2 Korintiyawa 1 – HCB & SNC

Hausa Contemporary Bible

2 Korintiyawa 1:1-24

1Bulus, manzon Kiristi Yesu ta wurin nufin Allah, da kuma daga Timoti ɗan’uwanmu,

Zuwa ga ikkilisiyar Allah da take a Korint, tare da dukan tsarkaka a ko’ina a Akayya.

2Alheri da salama daga Allah Ubanmu da kuma Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku.

Allah na dukan ta’aziyya

3Yabo ya tabbata ga Allah, da Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, Uba mai tausayi, da kuma Allah na dukan ta’aziyya, 4wanda yakan yi mana ta’aziyya a cikin dukan wahalolinmu, domin mu kuma mu iya ta’azantar da waɗanda suke cikin kowace irin wahala, da ta’aziyyar da mu kanmu muka samu daga Allah. 5Gama kamar yadda wahalar Kiristi ta cika har tana zuba a cikin rayuwarmu, haka nan kuma ta wurin Kiristi ta’aziyyarmu ta cika har tana zuba. 6In muna shan wahala, ai, muna shanta domin ta’aziyyarku, da cetonku ne, in mun sami ta’aziyya, ai, mun same ta domin ta’aziyyarku ce, wadda take sa ku jure wa irin wahalan nan, da muke sha. 7Begen da muke da shi dominku kuwa, tabbatacce ne, domin mun san cewa kamar yadda kuke tarayya da mu a cikin wahalolinmu, haka kuma kuke tarayya da mu a cikin ta’aziyyarmu.

8’Yan’uwa, ba ma so ku zama da rashin sani, a kan wahalolin da muka sha a lardin Asiya. Mun sha wahaloli sosai, har abin ya fi ƙarfinmu, ya sa muka fid da tsammanin rayuwa. 9Ba shakka, a zuciyarmu mun ji kamar hukuncin kisa ne aka yi mana. Wannan kuwa ya faru ne domin kada mu dogara da kanmu, sai dai ga Allah, wanda yake tā da matattu. 10Shi ya cece mu daga irin wannan hatsari na mutuwa, zai kuwa cece mu. A kansa muka kafa bege cewa zai ci gaba da cetonmu, 11yayinda kuke taimakonmu ta wurin addu’o’inku. Mutane da yawa kuwa za su yi godiya ta dalilinmu, saboda albarkar da aka yi mana, ta amsa addu’o’i masu yawa.

Canja shirye-shiryen Bulus

12Wannan shi ne taƙamarmu. Lamirinmu yana ba da shaida cewa mun yi zamanmu a duniya, musamman a dangantakarmu da ku cikin tsarki, tsakani da Allah. Mun yi haka ta wurin bishewar alherin Allah, ba bisa ga hikimar duniya ba. 13Gama ba mu rubuta muku abin da ba za ku iya karatu ko ku kāsa fahimta ba. Ina kuma fata cewa, 14kamar yadda kuka ɗan fahimce mu, za ku kai ga cikakkiyar fahimta cewa za ku iya yin taƙama da mu, kamar yadda mu ma za mu yi taƙama da ku a ranar da Ubangiji Yesu zai dawo.

15Saboda na amince da haka, shi ya sa na so zuwa wurinku da fari, domin ku sami albarka riɓi biyu. 16Na yi shiri in ziyarce ku a kan hanyata zuwa Makidoniya, in kuma sāke dawo wurinku a kan hanyata daga Makidoniya, sa’an nan ku yi mini rakiya a hanyata zuwa Yahudiya. 17Kuna gani na yi wannan shirin ba da sanin abin da nake yi ba ne? Ko kuwa, kuna gani na yi shirin nan da halin mutuntaka ne, don in ce, “I” in koma in ce, “A’a”?

18Kamar dai yadda ba shakka Allah yake mai aminci, haka ma maganar da muka yi muku, ba “I” da kuma “A’a” ba ce. 19Gama Ɗan Allah, Yesu Kiristi, wanda ni da Sila da Timoti muka yi muku wa’azinsa, ai, ba “I” da “A’a” ba ne, amma a cikin Kiristi, “I” ne kullum. 20Domin dukan alkawaran Allah cikarsu a gare shi suke, ta wurinsa ne kuma muke faɗar “Amin”, domin a ɗaukaka Allah. 21Allah ne fa yake sa mu da ku mu tsaya daram cikin Kiristi. Shi ne ya shafe mu, 22ya buga mana hatiminsa a kan mu nasa ne, ya kuma sa mana Ruhunsa a cikin zukatanmu, domin yă tabbatar da abin da yake zuwa nan gaba.

23Labudda, Allah shi ne shaidata cewa don kada in ƙara muku wahala ne ya sa ban koma Korint ba. 24Ba nuna muku iko a kan bangaskiyarku muke yi ba, sai dai muna aiki tare da ku ne saboda farin cikinku, domin bisa ga bangaskiya ce kuke tsaye da ƙarfi.

Slovo na cestu

2. Korintským 1:1-24

Úvodní pozdravy

1Drazí bratři, tento dopis vám píši jako Bohem zmocněný posel Ježíše Krista, společně s Timotejem. Adresovaný je sice k vám do Korintu, ale je určen všem křesťanům v celém Řecku: 2kéž vás náš Otec Bůh i Ježíš Kristus bohatě obdarují svou milostí a pokojem.

Bůh pomáhá v utrpení

3-4Jak nevýslovně dobrý je náš Bůh. V něm, Otci našeho Pána Ježíše Krista, máme nevyčerpatelný zdroj útěchy a posily pro naše zkoušky a utrpení, takže i jiné pak můžeme těšit a posilovat, když je to zapotřebí. 5Stejnou pomoc, jakou jsme obdrželi od Boha, rozdáváme všude kolem sebe. 6Můžete se spolehnout, že čím víc utrpení podstoupíme pro Krista, tím hojněji nás zahrne svou útěchou a povzbuzením. Kristovo utrpení je mým denním chlebem, ale to je můj příspěvek k vaší záchraně. 7On mi však denně dává též novou sílu a klid – a to má být zase posilou vám ve vašich zkouškách. Pokud s námi sdílíte naše bolesti, nemám o vás obavy: zdroj naší útěchy je otevřen i pro vás.

8-9Nebudu vám, drazí, tajit, že tady v Malé Asii jsme prožili snad nejhorší chvíle svého života. Vypadalo to už, že je s námi konec, připravovali jsme se na smrt. Cítím, že to muselo dojít tak daleko proto, abychom nespoléhali již na nic jiného než na Boha, který má moc vzkřísit i mrtvé. 10Skutečně nás vyrval přímo z drápů smrti a věřím, že ne naposledy. 11Přesto prosím, abyste na nás stále mysleli ve svých modlitbách – tím větší budou pak vaše chvály a vděčnost za jejich vyslyšení.

12S naprosto čistým svědomím mohu prohlásit, že jsem s vámi ve všech směrech jednal vždy jen a jen upřímně, jak mě Bůh vedl, a na to jsem hrdý. Ne lidská vypočítavost, ale Boží milost je mi vůdčí silou. To platilo vždy i ve vztahu k vám. 13-14Všechno, co čtete v mých listech, je míněno naprosto upřímně. Doufám, že to tak přijmete, i když se dosud mnoho neznáme, a že při Kristově návratu se za sebe navzájem nebudeme muset stydět, ale naopak budeme mít důvod k hrdosti.

Pavel mění plán svých cest

15V této důvěře jsem vás chtěl navštívit už na cestě do Makedonie a pak se vrátit do Judska zase přes Korint. 16-20Proč jsem svůj plán později změnil? Nebylo to z vrtkavosti ani z lehkomyslnosti. Když jednou něco řeknu, pak to také tak myslím; nikdy neříkám „ano“, když myslím „ne“, a naopak. Boží Syn Ježíš Kristus, jak jsme vám ho přiblížili se Silvánem a Timotejem, také nebyl muž dvojí tváře. Jeho osoba je hmatatelným ANO všem slibům, které Bůh kdy dal člověku. Proto taky, když k modlitbě připojíme Amen (tj. „ano“), připomínáme si vlastně, že v Kristu na ně Bůh už odpověděl, a oslavujeme ho za to. 21Že jste v Kristu obdrželi tentýž nový život jako my, že v něm dosud pevně stojíme – to je jen Boží dílo. 22To on nás učinil svým vlastnictvím, pověřil svým poselstvím a vtiskl nám svou vlastnickou pečeť – svatého Ducha – jako záruku na vše ostatní, co má ještě pro nás přichystáno.

23Pán Bůh ví, že to nebylo jinak, než vám tady píšu: Korint jsem nakonec rozhodl vynechat jen proto, abych vás ušetřil setkání, které by pro vás mohlo být velice trapné. 24Ne že bych vám chtěl vytýkat nedostatky ve vaší víře – v té si stojíte docela dobře.