1 Korintiyawa 3 – HCB & JCB

Hausa Contemporary Bible

1 Korintiyawa 3:1-23

A kan tsattsaguwa a cikin ikkilisiya

1’Yan’uwa, ban iya yi muku magana kamar masu ruhaniya ba, sai dai kamar masu halin mutuntaka, jarirai cikin bin Kiristi kawai. 2Na ba ku madara ba abinci mai tauri ba, domin ba ku balaga ba a lokacin. Kai, har yanzu ma, ba ku balaga ba. 3Har yanzu kuna rayuwa bisa ga halin mutuntaka. Da yake akwai kishi da faɗace-faɗace a cikinku, ba rayuwa irin ta halin mutuntaka ke nan kuke yi ba? Kuma ba rayuwa irin ta mutane ce kawai kuke yi ba? 4Gama sa’ad da wani ya ce, “Ni na Bulus ne,” wani kuma ya ce, “Ni na Afollos ne,” ba rayuwa irin ta mutane ke nan kuke yi ba?

5Shin, wane ne Afollos? Wane ne kuma Bulus? Ai, bayi ne kawai waɗanda ta wurinsu kuka gaskata, kamar yadda Ubangiji ya ba kowannensu aikinsa. 6Ni na shuka iri, Afollos kuma ya yi banruwa, amma Allah ne ya sa irin ya yi girma. 7Don haka, da wanda ya yi shuki, da wanda ya yi banruwa, ba a bakin kome suke ba, sai dai Allah kaɗai, mai sa abubuwa su yi girma. 8Mutumin da ya yi shuki, da mutumin da ya yi banruwa nufinsu ɗaya ne, kuma kowannensu zai sami lada gwargwadon aikinsa. 9Gama mu abokan aiki ne na Allah; ku kuwa gonar ce ta Allah, ginin Allah kuma.

10Ta wurin alherin da Allah ya ba ni, na kafa tushen gini kamar ƙwararren magini, wani kuma dabam yana gini a kai. Amma kowa yă lura da yadda yake gini. 11Gama babu wanda zai iya kafa wani tushen gini dabam da wanda aka riga aka kafa, wanda yake Yesu Kiristi. 12In wani ya yi gini a kan tushen ginin nan da zinariya, azurfa, duwatsu masu daraja, itace, ciyawa ko kara, 13aikin zai bayyana kansa, domin za a nuna shi a sarari a Ranar. Wuta ce za tă bayyana aikin, wutar kuwa za tă gwada ingancin aikin kowa. 14In abin da kowane mutum ya gina ya tsaya, zai sami lada. 15In ya ƙone, zai yi hasara, amma zai sami ceto, sai dai kamar wanda ya bi ta tsakiyar wuta ne.

16Ashe, ba ku sani ba cewa ku kanku haikalin Allah ne, Ruhun Allah kuma yana zaune a cikinku? 17Duk wanda ya ɓata haikalin Allah, Allah zai ɓata shi, don haikalin Allah mai tsarki ne, ku ne kuwa haikalin nan.

18Kada ku ruɗi kanku. In waninku yana tsammani cewa yana da hikima, yadda duniya ta ɗauki hikima, to, sai ya mai da kansa “wawa” don yă zama mai hikima. 19Gama hikimar duniyan nan, wauta ce a gaban Allah, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Yakan kama masu hikima a cikin makircinsu”3.19 Ayu 5.13; 20kuma a rubuce yake cewa, “Ubangiji ya san dukan tunanin masu hikima banza ne.” 21Saboda haka, kada wani yă yi taƙama da mutum! Gama kome naku ne, 22ko Bulus ko Afollos ko Kefas ko duniya ko rai ko mutuwa ko abubuwa na yanzu ko na nan gaba, ai, duka naku ne, 23ku kuwa na Kiristi ne, Kiristi kuma na Allah ne.

Japanese Contemporary Bible

コリント人への手紙Ⅰ 3:1-23

3

自分を知者と思うな

1愛する皆さん。私は皆さんに、クリスチャンの生活面について、まるで子どもに語るように書いてきました。実際あなたがたは、主に従わないで、好きかってにふるまっています。そんなあなたがたに、聖霊に満たされた人を相手にしているようには書けないからです。 2つまり、堅い食物を避けてミルクを飲ませました。堅い食物の消化はむりだったからです。実は今でも、あなたがたはミルクしか飲めない状態です。 3相変わらず、よちよち歩きもおぼつかないクリスチャンで、それは、あなたがたがねたみ合い、仲間割れをしていることからも明らかです。実際、あなたがたの態度ときたら、まるで主を信じていない人のようです。 4「パウロとアポロとどちらが偉いか」などと口論して、教会を分裂させている現状では、主にあって少しも成長していないことをさらけ出しているようなものではありませんか。

5私たちが争いの原因になるとは、いったい、私が何者だと言うのですか。アポロが何者ですか。ただ神に仕える者にすぎず、それぞれに特別の能力が与えられて、あなたがたが信じるための手助けをしたにすぎません。 6私の仕事は、あなたがたの心に種をまくことでした。アポロの仕事は、それに水をやることでした。しかし、あなたがたの心の中でそれを成長させたのは神であって、私たちではありません。 7まく者も、水をやる者も、さほど大切ではありません。大切なのは、成長させてくださる神なのです。 8アポロも私も、同じ目標を目指して働いていますが、それぞれ、その労苦に従って報酬を受けるでしょう。 9私たちは神の協力者にすぎません。あなたがたは私たちの畑ではなく、神の畑です。私たちの建物ではなく、神の建物です。

10神様は恵みによって、私に、どうしたら腕のよい建築家になれるかを教えてくださいました。私が土台をすえ、アポロがその上に建物を建てました。しかし、その土台の上に建物を建てるには、細心の注意が必要です。 11私たちがすでに持っている本物の土台、イエス・キリスト以外に、土台をすえることなどだれにもできないのです。 12しかし、この土台の上には、いろいろの材料で建てることができます。金や銀や宝石を使う人もいれば、また木や草、わらなどを用いる人もあります。 13やがて、すべてがテストされる、キリストのさばきの日が来ます。その時には、建築家が各自どんな材料で建てたかが明白になります。それぞれの仕事は火でテストされ、なお価値が変わらないかどうか、ほんとうに完璧な建物かどうかが、だれの目にも明らかになります。 14そして、その土台の上に適切な材料を使って建てた人は、建物がちゃんと残るので報いがあります。 15しかし、家が焼けてしまった人は、大損害をこうむります。その人自身は、炎の中をくぐり抜けるように、命からがら逃げて救われるでしょうが。

16あなたがたは自分たちが神の家であり、神の聖霊が自分の内に住んでおられることがわからないのですか。 17もし神の家を汚したり、こわしたりする人がいれば、神様はその人を滅ぼされます。なぜなら、神の家は聖なるものだからです。あなたがたは、その神の家なのです。

18自分をだますのはやめなさい。だれか、「自分は世の知者だ」と、もし考えているのなら、そんな考えは捨てて、愚か者になるほうが身のためです。天からの真の知恵を受ける妨げにならないためです。 19この世の知恵は、神から見れば愚かだからです。聖書のヨブ記に、「神は人の知恵を、その人を捕らえるわなとして用いられる」(5・13)と書いてあるとおりです。つまり、人は自分の「知恵」につまずいて倒れるのです。 20また、詩篇には、「主は、人間の考えや判断がどんな程度か、また、それがどんなに愚かしく無益か、よく知っておられる」(94・11)とあります。

21ですから、この世の知者の弟子であることを誇ってはなりません。神様はすでに、あなたがたに必要なものは全部与えてくださっているのです。 22パウロも、アポロも、ペテロも、あなたがたを助けるために神がお遣わしになったのです。神様は全世界を、あなたがたの益になるようにと与えてくださいました。生も死も、あなたがたのものなのです。現在のことも、将来のことも、すべては、あなたがたの手にあります。 23そして、あなたがたはキリストのもの、キリストは神のものです。