Filibbiyawa 2 – HCB & HHH

Hausa Contemporary Bible

Filibbiyawa 2:1-30

Koyi tawali’un Kiristi

1In kuna da wata ƙarfafawa daga tarayya da Kiristi, in da wata ta’aziyya daga ƙaunarsa, in da wani zumunci da Ruhu, in da juyayi da tausayi, 2to, sai ku sa farin cikina yă zama cikakke ta wurin kasance da hali ɗaya, kuna ƙauna ɗaya, kuna zama ɗaya cikin ruhu da kuma manufa. 3Kada ku yi kome da sonkai ko girman kai, sai dai cikin tawali’u, ku ɗauki waɗansu sun fi ku. 4Bai kamata kowannenku yă kula da sha’anin kansa kawai ba, sai dai yă kula da sha’anin waɗansu ma.

5A cikin dangantakarku da juna, ya kamata halayenku su zama kamar na Kiristi Yesu.

6Wanda, ko da yake cikin ainihin surar Allah yake,

bai mai da daidaitakansa nan da Allah wani abin riƙewa kam-kam ba,

7amma ya mai da kansa ba kome ba,

yana ɗaukan ainihin surar bawa,

aka yi shi cikin siffar mutum.

8Aka kuma same shi a kamannin mutum,

ya ƙasƙantar da kansa

ya kuma zama mai biyayya wadda ta kai shi har mutuwa,

mutuwar ma ta gicciye!

9Saboda haka Allah ya ɗaukaka shi zuwa mafificin wuri

ya kuma ba shi sunan da ya fi dukan sunaye,

10don a sunan Yesu kowace gwiwa za tă durƙusa,

a sama da a ƙasa da kuma a ƙarƙashin ƙasa,

11kowane harshe kuma yă furta cewa Yesu Kiristi Ubangiji ne,

don ɗaukakar Allah Uba.

Haskaka kamar taurari

12Saboda haka, ya abokaina ƙaunatattu, kamar yadda kullum kuke biyayya ba kawai sa’ad da ina nan ba, amma yanzu da ba na nan tare da ku, ku ci gaba da yin ayyukan cetonku da tsoro da kuma rawan jiki, 13gama Allah ne yake aiki a cikinku, don ku nufa ku kuma aikata bisa ga nufinsa mai kyau.

14Ku yi kome ba tare da gunaguni ko gardama ba, 15don ku zama marasa abin zargi, sahihai ’ya’yan Allah, waɗanda ba su da laifi, a zamanin mutane karkatattu, kangararru, waɗanda kuke haskakawa a cikinsu kamar fitilu a duniya 16kuna kuwa cin gaba da riƙe maganar rai domin in yi taƙama a ranar Kiristi cewa ban yi gudu ko fama a banza ba. 17Amma ko da ana tsiyaye jinina kamar hadaya ta sha a kan hadaya da kuma hidimar da take fitowa daga bangaskiyarku, ina murna ina kuma farin ciki da ku duka. 18Haka ma ya kamata ku yi murna ku kuma yi farin ciki tare da ni.

Timoti da Afaforiditus

19Ina sa rai a cikin Ubangiji Yesu cewa zan aika da Timoti zuwa gare ku ba da daɗewa ba, don ni ma in ji daɗi sa’ad da na ji labarinku. 20Ba ni da wani kamar sa, wanda yake da ainihin sha’awa a zaman lafiyarku. 21Gama kowa yana lura da al’amuran kansa ne kawai, ba na Kiristi Yesu ba. 22Amma, ai, kun san darajar Timoti yadda muka yi bautar bishara tare, kamar ɗa da mahaifinsa. 23Saboda haka, ina sa rai, in aike shi da zarar na ga yadda abubuwa suke a nan. 24Ni kuma ina da tabbaci a cikin Ubangiji cewa zan zo ba da daɗewa ba.

25Amma ina gani ya dace in aika da Afaforiditus, ɗan’uwana, abokin aikina da kuma abokin famana, wanda kuma yake ɗan saƙonku, wanda kuka aika domin yă biya mini bukatuna. 26Gama yana marmarin ganinku duka ya kuma damu domin kun ji cewa ya yi rashin lafiya. 27Ba shakka ya yi rashin lafiya, har ya kusa mutuwa. Amma Allah ya nuna masa jinƙai, ba shi kaɗai ba amma har da ni ma, don yă rage mini baƙin ciki kan baƙin ciki. 28Saboda haka na yi niyya ƙwarai in aike shi wurinku, don sa’ad da kuka sāke ganinsa za ku yi murna, ni kuma in rage damuwa. 29Ku marabce shi cikin Ubangiji da farin ciki mai yawa, ku kuma girmama mutane irinsa, 30domin ya kusa yă mutu saboda aikin Kiristi, ya yi kasai da ransa don yă cikasa taimakon da ba ku iya yi mini ba.

Habrit Hakhadasha/Haderekh

אגרת פולוס השליח אל-הפיליפיים 2:1-30

1אם קיים עידוד הדדי כלשהו בין המאמינים, אם אתם אוהבים אותי עד כדי לרצות לעזור לי, אם יש בלבכם רחמים ואהדה, אם יש בעיניכם משמעות כלשהי לעובדה שאנו אחים באמונה וששוכן בנו אותו רוח הקודש, 2אזי דעו לכם שתגרמו לי שמחה אמיתית אם תאהבו איש את רעהו, אם לא תריבו זה עם זה, ואם תעבדו יחד בלב ובדעה אחת למען מטרה אחת.

3אל תהיו אנוכיים, ואל תנסו לעשות רושם על אחרים. היו ענווים, התחשבו באחרים והעריכו אותם יותר מאשר את עצמכם. 4אל תעסקו כל הזמן רק בעניינים שלכם, אלא התעניינו גם באנשים אחרים ובמעשיהם. 5התנהגו עם הזולת כמו שישוע התנהג איתנו: 6למרות שהיה בדמות אלוהים הוא לא דרש את זכויותיו כאלוהים, 7אלא הפשיט מעצמו את כוחו הרב, את ההוד והתהילה, ולבש דמות עבד הדומה לבן־אדם. 8הוא אף השפיל את עצמו כל־כך עד שבחר למות מוות בזוי על הצלב.

9על כן העלהו אלוהים למרומי השמים ונתן לו שם העולה בכבודו על כל שם אחר, 10כדי שבשם ישוע יכרעו כולם ברך וישתחוו לו בשמים, בארץ ומתחת לארץ, 11וכל אדם יודה שישוע הוא האדון, לכבודו של אלוהים האב.

12ידידי היקרים, כשהייתי אצלכם שמעתם בקולי תמיד. עתה כשאני רחוק מכם, אני מבקש שתמשיכו לעשות מעשים טובים שנובעים מישועתכם. שמעו בקול אלוהים ביראה עמוקה, והתרחקו מכל דבר העלול לא למצוא־חן בעיניו. 13כי אלוהים הוא פועל בכם לרצות להישמע לו, והוא גם עוזר לכם למלא את רצונו.

14עשו כל דבר ללא ויכוחים וללא תלונות, 15כדי שאיש לא יוכל לדבר נגדכם. עליכם לחיות חיים פשוטים, טהורים ותמימים, כמו בני אלוהים בתוך עולם של נוכלים ורמאים. עליכם להאיר ולזרוח ביניהם כקרני אור בחשכה, 16ולספר להם על דבר אלוהים – על דבר החיים! אם כך תנהגו, אתגאה בכם בשובו של המשיח אלינו, שכן עבודתי ביניכם לא הייתה לשווא.

17גם אם עלי לשפוך את דמי כנסך על קורבן אמונתכם, כלומר, אם יהיה עלי להקריב את חיי למענכם, אגיל ואשמח עם כל אחד מכם. 18גם אתם צריכים לשמוח איתי על כך.

19אם ירצה השם אשלח אליכם בקרוב את טימותיוס, וכשישוב מביקורו אשמח לשמוע מפיו מה נשמע אצלכם. 20הידעתם שטימותיוס מתעניין בכם יותר מכל אדם אחר? 21נראה שכל אחד אחר דואג רק לעצמו ולתוכניותיו, ולא לתוכניותיו של ישוע המשיח. 22אך מכירים אתם את טימותיוס. בכל הנוגע להפצת הבשורה על המשיח הוא כבן לי. 23אני מקווה לשלחו אליכם ברגע שאדע מה עומד לקרות לי כאן. 24אני בטוח שהאדון יאפשר לי לבקר אתכם בקרוב.

25חושבני כי בינתיים מוטב שאשלח אליכם חזרה את אפפרודיטוס. שלחתם אותו כדי שיעזור לי בענייני, והוא אמנם עזר לי. שנינו היינו ממש כאחים; עבדנו יחד ואף סבלנו יחד למען המשיח. 26עתה אני מחזירו הביתה, שכן הוא מתגעגע אליכם מאוד ומודאג מהעובדה ששמעתם כי היה חולה. 27הוא באמת היה חולה, ואפילו עמד למות! אולם אלוהים ריחם עליו וגם עלי – בחסכו ממני את הצער הזה שלא יתווסף לסבלי.

28אני רוצה מאוד להחזיר אליכם את אפפרודיטוס, שכן אני יודע עד כמה תשמחו לראותו, וגם אני אשמח ויוקל לי מאוד. 29קבלוהו באדון בשמחה רבה, והביעו את הוקרתכם והערכתכם, כי הוא סיכן את חייו למען עבודת המשיח, 30ואף עמד למות בעודו משתדל לעשות מה שאתם לא יכולתם לעשות, בגלל היותכם רחוקים ממני.