Ayyukan Manzanni 2 – HCB & NVI

Hausa Contemporary Bible

Ayyukan Manzanni 2:1-47

Ruhu Mai Tsarki ya zo a Fentekos

1Da ranar Fentekos ta yi, dukansu suna tare wuri ɗaya. 2Ba zato ba tsammani sai aka ji motsi kamar ta babbar iska tana hurowa daga sama ta kuma cika dukan gidan da suke zaune. 3Suka ga wani abin da ya yi kama da harsunan wuta, suka rarrabu suna kuma sassauka a kan kowannensu. 4Dukansu kuwa suka cika da Ruhu Mai Tsarki suka kuma fara magana da waɗansu harsuna yadda Ruhu ya sa suka iya.

5To, a Urushalima akwai Yahudawa masu tsoron Allah, daga kowace ƙasa a duniya. 6Da suka ji wannan motsi, taro ya haɗu wuri ɗaya a ruɗe, domin kowannensu ya ji suna magana da yarensa. 7Cike da mamaki, suka yi tambaya suna cewa, “Ashe, duk waɗannan mutane masu magana ba Galiliyawa ba ne? 8To, yaya kowannenmu yana ji suna yarensa? 9Fartiyawa, Medes da Elamawa; mazaunan Mesofotamiya, Yahudiya da Kaffadokiya, Fontus da Asiya, 10Firjiya da Famfiliya, Masar da sassa Libiya kusa da Sairin; baƙi daga Roma 11(Yahudawa da kuma waɗanda suka tuba suka shiga Yahudanci); Kiretawa da Larabawa, mun ji su suna shelar abubuwan banmamaki na Allah da yarenmu!” 12A ruɗe kuma cike da mamaki, suka tambayi junansu cewa, “Mene ne wannan yake nufi?”

13Duk da haka waɗansu suka yi musu ba’a suka ce, “Sun yi tatil da ruwan inabi ne.”

Bitrus ya yi wa taron jawabi

14Sai Bitrus ya miƙe tsaye tare da Sha Ɗayan nan, ya ɗaga muryarsa ya yi wa taron jawabi ya ce, “’Yan’uwana Yahudawa da dukanku da kuke zama cikin Urushalima, bari in bayyana muku wannan, ku saurara da kyau ga abin da zan faɗa. 15Waɗannan mutane ba su bugu ba, kamar yadda kuka ɗauka. Yanzu ƙarfe tara na safe ne kawai! 16A’a, ai, abin da aka yi magana ta bakin annabi Yowel ke nan cewa,

17“Allah ya ce, ‘A kwanakin ƙarshe,

zan zubo Ruhuna bisa dukan mutane.

’Ya’yanku maza da mata za su yi annabci,

samarinku za su ga wahayoyi,

dattawanku kuma za su yi mafarkai.

18Kai, har ma a kan bayina, maza da mata,

zan zubo Ruhuna a waɗancan kwanaki,

za su kuwa yi annabci.

19Zan nuna abubuwan banmamaki a sararin sama

da alamu a nan ƙasa,

jini da wuta da kuma hauhawan hayaƙi.

20Za a mai da rana duhu,

wata kuma ya zama jini,

kafin zuwa rana mai girma da kuma ta ɗaukaka ta Ubangiji.

21Kuma duk wanda ya kira

bisa sunan Ubangiji zai sami ceto.’2.21 Yow 2.28-32

22“Mutanen Isra’ila, ku saurari wannan. Yesu Banazare shi ne mutumin da Allah ya tabbatar muku ta wurin mu’ujizai, ayyukan banmamaki, da kuma alamu, waɗanda Allah ya yi a cikinku ta wurinsa, kamar yadda ku kanku kuka sani. 23An ba da wannan mutum gare ku bisa ga nufin Allah da kuma rigyasaninsa, ku kuma tare da taimakon mugayen mutane, kuka kashe shi ta wurin kafa shi a kan gicciye. 24Amma Allah ya tashe shi daga matattu, ya ’yantar da shi daga azabar mutuwa, don ba ya yiwuwa mutuwa ta riƙe shi. 25Dawuda ya yi faɗi game da shi cewa,

“ ‘Kullum ina ganin Ubangiji a gabana.

Gama yana a hannuna na dama,

ba zan jijjigu ba.

26Saboda haka, zuciyata na farin ciki, harshena kuma na murna,

jikina kuma zai kasance da bege,

27gama ba za ka bar ni cikin kabari ba,

ba kuwa za ka yarda Mai Tsarkinka yă ruɓa ba.

28Ka sanar da ni hanyoyin rai,

za ka cika ni da farin ciki a gabanka.’2.28 Zab 16.8-11

29“’Yan’uwa, zan iya tabbatar muku gabagadi cewa kakanmu Dawuda ya mutu aka kuma binne shi, kabarinsa kuwa yana a nan har yă zuwa yau. 30Amma shi annabi ne ya kuma san abin da Allah ya yi masa alkawari da rantsuwa cewa zai ɗora ɗaya daga cikin zuriyarsa a kan gadon sarautarsa. 31Ganin abin da yake gaba, ya yi magana a kan tashin Kiristi daga matattu cewa, ba a bar shi a kabari ba, jikinsa kuma bai ruɓa ba. 32Allah ya tashe wannan Yesu zuwa rai, mu kuwa duk shaidu ne ga wannan. 33An ɗaukaka shi zuwa ga hannun dama na Allah, ya karɓi alkawarin Ruhu Mai Tsarki daga Uba, ya kuma zubo abin da yanzu kuke gani kuke kuma ji. 34Gama Dawuda bai hau zuwa sama ba, duk da haka ya ce,

“ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina,

“Zauna a hannun damana,

35sai na sa abokan gābanka

su zama matashin sawunka.” ’2.35 Zab 110.1

36“Saboda haka bari dukan Isra’ila su tabbatar da wannan. Allah ya mai da wannan Yesu, da kuka gicciye, Ubangiji da kuma Kiristi.”

37Sa’ad da mutane suka ji wannan, sai suka soku a zuci sai suka ce wa Bitrus da sauran manzanni, “’Yan’uwa, me za mu yi?”

38Bitrus ya amsa, “Ku tuba a kuma yi muku baftisma, kowannenku a cikin sunan Yesu Kiristi domin gafarar zunubanku. Za ku kuwa karɓi kyautar Ruhu Mai Tsarki. 39Alkawarin dominku ne da ’ya’yanku da kuma dukan waɗanda suke da nesa, domin dukan waɗanda Ubangiji Allahnmu zai kira.”

40Da waɗansu kalmomi masu yawa ya gargaɗe su; ya kuma roƙe su cewa, “Ku ceci kanku daga wannan lalataccen zamani.” 41Waɗanda suka yarda da saƙonsa kuwa aka yi musu baftisma, a ranar kuwa yawansu ya ƙaru da mutum kusan dubu uku.

Zumuncin masu bi

42Suka ba da kansu ga koyarwar manzanni da kuma ga zumunci, ga gutsuttsura burodin da kuma ga addu’a. 43Kowa ya cika da tsoro, manzannin kuwa suka aikata abubuwan banmamaki da alamu masu yawa. 44Dukan masu bi suna tare, suna kuma mallakar kome tare. 45Suka dinga sayar da ƙaddarorinsu da kayayyakinsu, suka ba wa kowa gwargwadon bukatarsa. 46Kowace rana suka ci gaba da taruwa a filin haikali. Suka gutsuttsura burodi a gidajensu suna cin abinci tare da farin ciki da zuciya ɗaya, 47suna yabon Allah suna kuma samun tagomashin dukan mutane. Ubangiji kuwa ya ƙara yawansu kowace rana na waɗanda suke samun ceto.

Nueva Versión Internacional

Hechos 2:1-47

El Espíritu Santo desciende en Pentecostés

1Cuando llegó el día de Pentecostés, estaban todos juntos en el mismo lugar. 2De repente, vino del cielo un ruido como el de una violenta ráfaga de viento y llenó toda la casa donde estaban reunidos. 3Aparecieron entonces unas lenguas como de fuego que se repartieron y se posaron sobre cada uno de ellos. 4Todos fueron llenos del Espíritu Santo y comenzaron a hablar en diferentes lenguas, según el Espíritu les concedía expresarse.

5Estaban de visita en Jerusalén judíos piadosos, procedentes de todas las naciones de la tierra. 6Al oír aquel bullicio, muchos corrieron al lugar y quedaron todos pasmados porque cada uno los escuchaba hablar en su propio idioma. 7Desconcertados y maravillados, decían: «¿No son galileos todos estos que están hablando? 8¿Cómo es que cada uno de nosotros los oye hablar en su lengua materna? 9Partos, medos y elamitas; habitantes de Mesopotamia, de Judea y de Capadocia, del Ponto y de la provincia de Asia, 10de Frigia y de Panfilia, de Egipto y de las regiones de Libia cercanas a Cirene; visitantes llegados de Roma; 11judíos y convertidos al judaísmo; cretenses y árabes: ¡todos por igual los oímos proclamar en nuestra propia lengua las maravillas de Dios!».

12Desconcertados y perplejos, se preguntaban: «¿Qué quiere decir esto?». 13Otros se burlaban y decían: «Lo que pasa es que están borrachos».

Pedro se dirige a la multitud

14Entonces Pedro, con los once, se puso de pie y dijo a voz en cuello: «Compatriotas judíos y todos ustedes que están en Jerusalén, déjenme explicarles lo que sucede; presten atención a lo que voy a decir. 15Estos no están borrachos, como suponen ustedes. ¡Apenas son las nueve de la mañana!2:15 son las nueve de la mañana. Lit. es la hora tercera del día. 16En realidad lo que pasa es lo que anunció el profeta Joel:

17»“Sucederá que en los últimos días —dice Dios—,

derramaré mi Espíritu sobre todo ser humano.

Los hijos y las hijas de ustedes profetizarán,

tendrán visiones los jóvenes

y sueños los ancianos.

18En esos días derramaré mi Espíritu

aun sobre mis siervos y mis siervas,

y profetizarán.

19Arriba en el cielo y abajo en la tierra mostraré prodigios:

sangre, fuego y nubes de humo.

20El sol se convertirá en tinieblas

y la luna en sangre

antes que llegue el día del Señor,

día grande y esplendoroso.

21Y todo el que invoque el nombre del Señor será salvo”.2:21 Jl 2:28-32.

22»Pueblo de Israel, escuchen esto: Jesús de Nazaret fue un hombre acreditado por Dios ante ustedes con milagros, señales y prodigios, los cuales realizó Dios entre ustedes por medio de él, como bien lo saben. 23Este fue entregado según el determinado propósito y el previo conocimiento de Dios; y por medio de gente malvada, ustedes lo mataron, clavándolo en la cruz. 24Sin embargo, Dios lo resucitó, librándolo de las angustias de la muerte, porque era imposible que la muerte lo mantuviera bajo su dominio. 25En efecto, David dijo de él:

»“Veía yo al Señor siempre delante de mí;

porque él está a mi derecha,

nada me hará caer.

26Por eso mi corazón se alegra y canta con gozo mi lengua;

mi cuerpo también vivirá en esperanza.

27No dejarás que mi vida termine en los dominios de la muerte;2:27 los dominios de la muerte. Lit. Hades; también en v. 31.

no permitirás que tu santo sufra corrupción.

28Me has dado a conocer los caminos de la vida;

me llenarás de alegría en tu presencia”.2:28 Sal 16:8-11.

29»Hermanos, permítanme hablarles con franqueza acerca del patriarca David, quien murió y fue sepultado, y cuyo sepulcro está entre nosotros hasta el día de hoy. 30Era profeta y sabía que Dios le había prometido bajo juramento poner en el trono a uno de sus descendientes.2:30 Sal 132:11. 31Fue así como previó lo que iba a suceder. Refiriéndose a la resurrección del Cristo, afirmó que Dios no dejaría que su vida terminara en los dominios de la muerte ni que su fin fuera la corrupción. 32A este Jesús, Dios lo resucitó y de ello todos nosotros somos testigos. 33Exaltado a la derecha de Dios y, habiendo recibido del Padre el Espíritu Santo prometido, ha derramado esto que ustedes ahora ven y oyen. 34David no subió al cielo, y sin embargo declaró:

»“Dijo el Señor a mi Señor:

‘Siéntate a mi derecha,

35hasta que ponga a tus enemigos

por debajo de tus pies’ ”.2:35 Sal 110:1.

36»Por tanto, que todo Israel esté bien seguro de que este Jesús, a quien ustedes crucificaron, Dios lo ha hecho Señor y Cristo».

37Cuando oyeron esto, todos se sintieron profundamente conmovidos y dijeron a Pedro y a los otros apóstoles:

—Hermanos, ¿qué debemos hacer?

38—Arrepiéntase y bautícese cada uno de ustedes en el nombre de Jesucristo para perdón de sus pecados —contestó Pedro—, y recibirán el don del Espíritu Santo. 39En efecto, la promesa es para ustedes, para sus hijos y para todos los que están lejos; es decir, para todos aquellos a quienes el Señor, nuestro Dios, llame.

40Y con muchas otras palabras les exhortaba insistentemente:

—¡Sálvense de esta generación perversa!

La comunidad de los creyentes

41Así, pues, los que recibieron su mensaje fueron bautizados y aquel día se unieron a la iglesia unas tres mil personas. 42Se mantenían firmes en la enseñanza de los apóstoles, en la comunión, en el partimiento del pan y en la oración. 43Todos estaban asombrados por los muchos prodigios y señales que realizaban los apóstoles. 44Todos los creyentes estaban juntos y tenían todo en común: 45vendían sus propiedades y posesiones, y compartían sus bienes entre sí según la necesidad de cada uno. 46No dejaban de reunirse unánimes en el Templo ni un solo día. De casa en casa partían el pan y compartían la comida con alegría y generosidad, 47alabando a Dios y disfrutando de la estimación general del pueblo. Y cada día el Señor añadía al grupo los que iban siendo salvos.