Afisawa 1 – HCB & KLB

Hausa Contemporary Bible

Afisawa 1:1-23

1Bulus, wanda Allah ya zaɓa don yă zama manzon Kiristi Yesu,

Zuwa ga tsarkaka da suke a Afisa,1.1 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā ba su da a Afisa. da kuma suke amintattu1.1 Ko kuwa masu bi waɗanda cikin Kiristi Yesu.

2Alheri da salama daga Allah Ubanmu da Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku.

Albarkun ruhaniya a cikin Kiristi

3Yabo ya tabbata ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, wanda ya kawo mana kowace albarka ta ruhaniya daga sama. 4Gama ya zaɓe mu a cikin Kiristi tun dā can, kafin ma a halicci duniya don mu zama masu tsarki da kuma marasa aibi a gabansa. 5A cikin ƙauna, ya1.4,5 Ko kuwa gani cikin ƙauna. 5 Ya ƙaddara mu zama ’ya’yansa na riƙo ta wurin Kiristi Yesu, bisa ga nufinsa na alheri. 6Ya yi haka don mu yabi Allah saboda alherin da ya yi mana saboda mu na ƙaunataccen Ɗansa ne. 7A cikinsa muka sami fansa ta wurin jininsa, wato, yafewar zunubanmu. Kiristi ya yi wannan saboda yawan alherin Allah 8wanda ya ba mu babu iyaka tare da dukan hikima da fahimta. 9Allah ya yi abin da ya nufa, ya kuma sanar mana shirin asirin da ya riga ya shirya yă cika ta wurin Kiristi. 10Nufinsa ke nan, idan lokaci ya cika, yă harhaɗa dukan abubuwa a ƙarƙashin ikon Kiristi, wato, dukan abubuwan da suke sama da abubuwan da suke ƙasa.

11A cikinsa ne kuma aka zaɓe mu mu sami gādo daga Allah,1.11 Ko kuwa mun zama abin gādon Allah an kuwa ƙaddara mu ga haka bisa ga nufin wannan da yake zartar da dukan abubuwa yadda ya yi nufi yă yi. 12Manufar Allah ita ce cewa mu da muka fara sa bege a cikin Kiristi, mu yi zaman yabon ɗaukakar Allah. 13An kuma haɗa ku a cikin Kiristi lokacin da kuka ji saƙon nan na gaskiya, wanda yake labari mai daɗi na cetonku. Da kuka ba da gaskiya, sai aka yi muku alamar shaida a cikinsa da Ruhu Mai Tsarki. 14Ruhu Mai Tsarkin nan shi ne tabbacin da Allah ya yi na cewa zai ba mu kome da ya yi alkawari, har ya sa muka sani nan gaba Allah zai ceci waɗanda suke nasa. Wannan kuwa domin yabon ɗaukakarsa ne.

Godiya da addu’a

15Saboda haka, tun lokacin da na ji labarin bangaskiyarku cikin Ubangiji Yesu da kuma ƙaunar da kuke yi wa dukan mutanen Allah, 16ban fasa yin godiya saboda ku ba, ina tuna da ku cikin addu’o’ina. 17Ina ta roƙo cewa Allah na Ubangijinmu Yesu Kiristi, Uba Maɗaukaki, yă ba ku Ruhun hikima da na ganewa, domin ku san shi da kyau. 18Ina kuma addu’a cewa zuciyarku tă waye don ku gane ko mene ne sa zuciyan nan da ya kira ku a kansa, ku kuma san darajar dukiyan nan wadda take ta mutanen Allah, wato, albarkunsa. 19Ina addu’a ku san girman ikon Allah wanda ya wuce misali, wanda yake namu. Ikon da yake aiki a cikinmu, ɗaya ne da ikon nan 20da ya tā da Kiristi daga matattu, ya kuma sa ya zauna a hannun damansa a cikin mulkin samaniya. 21Yanzu yana mulki a kan dukan masu sarauta, da masu iko, da masu ƙarfi, da kuma masu mulki. Yana mulkin kome a wannan duniya, zai kuma yi mulkin duniya mai zuwa. 22Allah ya sa kome a ƙarƙashin ikonsa, ya kuma ba shi iko a kan kome don amfanin ikkilisiya. 23Kuma ikkilisiya ce jikinsa; ta kuma cika da Kiristi, wanda ya cika kome ta kowace hanya.

Korean Living Bible

에베소서 1:1-23

1하나님의 뜻에 따라 그리스도 예수님의 사도가 된 나 바울은 에베소에 있는 성도 들과 그리스도 예수님을 믿는 신자들에게

2하나님 우리 아버지와 주 예수 그리스도의 은혜와 평안이 함께하기를 기도합니다.

그리스도 안에서 누리는 영적인 복

3우리 주 예수 그리스도의 아버지 하나님께 찬양을 드립니다. 하나님 아버지께서는 그리스도 안에서 하늘의 모든 영적인 복을 우리에게 내려 주셨습니다.

4하나님은 우리가 자기 앞에서 거룩하고 흠이 없게 하시려고 세상을 창조하시기 전에 그리스도 안에서 우리를 선택하셨습니다. 그리고 우리를 사랑하셨기 때문에

5하나님은 예수 그리스도를 통하여 그분의 기뻐하시는 뜻을 따라 우리를 자기 자녀로 예정하셨습니다.

6이것은 우리가 그분이 사랑하시는 아들 안에서 우리에게 거저 주신 은혜와 영광을 찬양하게 하려는 것입니다.

7우리는 하나님의 풍성하신 은혜를 따라 그리스도 안에서 그분의 피로 죄 사함을 받고 구원을 얻었습니다.

8하나님은 모든 지혜와 총명으로 우리에게 그런 은혜를 주신 것입니다.

9그리고 하나님은 자기가 기뻐하시는 뜻대로 그리스도 안에서 미리 계획하신 비밀을 우리에게 알려 주셨는데

10그것은 때가 되면 하늘과 땅에 있는 모든 것이 그리스도 안에서 하나가 되도록 하는 것입니다.

11그리스도 안에서 모든 것을 자기 뜻대로 이루시는 하나님의 계획을 따라 예정대로 우리는 그분의 1:11 또는 ‘기업’백성이 되었습니다.

12이것은 제일 먼저 그리스도를 대망하던 우리가 하나님의 영광을 찬양하도록 하기 위한 것입니다.

13그리고 여러분도 진리의 말씀인 구원의 기쁜 소식을 듣고 그리스도를 믿게 되었으며 하나님께서는 이를 확인하는 표로 약속하신 성령을 우리에게 주셨습니다.

14성령께서는 하나님이 약속하신 것을 우리가 받을 것이라는 것을 보증하시고 하나님의 백성이 구원을 받아 그분의 영광을 찬양하도록 하십니다.

감사와 기도

15나는 여러분이 주 예수님을 잘 믿고 모든 성도를 사랑한다는 말을 듣고

16기도할 때마다 여러분을 생각하며 항상 하나님께 감사하고 있습니다.

17나는 우리 주 예수 그리스도의 하나님, 영광의 아버지께서 여러분에게 지혜와 계시의 성령을 주셔서 하나님을 더욱 잘 알게 해 주시고

18여러분의 마음의 눈을 밝히셔서 부르심을 받은 여러분의 희망이 무엇이며 성도들이 하늘 나라에서 받게 될 영광스러운 축복이 얼마나 풍성한가를 알게 해 주시고

19또 믿는 우리 속에서 강한 능력으로 역사하시는 하나님의 권능이 얼마나 큰가를 알게 하시기를 기도합니다.

20하나님께서는 그 크신 능력으로 그리스도를 죽은 사람들 가운데서 다시 살리시고 하늘 나라에서 자기 오른편에 앉게 하셨습니다.

21그뿐만 아니라 그리스도를 모든 통치자와 권세와 능력과 지배권과 또 이 세상이나 오는 세상의 모든 이름 위에 뛰어나게 하셨습니다.

22그리고 하나님은 모든 것을 그리스도의 발 아래 복종하게 하시고 그분을 만물 위에 교회의 머리로 삼으셨습니다.

23교회는 그리스도의 몸이며 어디서나 모든 것을 넘치도록 채워 주시는 분이 계신 곳입니다.