお願いします。どうか、主の助けによってけんかをやめ、もとどおり仲よくなってください。 3私の真実の協力者である皆さん。あなたがたにもお願いします。彼女たちを助けてやってください。福音を宣べ伝えるために、私と手を組んで働いてくれた人たちだからです。それに彼女たちは、いのちの書に名前が記されているクレメンスやほかの協力者たちとともに、力を合わせて働いてくれたのです。

4いつも主にあって喜びなさい。もう一度言います。喜びなさい。 5自己中心にならず、あなたがたが思いやりにあふれていることを、だれもが知る者になりなさい。主がもうすぐ来られると、いつも意識していなさい。 6何事も心配しないで、どんな時でも神に祈りなさい。そして、祈りに答えてくださる神に感謝しましょう。 7そうすれば、人間の理解をはるかに超えた、すばらしい神の平安を経験します。キリスト・イエスにあって、その平安はあなたがたの心と思いを静め、安らかにしてくれるのです。

8さて皆さん。筆を置く前に、もう一つ申し上げたいことがあります。真実なこと、良いこと、正しいことに注目しなさい。きよいこと、愛すべきことについて思いめぐらし、他の人の長所に目をとめなさい。神を喜び、賛美することばかりを考えなさい。 9私から学んだこと、その行動から教えられたことがあれば、実行しなさい。そうすれば、平和の神が共にいてくださいます。

10あなたがたがまた助けてくれるようになって、どんなに感謝し、主を賛美しているか知れません。あなたがたはいつもできるかぎりのものを私に送ろうと心がけていたのに、機会に恵まれなかったのです。 11生活に困っていたから、こう言うのではありません。私は、物が豊富にあろうとなかろうと、楽しく生きていくすべを学びました。 12無一文の時にも、何でもそろっている時にも、どのように生活すべきか知っています。満腹の時にも空腹の時にも、豊かな時にも貧しい時にも、どんな境遇でも満足する秘訣を身につけました。 13力を与え、強めてくださる方によって、私は、神に求められるどんなことでもできるからです。

14しかし、それにしても、よくぞ困難な状況下にある私を助けてくれました。 15知ってのとおり、福音を携え、初めてあなたがたを訪問した私が、その後マケドニヤを離れて他の地方に向かった時、物をやり取りして協力してくれたのは、あなたがたピリピの教会だけでした。ほかに、そんな教会はありませんでした。 16テサロニケ滞在中でさえ、二度までも、物資を援助してくれました。 17贈り物を感謝するのはもちろんのこと、何よりもうれしいのは、その親切な行いのゆえにあなたがたが受ける、豊かな報いのことです。 18今のところ、必要な物は何でもそろっています。それどころか、必要以上に満たされています。エパフロデトにことづけてくれた贈り物をいただいて、十分すぎるほどです。その贈り物は、神が喜んで受け入れてくださる、香ばしいかおりの供え物です。 19神は、キリスト・イエスが成し遂げてくださったことによるご自身の栄光の富の中から、あなたがたに必要なものをすべて満たしてくださる方です。 20父なる神に、栄光が、とこしえに限りなくありますように。アーメン。

パウロ

追伸

21そちらの信徒一人一人によろしくお伝えください。こちらにいる兄弟たちがよろしくとのことです。 22また、他の信徒もみな、特にカイザル(ローマ皇帝)の宮廷に仕えている人々が、よろしくと言っています。 23どうか、主イエス・キリストの祝福が、あなたがたの霊と共にありますように。