Filemon 1 – HCB & CCB

Hausa Contemporary Bible

Filemon 1:1-25

1Bulus, ɗan kurkuku saboda Kiristi Yesu, da kuma Timoti ɗan’uwanmu,

Zuwa ga Filemon ƙaunataccen abokinmu da kuma abokin aikinmu, 2zuwa kuma ga Affiya ’yar’uwarmu, zuwa kuma ga Arkiffus abokin famarmu, da zuwa kuma ga ikkilisiyar da take taruwa a gidanka.

3Alheri da salama daga Allah Ubanmu da kuma Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku.

Godiya da addu’a

4Kullum nakan gode wa Allahna sa’ad da nake tuna da kai cikin addu’o’ina, 5domin ina jin labari bangaskiyarka cikin Ubangiji Yesu da kuma ƙaunarka da kake yi saboda dukan tsarkaka. 6Ina addu’a ka zama mai ƙwazo cikin shaida bangaskiyarka, domin ka sami cikakken fahimta ta kowane abin da yake nagarin da muke da shi cikin Kiristi. 7Ƙaunarka ta sa ni farin ciki ƙwarai ta kuma ƙarfafa ni, domin kai, ɗan’uwa, ka wartsake zukatan tsarkaka.

Roƙon Bulus domin Onisemus

8Saboda haka, ko da yake cikin Kiristi ina iya yin ƙarfin hali in umarce ka ka yi abin da ya kamata, 9duk da haka ina roƙonka saboda ƙauna, na fi so in roƙe ka, ni Bulus tsoho, a yanzu kuma ga ni ɗan sarƙa saboda Kiristi Yesu. 10Ina roƙonka saboda ɗana Onesimus,10 Onesimus yana nufin mai amfani. wanda ya zama ɗana yayinda nake cikin sarƙoƙi. 11Dā kam, ba shi da amfani a gare ka, amma yanzu ya zama da amfani a gare ka da kuma gare ni.

12Ina aike shi yă koma gare ka, shi da yake zuciyata. 13Na so in riƙe shi a wurina a madadinka domin yă taimake ni yayinda nake cikin sarƙoƙi saboda bishara. 14Sai dai ban so in yi kome ban da yardarka ba, domin kowane alherin da za ka yi, yă fito daga zuciyarka, ba na tilas ba. 15Wataƙila abin da ya sa aka raba ka da shi na ɗan lokaci ƙanƙani shi ne don ka same shi da amfani 16ba kamar bawa kuma ba, sai dai fiye da bawa, a matsayin ƙaunataccen ɗan’uwa. Shi ƙaunatacce ne sosai a gare ni amma a gare ka ya ma fi zama ƙaunatacce, kamar mutum da kuma kamar ɗan’uwa a cikin Ubangiji.

17Saboda haka in ka ɗauke ni a kan ni abokin tarayya ne, sai ka marabce shi kamar yadda za ka marabce ni. 18In ya yi maka wani laifi ko kuma yana riƙe maka wani bashi, sai ka mai da shi a kaina. 19Ni, Bulus, nake rubuta wannan da hannuna. Zan biya ka, kada ma a yi zancen ranka da kake riƙe mini bashi. 20Ina fata, ɗan’uwa, zan sami amfani daga gare ka cikin Ubangiji; ka wartsake zuciyata cikin Kiristi. 21Da tabbacin biyayyarka, ina rubuta maka, da sanin za ka yi fiye da abin da na ce.

22Abu guda ya rage, ka shirya mini masauƙi, domin ina bege za a mayar da ni gare ku albarkacin addu’o’inku.

23Efafaras, abokin tarayyata a kurkuku cikin Kiristi Yesu, yana gaishe ka.

24Haka kuma Markus, Aristarkus, Demas da kuma Luka, abokan aikina.

25Alherin Ubangiji Yesu Kiristi yă kasance da ruhunku.

Chinese Contemporary Bible (Simplified)

腓利门书 1:1-25

1我是为了传扬基督耶稣而被囚禁的保罗,与提摩太弟兄写信给我们亲爱的同工腓利门弟兄、 2亚腓亚姊妹和我们的战友亚基布,以及在腓利门家里聚会的弟兄姊妹。

3愿我们的父上帝和主耶稣基督赐给你们恩典和平安!

称赞腓利门

4腓利门弟兄,我常常在祷告中为你感谢上帝, 5因为我听说了你对主耶稣的信心和对众圣徒的爱心。 6我求上帝使你能有效地与人分享信仰,明白我们所做的一切美事都是为了基督。 7弟兄啊,你的爱心给我带来极大的喜乐和安慰,因为你使众圣徒感到欣慰。

凭爱心求情

8因此,我尽管可以奉基督的名吩咐你去做当做的事, 9然而我这上了年纪又为基督耶稣的缘故被囚禁的保罗宁愿凭爱心求你, 10就是替阿尼西谋1:10 阿尼西谋”这个名字意思是有用、有益处。求你。他是我在狱中带领归主的属灵儿子, 11他过去对你没有什么益处,但现在对你对我都有益处。

12我现在派我深爱的阿尼西谋回你那里。 13我本想把他留在身边,让他在我为传福音而坐牢期间代替你服侍我。 14不过,未经你同意,我不愿意这样做,因为我盼望你的善行是出于甘心,而非勉强。 15或许他暂时离开你是为了让你以后永远得到他。 16你得到的不再是一个奴隶,而是一位远超过奴隶的亲爱弟兄。对我而言,的确如此,更何况对你呢!就肉身说你们是主仆,但在主里你们是弟兄。

17如果你当我是同伴,就请你像接纳我一样接纳他。 18如果他得罪你,或亏欠你什么,都记在我的账上吧。 19保罗在此亲笔保证,我必偿还。其实我不说你也知道,连你自己也欠我。

20弟兄啊,看在主的份上,请你答应我的请求,在基督里让我的心得到安慰吧! 21我写信给你,深信你一定会照办,甚至超过我的要求。 22同时,也请你为我预备住处,因为我盼望借着你们的祷告,我可以蒙恩到你们那里。

问候

23为了基督耶稣的缘故和我一同坐牢的以巴弗问候你。 24此外,我的同工马可亚里达古底马路加都问候你。

25愿我们主耶稣基督的恩典与你们同在。阿们!